Malam Direba

Wani Direban jirgin samane ke ɗauke da wasu dubban mahauka a cikin jirgi da ga legas zai kaisu Afrika ta kudu domin ai musu magani. Ana cikin tafiya sai mahaukatan nan suka fara hayaniya da faɗace-faɗace har suka takurawa direban jirgin, ana cikin haka sai ɗaya daga cikinsu (TALLE) ya shiga inda direban jirgin yake yace ya koya masa tuƙi. Direba: to zan koya maka tuƙi amma bisa sharaɗi. Talle: mene ne sharaɗin? Direba: sai in har ka yadda zaka sa abokanka suyi shiru. Bayan kamar minti biyar sai ga talle ya dawo kuma jirgin yayi shiru tsit. Direba: ah! Meka faɗa musu sukayi shiru? Talle: ƙofa na buɗe musu nace suje suyi wasa!

Post a Comment (0)