ABDULKADIR SALADIN 01

1. ABDULKADIR SALADIN​
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
NA TAFI SUDAN
Cikin watan Yuli, 1878, na sami wasika daga Janar Gordon ya ce in je wurinsa a Sudan in kama aiki. Ni a lokacin nan ina soja ne a kasarmu Austria a Turai, da darajar hafsa.
Sudan ba bakuwar kasa ce gare ni ba, don da ma na taba zuwa cikin 1874, har na yi ’yan yawace yawace a cikinta. Na san dutsen Nuba, na dan zauna a Delen tare da wadansu Turawan Mishan. Ina ma cikin kasar ne tawaye ya tashi na Larabawan Hawazma. Da ya ke ni bako ne, sai aka ce maza in rabu da wannan hargitsi in tafi Lubayya, a Lardin Kordofan, inda babu tashin hankali. Dalilin wannan hargitsi, wai haraji ne ya yi wa talakawa yawa, suka yi wa gwamnati tawaye. Ko da kura ta lafa, ban koma Delen ba, sai na nufi Darfur.
A lokacin nan, babban gwamnan kasar Sudan wani mutumin kasar Masar ne wai shi Isma’ila Pasha Ayub, don Sudan cikin mulkin Masar ta ke. Yana zaune a El Fashar, babban birnin Darfur. Ina ta murna na fito daga hadarin ’yan tawayen Hawazma, ina ta dokin in kai El Fashar, amma ko da na iso Kaga da Katul, me na tarar ? Na sami gwamnati ta yi oda wai kada bakon da ya shiga kasar Darfur, don kasar danya ce, ba a dade da bishe ta ba. Jin haka sai na tausa Iinzami, na juya sai Kahartum. A can na sami Turawa da yawa. muka saba. A cikinsu har da Likita Emin, wanda Larabawa ke kira Emin Pasha.
Duk lokacin nan, Janar Gordon shi ne gwamnan kasashen da ke kudu da Sudan, yana zaune a Lado. Sai ni da Emin muka rubuta masa takarda, muka gaya masa ga halin da mu ke ciki, kuma ya taimake mu da shawarar yadda za mu yi. Bayan wata biyu, sai ga amsar Gordon, cewa in yi maza in tafi Lado. Amma kuma kafin amsar ta zo na sami wasika daga garimmu Vienna a Turai, cewa in koma gida. Ga shi ba ni da lafiya a nan, ga shi kuma ina da sauran shekara guda kafin lokacin alkawarina na aikin soja ya cika a gida. Nan fa na shiga sakar zuci, in je gida ne ko in je wajen Gordon ? Daga karshe dai na dauki shawara ta farko, na amsa kiran iyayena. Emin Pasha kuwa ya amsa kiran Gordon, muka yi shiri muka tashi tare. Shi ya nufi kudu wajen Gordon, ni kuwa na ratsa ta Masar, har dai na kai Turai cikin 1875. Amma kafin mu rabu, na roki Emin Pasha ya koda ni a wurin Gordon. Ya kuwa yi kuda mai kyau, har sabo da kudarsa ne na sami takardan nan ta kiran kama aiki bayan na koma Turai da shekara uku.
Emin ya tashi a sa’a, don da isarsa Lado sai aka ba shi daraja ta 'Bey’, aka nada shi gwamnan kasar. Da Gordon ya bar Lado ma shi ya gaje shi, ya haye kujerar babban gwamnan kasashen kudu. Bai sauka ba sai cikin 1889, da Mr. Stanley ya karbe shi.
Takardar Gordon ta kirana in komo Sudan ta same ni a lokacin nan kasar Austria tana cikin yaki. Sai na kosa a kare wannan hargitsi, amma ban sami barin Turai ba sai da yaki ya kare. Da yaki ya kare, bataliyata ta komo gida, ni kuma aka fisshe ni daga soja farofaro, na zama dan rijau. Sa’an nan ne aka ba ni iznin komowa Afirka.
