ATTAJIRI MAI MATA HUƊU


ATTAJIRI MAI MATA HUDU

A Kwai wani Attajirin mai kudi dake da mata hudu(4). Wannan attajiri yana yana matuqar ji da matarsa ta hudu wato Amarya yana qawatata da kayan ado masu tsada da daraja yana bata kyakkyar kulawa fiye da sauran matansa.
Yana tsananin kaunar matarsa ta uku 3 domin da ita yake shiga taro yana nunawa abokansa, duk da yanajin ts0r0n kada wataran arabashi da ita.
Matarsa ta 2 kuwa itama yana s0 da kaunarta domin kuwa itace abokiyar shawararsa a duk lokacin da ya fuskanci wata matsaloli a harkokinsa, kuma duk lokacin da yazo gunta tana taimaka masa da shawarwari nagartattu.
Ita kuwa matar tafarko 1 ita ke tsananin kaunarsa amman bai damu da itaba duk da yanda take kula da dukiyarsa, kuma tataka babbarawa a matsayin dayake ciki a wannan lokaci ma'ana da ita aka tara dukiyar dayake tinqaho da ita.
Ananan watarana sai yakwanta lalura ta rashin lafiya, yana cikin jinya yakuma ji ajikinsa wannan lalura ba ta tashi bace ba, sai yake gayawa kansa cewa, " inada mata na aure hudu 4 yanzu inna mutu ni kadai xa'a kaini kabarina abarni cikin kadaici, ba wacce zata bini"
Sai yai kiran amaryarsa yace, "Na qawataki da kayan ado na alfarma masu tsada, nakuma baki kulawar da ban baiwa sauran matana ba.. .. yanzu inna mutu zaki yarda kibini?? Tace "Allah ya kyauta" taja tsaki ta tafi. Yaji wannan amsa tata kamar an daba masa kakkaifar wuqa a wuya.
Sai yakira ta ukun 3 yace da ita, "Na soki son da banyiwa sauran matana ba yanzu inna mutu bazaki yarda kibini ba??? Tace masa "haba haka kawai rayuwa fa nada dadi me zaisa kawai na katse tawa na bika?? To barima kaji kana mutuwa Aure zan sake wani zan aure na more rayuwata" tana gama fadin haka tajuya tai tafiyarta.
Sai yai kiran matarsa ta biyu 2 yace mata, "Kece wace nake zuwa da duk wata matsalata ki kuma sharemun kukana, Yau ga wata bukatar tawa ko zaki sharemun kukana kibini inna mutu mu tafi tare??? Tai murmushi tace, "tace wannan lokacin kam banda wani taimako da xan maka sai ins0 kake na ai kaka barzahu" itama daga haka tai tafiyarta,
Saifa hawaye yake yana fadin, "yanzu acikinku bawacce zata bini duk irin halaccin danaimuku a rayuwa? Can sai yaji wata da kusasshiyar murya tace "masa ni zan bika zan zauna tare dakai duk inda katafi" Sa ya dago kai dan yaga wace ke wannan maganar Sai Yaga ashe matarsa ce ta farko saifa kukansa yaqaru yana cewa, "kimun afuwa inama na kula dake alokacin da nake da damar yin haka"
***DARASIN DAKE CIKIN WANNAN LABARIN***
Wadannan mata 4 sune abubuwan dake tare da duk wani mu2m alokacin rayuwarsa ta dunia.
(4) matar nan ta hudu itace gangar jikin mu wacce xamu qawata mubita da mayuka masu tsada da kayan ado masu tsada, da mun mutu wannan ado yazama na banza za a sata akasa ta xagwanye ta lalace.
(3) matar 3 kuwa itace matsayi da mulki dakuma dukiyar da muka tara a dunia, dafa mun mutu ba abinda xai bimu saidai ma wasune xasu gaji mulkin ko matsayin ko kuma dukiyar.
(2) mace ta 2 itace yan uwa da abokan arzikin mu na dunia ayayin rayuwa sune muke kaiwa duk wata matsala tamu munemi shawara gunsu amman da mun mutu mai kwana da gawar mu ma sai anyi daqyar ake samu.
(1) matar kuwa ta 1 itace ruhin mu wanda bamu damu da muqawata shi ba da dai ance physical appearance namu yafito tsaf to bama damuwa da gyara ruhin mu, bayan kuma shine xamu tafi dashi shine ke tare damu ..
To en uwa mu gyara halayen mu kar ya zamana sai munzo mu2wa muxo muna danasani da munyi abu kaza da abu kaza.
ALLAH YASA MUDACE ALBARKACIN ANNABI (S.A.W)
Post a Comment (0)