ABDULKADIR SALADIN 02

2. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Da na isa Mesalamia, nan na ga wata bakar hanya ta neman kudi. Na ga tajirai suna tara yaran mata, suna ba da hayarsu kamar yadda a ke hayar basukur. Wannan mummunar safara tana kawo musu kudi kwarai, amma ta yaya za a iya sa wa masu yin ta haraji? Na yi matukar tunani, amma na kasa gano hanya mai fita.
Da na ga dai babu yadda zan iya warware al’amarin don muninsa da ban kunya tasa, sai na aika da takarda, na ce ba na yin aikin dungum dungum. A lokacin nan Gordon ya tafi Darfur sabo da binciken wani yaki da aka tasam ma yi da Sulaiman Ibn Zubairu Pasha, ya bar Giegler shi ne wakilin gwamna. Sai na rubuce labarina duk, da aikin da na iya yi, da wanda na kasa yi, na aika wa Gordon. Kwana kadan sai ga waya, an hutasshe ni daga aikin mai duba sha’anin kudi.
Kada ka so ka ji zuciyata da na ga wannan waya! Aikin dai dungum ya juyar mini da kai, don a ganina babu kome cikinsa, daga barna sai zalunci. Bayan 'yan kwanaki kuma, sai ga wata waya daga Gordon, cewa ya nada ni mudir na Dara, watau babban kwamanda. Aka ce in yi maza in je Dara don in shirya yakin da za a yi da Sultan Harun, wanda ya kakufe shi dai sai ya kwato kasar ubansa daga hannun Masar. Amma Gordon ya ce kafin in zarce Dara, yana so mu sadu da shi a Farin Nil, tsakanin Lubayya da Tural Hadra.
Da na isa, aka ce bai iso ba tukuna, sai na bi shi a bisa rakumi. Na same shi ya sauka yana hutawa a karkashin wata bishiya. Ya gaji tubus, kuma yana fama da wadansu miyaku a kafafunsa. Aka yi katari ina tafe da ’yar barasa, na ba shi ya sha, sa’an nan ne ya ji karfi karfi har muka yi gaba. Nan tare da shi na sadu da mutum biyu, da Hasan Pasha, babban gwamnan Kordifon da Dadur na da, da kuma Yusuf Pasha Shellali. Da isarmu Tura sai muka shiga jirgin ruwan da zai dauki Gordon don mu yi shawarar abin da zan yi. Muna zaune kafin a shiga shawarwari, sai na yi wata ’yar wauta ta rashin sani. Kusa da ni, nan Yusuf ke zaune, a can kusa da shi kuma ga modar shan ruwa. Kishi kuwa ya kama ni. Sai na ce Yusuf ya miko mini ruwa a ciki in sha. Jin haka, sai Gordon ya yi dan murmushi, ya dube ni ya ce mini da faransanci, “Ba ka san Yusuf Pasha shi ne gaba da kai kwarai ba, ko don ka gan shi baki haka ? Kai mudir ne kurum, sabo da haka ba daidai ba ne ka ce ya miko maka ruwa ka sha.” Nan da nan sai na juya gun Yusuf na ce ya yafe ni. Sai ya ce wannan ba kome, a kullum shi yana farin cikin ne ya taimaki dan'uwansa, ko wane ne.
Da muka zauna a cikin jirgi muka shiga shawara, Gordon ya ce yana so in yi iyakar kokarina in kashe wannan hargitsi na Sultan Harun. Ya ce Harun ya hana kasa zama lafiya a shekarun nan, ko yaushe sai zubad da jini ya ke ta yi. Bayan mun kare shawara, muka yi ban kwana. Gordon ya ce, “Slatin, sai wata rana ke nan. Na tabbata kome tsanani za ka jure, kuma za ka yi iyakar karfinka. Je ka, Allah ya taimake ka. Kila zan tafi Ingila ba da dadewa ba, ya yiwu mu sadu a can.” Wannan ita ce magana ta karshe da muka yi da Gordon, muka rabu. Ba mu sani ba, ko wannemmu da irin tasa wahalar da ke jiransa. Na yi masa godiyar duk irin taimakon da ya yi mini, muka yi sallama. Zuwa can sai na ji usir, fifir, firr, am ba jirgin ruwa odar tashi. Aka motsa injin, ina ta kada wa Gordon hannu har suka bace. Ashe iyakar ganina da shi ke nan har a busa kaho!
