IYALAN MU DA SALLAH 02

*🎊IYALAN MU DA SALLAH 02🎊*

🎉Kai ziyara a lokacin bukukuwan sallah abu ne mai kyau. Idan kin ce ya'yanki su shirya su je  gaishe da yan'uwa da abokan arziki wannan ba laifi bane.

🎉Sai dai ana son ki kula kuma kisa idon sanin ina da ina suke zuwa. Kulawa da in da suke zuwa wannan shine abun da yawancin iyaye basa damuwa da shi. Don yau sallah ne shike nan an bawa yara dama su je duk in da suka gadama. Kuma babu ruwan ta da sanin in da suka je. Yarinya zata fita tun safe amma ba zata dawo ba sai gari ya fara duhu, in ta dawo kuma babu ruwan ki saboda kawai yau sallah. Wannan kuskure ne babba, 'yan mata da kuke gani sun san yanda za su shirya da samari a hadu a can wani wuri. Idan ma ba'a hadu ba to za su musu kwatancen 'dakinsu su kai musu ziyara, kin ga daga nan duk abun da ya faru sai ki kuka da kanki. Don haka ki sasu su je gidan yan'uwan ki, kuma ki kira ki tabbatar da cewa eh sun je gidan ne.

🎉Amma a bar yaro yana yawo kwararo kwararo da sunan yawon sallah wannan bai dace ba. Abu mai wuya ne a yi sallah a gama baka ji an yi cigiyan yara ba, saboda kananun yara ana barin su yawo anyhow. Kuma in ma ba a sace su ba yanzu za a fyede miki 'yaya babu mace babu namiji. Don haka ita uwa bata ta'ba ajiye makaman tarbiyyan ya'yanta.

🎉Sannan kula da irin kuďaden da zaki gansu da shi, da kuma tambayar su wanda ya basu. A al'adar hausa ana bada barka da sallah, to amma ki hana su rokon mutane kudi. Idan sun ga mutum sun masa gaisuwar sallah yace su zo su amshi goron sallah to wannan babu laifi, amma a hana su tsare babba su ce sai ya basu kudi. Sannan a hana su karba daga wadanda basu sani ba, don wannan ma salo ne na sace yara.

🎉Kai uba yana da kyau idan matar ka bata san me take ba, to kai ka tsawatar a matsayin ka na shugaban gidan, don ganin abubuwa sun tafi dai-dai.

*🖎Sadeeya Lawal Abubakar*

*📚MARKAZUS SUNNAH*

*📞Zaku iya shiga group din ta wainnan numbers din 08034643244 08089074217*

Post a Comment (0)