Ƴar Bautar Ƙasa 15


*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*masoyana ina alfahari daku ako ina kuke,nima ina sonku,gaskiya bazan ɓoye mukuba,comments ɗinku nayau yamin daɗi ba kaɗanba,Allah yasa ku ɗore ahaka,sabida comments shike ƙara mana ƙarfin guiwa,nagode nagode nagode sosai,dan wlh ban ɗauka ana karanta littafin kamar hakaba,naji daɗi Allah yabarmu tare,burin surbjo kenan kullum sanya farin ciki da walwala acikin zukatanku,domin mantar daku ɓacin rai,love you all*.


*15*


Najeeb Hassan Alkanawi shine cikakken sunanshi.

Saurayine ɗan kimanin shekaru talatin da biyar da haihuwa.

Ɗan garin kano ne,acikin anguwar nasarawa GRA gidan mahaifinshi yake.

Mahaifinshi Alhaji hassan Alkanawi,hamshaƙin me kuɗine ajihar ta kano,mahaifiyar najeeb ta rasu tun yan da shekara goma aduniya.

Yataso a hannun kishiyar mahaifiyarshine me suna hajiya kaltum,sam hajiya kaltum bata ƙaunar najeeb ko kaɗan,duk wani abu daze zama sanadin farincikin shi bata sonshi,kuma setasan yadda tayi ta hanashi samunshi.

Najeeb mutumne miskili me haƙuri,ko kaɗan amman beson raini,mhaifinshi nasonshi yanamasa duk abinda yakeso,amman in hajiya kaltum tagani kotasan zaamasa seta hana.

Dayake Alhjin tsoronta yakeji.

Dakyar njeeb yasamu yagama karatunshi har yasamu ayki,najeeb kyakkyawne ajin farko,duk abinda ake kira kyau ajikin ɗa namiji najeeb ya mallakeshi.

Kyanshine ya janyo hajiya kaltum jin,shaawar haɗa shinfiɗa dashi.

Tun tana ɓoye mishi nufinta har tazo ta bayyana masa face to face,ranar najeeb kwana yayi kuka sabida be taɓa ganin balai irin wannan ba.

Su uku ne agurin mahaifinnasu,shi da ƙannasa mata guda biyu hassana da ussaina,wainda suke ƴaƴa ga hajiya kaltum.

Mahaifinshi mutum ne me tafiye tafiye,shiyasa da zaran yabar ƙasar hajiya kaltum se ta buɗe babin iskanci.

so biyu tanayin tsirara agaban najeeb wai dole sai ya kwanta da ita.takaicin hajiya kaltum ne ya haddasawa najeeb kamuwa da ciwon zuciya.

Sabida ita seda yasauya keys ɗin ɗakinshi amman kamar tsafi seta sama cikin dare sede yajishi rungume ajikinta.

so tari najeeb yasha kwana acikin lambun gidansu,sabida balain hajiya kaltum.

Tunda tafara nuna masa mugayan halayantane yafara neman transfer daga asibitin murtala na kano zuwa keffi,dan yafiso yayi nisa da gidan.

Cikin hukuncin Allah yasamu transfer ɗin ya haɗa inashi inashi yabar garin kano zuwa keffi tunda yakoma keffi da ayki se yayi shekara bezo kanoba,kuma ko yatashi zuwa se yasan mahaifinshi na gari yake zuwa.

Wannan hali na hajiya kaltum ne yajanyo najeeb ya tsani soyayya,sam sho ko macema bata birgeshi,sabida gani yake duk halinsu ɗaya.

Sanda yafara ganin salma yayi mamaki daya amince tazauna a office ɗinshi.sabida shi a ƙaidarshi baya lura da coper tamace sede namiji,sabida yatsani yin alaƙa kowacce irice da mace.

To amman abin mamaki yagaza korar salma kamar sauran.

yarasa dalili duk ranar dayaga salma tayi shiga mara kyau,wuni yake ya kwana cikin takaici da baƙinciki.

Uwa uba kuma idan yaganta da Alhaji Adamu,har ƴar matashiyar hauka yake aɗakinshi,sabida baƙin ciki.


Tunda yasamu labarin mutuwarta,yazama wani iri sam bashida natsuwa da kwanciyar hankali kullum cikin yimata addua da sadaka yake,kuma koyaushe se yayi mafarkinta,se ya dangana hakan da sa tunaninta arai dayayine.

Shiyasa randa yaganta a tv ya ruɗe sosai.

Besamu kwanciyar hankaliba seda yaga ya kuɓutar da ita.

*CIGABAN LABARI*

Awa biyu doctor yayi ahanya sannan ya iso Abuja.

Office ɗinshi yanufa yafara duba marasa lafiya,har zuw lokacin da,ze tashi.

Yana barin office ɗin gurin barrister kabeer yanufa sabida sunyi waya yashaida mishi yana hanya inya iso zezo gurinshi.

muje zuwa.

surbajo for life.

Post a Comment (0)