WANI BABA DA YARONSA SUNA CIN ABINCIN SALLAH TARE Wani yaro ne suna cikin cin abinci da babansa sai kalli baban nasa zai yi magana har ya fara ce "baba!!!..." sai baban ya daka masa tsawa yace "ba nace maka ba a magana idan ana cin abinci ba?" Sai yaro yayi shiru saboda biyayyan iyaye da yake dashi inji Babs. Chan bayan an gama cin abincin ne sai baban bayan yayi gyatsa sai yace wa yaron "dazun me kake son kace mun lokacin da muke cikin cin abinci?" Sai yaro yace "Daman wani katon kyankyaso matacce na gani ka hado loma dashi shine naso in gaya maka" Sai baban yace "toh yanzu kyankyason yana ina?" Sai yaro yace "ai ka cinyeshi" Sai baban cikin fushi yace "toh ya baka gaya mun tun da sauri ba?" Sai yaro yace "ai kaine ka hanani in gaya maka don kace ba a magana in ana cin abinci shine nayi shiru na barka ka cinyeshi" Sai baban ya shiga amai!!! :D