ABDULKADIR SALADIN 00

ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
ShimfiÉ—a.
Rudolf Carl Van Slatin soja ne ɗan ƙasar Austria, yana ɗaya daga cikin turawan da suka shiga ƙasar Sudan a matsayin 'yan mulkin mallaka a shekarar 1878.
Sai dai kash, Slatin ya shiga ƙasar da ƙafar hagu, domin kuwa bai jima da shiga ba wani malamin addinin Musulunci mai suna Muhammad Ahmad ya bayyana, wanda ya kira kansa da Mahadi - Mahadin da kowa ke jira.
Wannan malami ya janye hankalin ɗaukacin Musulmin ƙasar Sudan, har suka ɗaura niyyar jihadi da Gwamnati wadda take ƙarƙashin Turawa da kuma Larabawan Misira. An gwabza yaƙoƙi da dama tsakanin Gwamnati da Mahadi (idan ba ku manta ba, a littafin da muka gama karantawa na SHAIHU UMAR, an yi batun wannan tarzoma ta Mahadi da Gwamnatin Sudan).
Slatin na cikin sojojin da suka faɗa hannun Mahadi. Bayan ya kuɓuta ne, ya rubuta wani littafi mai suna FIRE AND SWORD IN THE SUDAN, a cikin wannan littafi ne ya bayyana yadda Mahadi ya ɓulla a Sudan da yadda ya yi ƙarfi, da irin rayuwar da ya yi a hannunsa yayin da ya zama fursunan yaƙi, da yadda ya tsira.
Wannan littafi ne Malam Nuhu Bamalli ya fassara mana zuwa Hausa, wanda ya sanya wa suna ABDULKADIR SALADIN, kuma shi ne littafin da za mu fara kawo muku idan Allah ya kai mu ranar Asabar mai zuwa.
Littafi ne na tarihi, ba ƙagagge ba, duk labarin da ke ciki gaskiya ne. Littafi ne mai cike da ilmantarwa da nishaɗantarwa, da tausayi da kuma ban dariya, tamkar littafin MUNGO PARK MABUDIN KWARA. Kafin lokacin, ga ɗanɗano jiran rabo:
...
"Jumma’a duk za a yi holin mayaka. A kan jeru a yi sahu uku, ko wanne da shugabansu. Bayan an shirya, Mahadi ya kan zo ya tsaya a tsakiya. Sai a ba da odar gaisuwa, mutanen nan dubbai kan dubbai, duk su bude baki gaba daya su gai da Mahadi. Gumjin sai wanda ya ji! Bayan sun yi shiru, sai shi kuma ya Shiga kewaya su yana sa musu albarka. A irin wannan farati babu karairayin da soja ba su fada. Wani ka ji ya ce ya ga Annabi a bisa taguwa kusa da Mahadi suna tadi, wani ya ce ya ji murya daga sama tana sa wa sojan Mahadi albarka, tana kuma tabbatar musu da nasara. Wani kuwa sai ya ce ya ga mala'iku suna yi wa Mahadi laima da fikafikansu don kada ya ji zafin rana. Kai, ga su nan dai, maganganu barkatai."
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D8EBAC33
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

1 Comments

Post a Comment