Ƴar Bautar Ƙasa 16

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhamnad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*16*


Yana shiga office ɗin barrister,tunkan yazauna barrister ya kwashe da dariya yana faɗin.

"najeebullahi na salma me abun mamaki,naku salon ba irin namu bane,laila majnun"yasake kwashewa da dariya har yana dukan table.

Haushine yaka najeeb,game da haɗashi da salma da yayi,dan haka miƙewa yayi ze tafi.

Da sauri kabeer yasha gabanshi yana dariya,yace.

"haba angon salma,banason wulakanci,yazaka kaje kayi kwanan soyayya,sannan dan wulaƙanci katashi zaka tafi baka bani labariba"ya ƙarasa maganar yana dariya sosai.

Bige hannunshi najeeb yayi sannan yace.

"uban waye yayi kwanan soyayyar,dahar zan baka labari?ni wallahi ka isheni da zancan yarinyarnan nasha faɗa maka ba sonta nakeba meyasa bazaka gane bane?"najeeb ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya.

Dariya kabeer yayi sannan yace.

"Ay danna fahimcekanne yasa nake fitoma da abun dake danunka wanda kai kaƙi amincewa dashi,shiyasa nake saka ahanya gudun aykata,danasani anan gaba"

Tsaki najeeb yayi sannan yace.

"inde akan salma ne babu ni babu danasni har abada,karubuta ka ajiye,kuma zancan kasani a hanya ma be tasoba,dan haka kabarni da damuwar tawa dakai ka hangota wacce ni bansan tana damuna ba"

Shide kabeer inbanda dariya ba abinda yakeyi gaba,ɗaya yakasa magana.

 A fusace najeeb yabar office ɗin yatafi gidanshi,dan ya lura kabeer ɗan rainin wayone dole yataka masa burki tun wuri.

Koda ya koma gidan gaba ɗaya ya rasa sukuni,salma kawai yake gani a fuskar shi,yayin da muryarta ke masa gizo a kunnensa.

A taƙaice de ranar beyi bacciba salma ce kawai aranshi.

Itama salma anata ɓangaren,koda ta tashi akace mata yatafi sam bataji daɗiba,dan yanzu bata gajiya da kallo dajin muryarshi,haka ta wuni tamkar mara lafiya.


Da safe doctor daya isa office ɗinshi ɗakin da salma ta kwanta ya shiga,ledar kayan daya siyamata yagani a ajiye akan gadon.

Ɗauka yayi yaje yasa a mota yadawo yafara duba marasa lafiya,wuni yayi yana kewar salma.

A daddafe ya iya yin sati ɗaya,ranar daya cika sati yakama hanyar kaduna.

Be jimaba ya isa,seda ya isa ƙofar gidanne kuma ya daburce yarasa mezece ya kawoshi,zama yayi amotar yana kallo ƙofar gidan inda sahabi ke zaune yakasa kayan miyansa.

Dayake bada motar daya kawo salma yazoba shiyasa sahabi be gane shiba,daɗin daɗawa glass ɗin motar baƙine,shine yabashi damar kallon komai batare da ansa yana yiba.


Salmace ta fito daga gidan sanye cikin dogon hijbi har ƙasa,hannunta riƙe da qurani,tagaban motarshi tazo ta wuce dan haka binta yayi baya dan yaga inda zata.

wata makarantar islamiyya yaga ta shiga,awa biyu yayi yana jiranta zuwacan segata ta fito ta kama hanyar gidansu sake binta yayi har suka dawo gidan,tashige gida shi kuma yayi parking.

najeeb yarasa abinyi,gashi laasar har tayi,be samu mafita ba,dan haka shahada yayi yafito yanufi sahabi.

Sallama yamasa cike da faraa sahabi ya ams yace.

"kaine tafe da yammacinnan?"

"munzo ɗaurin auran abokinmune,shine nace bari inbiyo mugaisa da baba"


"ikon Allah gaskiya ka kyauta wlh,sede baba bayanan yaje kano taaziyya,se mamace kawai muje ku gaisa"

Riƙe da hannun juna suka shiga cikin gidan.

Shigarsu tayi daidai da fitowar salma daga wanka ɗaure da tawul ko cinyoyinta be gama rufewa ba, dayake toilet ɗin atsakar gida yake.

batasan sunshigoba se aykin girgiza kanta takeyi,tanaso ta rage ruwan dake kan nata.

Tunda suka shiga idon najeeb ya,sauka akan fararan cinyoyin nata masu kyan tsari,wani abune ya,tsirga masa tundaga saman kansa zuwa tafin ƙafarsa,sam yakasa ɗauke idonshi akanta.

Shiko sahabi cikin masifa yatunkareta da niyyar dukanta yana faɗin.

"waike salma ubanwa zaki nunawa boko da wayewa,banace kar insake ganinki ɗaure da tawul zaki wanka ba,amman dayakw kinga ba yanzu zan shigoba shine kika ɗaura ko?"

Ɗagowa tayi daniyyar bashi haƙuri,karab idonta yasauka akan na doctor,da wani mahaukacin gudu ta faɗa cikin ɗakinta tamaida ƙofar ta rufe,jikinta se ɓari yake,shiko sahabi yaɗauka shi ta gudarwa danhaka juyawa yayi yana faɗin.

"ƴar nema yau da kintsaya dana koyamiki hankali"

Ɗakin mahaifiyarsu yashiga yaɗauko tabarma ya shimfiɗawa doctor sannan yakoma yatasota dayake bacci takeyi.

Tayi murna da ganin doctor ba kaɗanba,rasa inda zata sashi tayi,sun ɗan taɓa hira sannan yamiƙe ya ajiye musu kuɗi kimanin dubu ɗari biyar yace aba baba yaja jari.

Da kyar suka amshi kuɗin sunata samasa albarka,sannan sahabi ya rakashi mota,har yashiga,se sahabi yace.

"kaga har zaka tafi baku gaisa da salma bari inturota ku gaisa ay ba daɗi kazo baku gaisaba"

Yana kaiwa nan yajuya yashiga cikin gidan,yadunga kwala mata kira,fitowa tayi sanye da doguwar riga,ta yaf mayafi a kanta,bejira me zatacw ba yace.

"maza kije ku gaisa da najeeb sauri yake ze koma"

Yana gama bata umarnin yashige ɗakin mahaufiyarsu,ita kuma takama hanyar zuwa gurin najeeb ɗin.

koda tazo ƙofar gidan kasa ƙarasawa gurinshi tayi,dan ba ƙaramin kunyar haɗuwa dashi takeba,

Tun fitowarta najeeb yaganta,tunda ya lura bata da niyyar ƙarasowa ne,se yamata full light da fitilar motarshi kasancewar duhun dare yafara.

Hannu tasa takare hasken,jikinta har rawa yake,shiko waya yasa ya ɗauketa hoto ahakan,batare data saniba,horn yamata,da sauri tacire hannun data rufe fuskar,sake yimata wani hoton yayi.

Itako salma ganin yaƙi,dena haskatane yasa ta gane kiranta yakeyi,dan haka cike dajin kunya ta ƙarasa gurin motar.


Muje zuwa.

Surbajo for life.


Post a Comment (0)