A lokacin nan dan'uwana Henry ba ya gida, sabo da haka na yi kwana takwas kurum a Vienna, na yi ban kwana da sauran dangi, na bar gida ran 21 ga Disamba, 1878. Ashe ban sani ba da kafar hagu na fita gida. Ashe daga wannan fitar sai na shekara dai dai har goma sha bakwai kafin in maido fuskata wajen gida. Ban kuma sani ba, ashe wulakanci mara asani, da zilla mara iyaka, da azaba mara misaltuwa, su ke kirana!
A lokacin nan ban kula da kome ba, ina saurayi ne dan shekara ashirin da biyu kawai. Ban da balli da kutsa kai cikin duniya, ba na sha’awar kome.
Na dai taka jirgin ruwa na hau, ga mu nan sai Alkahira, babban Birnin Masar. Da isa, sai ga waya daga wani Bature wai shi Giegler Pasha. Ya ce gwamnatin Masar ta nada shi babban mai duba waya a Sudan, har zai fara fita rangadi ya duba tsakanin Massawa da Kahartum. Ya ce zai tafi tare da ni har Suakin daga nan mu rabu, shi ya nufi Massawa a jirgin ruwa, ni kuma in nufi Berber bisa rakumi. Na yi murna da wannan taimako, na kintsa, muka tashi. Da na isa Berber, sai na tarar har Gordon ya aiko da Jirgin ruwa ya dauke ni. Na shiga, na isa Kahartum ran 15 ga Janairu, 1879. Tibdi, na ga karyar liyafa a wannan wuri! Nan da nan Gordon ya sa aka shirya mini wani gida mai kyau kusa da fadarsa, aka hada ni da wani wai shi Ali Effendi, kome na ke so ya yi mini.
Cikin watan Fabrairu, Gordon ya nada ni mai duba sha’anin kudi. Aka ce in shiga rangadi ina binciken dalilan da suka sa mutanen Sudan kin biyan haraji, ko da ya ke harajin nan ba yawa ya yi musu ba. Da na tashi, na buga, sai Sennar da Fazoa, daga nan har duwatsun Kukoli da Regreg. Na bincika na kawo wa Gordon dalilan da na samu. A cikin labarin da na bayar, na ce ni a ganina babu adalci ga hanyar fasa haraji ko kadan. Dalili kuwa, domin talakawa, manoma, su a ke labta wa haraji, tajirai kuwa sai su ba masu fasawar hanci, su sa musu kadan. Wannan ya sa dukiya da yawa ba sa mata haraji, matalauta kuwa a dankara musu. Tushen hargitsin ke nan.
Bayan yawan haraji kuma, hanyar da a ke karbarsa ba ta da kyau ko kadan. Akwai azaba da wulakanci da firgitarwa kwarai wajen karbar, don soja ke karba. Saboda haka su ba su kula da kome ba, sai su wulakanta talakawa don su ba su dukiya. Wanda ya ba da ci, ya huta. Wanda bai bayar ba, ya shiga uku. A cikin bincikawar da na yi kuma, na tarar duk ma'aikatan gwamnati, Turkawa da mutanen kasar, ba sa biyan harajin kansu, ba sa biyan na dukiyarsu. Da na nemi dalili, sai aka ce wai don aikin da su ke wa kasa shi ya sa aka yafe musu. Na ce wannan ai maganar banza ce, tun da ya ke ba kyauta su ke wa kasa aiki ba, ana biyansu albashi. Jin haka, irin ma’aikatan nan suka diram mini kamar sa cinye ni. Amma nan da nan na sa aka tsare wadansu daga cikinsu sai da suka biya.
Da na isa Mesalamia, nan na ga wata bakar hanya ta neman kudi. Na ga tajirai suna tara yaran mata, suna ba da hayarsu kamar yadda a ke hayar basukur. Wannan mummunar safara tana kawo musu kudi kwarai, amma ta yaya za a iya sa wa masu yin ta haraji? Na yi matukar tunani, amma na kasa gano hanya mai fita.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D8EBAC33
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada


Post a Comment (0)