Washegari da safe, ni kuma na yi harama na tashi na nufi Dara. A hanya na sami waya daga gwamnan Kordofan, Ali Bey Sherif, cewa Sulaiman Zubairu ya fadi a fagen fama a Gara, ran 15 ga Yuli, 1879. Maganar Gordon ta tabbata ke nan da ya ce lalle ne ko dai Sulaiman ya bi ko a kashe shi.
Zubairu Pasha, uban Sulaiman, bayan da ya ci Darfur sai ya nufi Alkahira a Masar. Ya bar dansa Sulaiman ya lura da sha’aninsa a Shakka. A cikin 1877 Gordon ya nada Sulaiman gwamnan Bahrel Ghazal. Ana nan sai fada ya tashi tsakanin Sulaiman da wani amintaccen ubansa wai shi Idris Ebtar. Tun can asali kuwa da kabilar Zubairu da ta su Idris ba shiri a ke ba. To, kila dai ana iya cewa wannan dan tunzuri na tsakanin Sulaiman da Idris, shi ne asalin duk tashin hankali da jidalin da aka yi ta fama da shi a Sudan.
Da farko abu kamar ba’a, har dai ya kai ga shata daga. Idris ya yi maza ya kai kukansa ga gwamnati a Kahartum. Nan da nan kuwa gwamnati ta aika masa da gudummawar soja. Aka shiga ba-ta-kashi, har dai aka ci karfin Sulaiman, aka kama shi aka rataye shi. Daga cikin sarakunan yakin Sulaiman, akwai wani wai shi Rabeh. Da dai ya ga alamar rana za ta baci musu, sai ya janye kansa da rundunarsa ya yi yamma. Shi kuma ya dinga tafiya yana yaki yana waso, har ya kai Tabkin Cadi. Nan ya gina daula babba a Barno, a tsakiyar Afirka.
ZAMANA A KASAR DARFUR
Na bar Lubayya cikin watan Yuli, 1879, tare da Likita Zurbuchen, dubagari. Ya ce an aike shi Habasha ne wurin sarkin kasar. Da muka isa Om Shanga, muka tarar garin ya cika makil da tajiran bayi, wadanda suka rika taimakon Sulaiman da makamai. Da aka ci shi, su kuwa aka fasa su suka watsu cikin Sudan.
Na ga wani abin mamaki a wannan gari. Da zuwana, sai na ga mutane suna ba ni girma fiye da sauran abokan tafiyata. Ko da na tambaya, sai na ji wai ashe labari ya watsu, cewa ni kanen Gordon ne. Na rasa shaidanin da ya kitsa wannan karya, ko kuwa don sun ga kwayar idona irin ta Gordon ce, kuma ba ni da gemu kamarsa, oho! Nan da nan mutane suka rufe ni, kowa yana kawo kukansa, suna so in taimake su wurin wana, wanda ya jawo musu wannan masifa ta kora. Na ce Om Shanga ba a cikin kasata ta ke ba, sabo da haka ba na iya taimakonsu. Amma duk da haka na yi wani karambani daya, har na kashe aure. Kafin im fadi yadda al’amarin ya faru, ina so im bayyana cewa na keta haddin shari’ar Musulunci, na kuma yi abin da addini bai ce ba. Amma kila duk wanda ya karanta ya ji, zai iya gane dalilin da na yi hakanan. Ko fa hujjata mai karfi ce, ko ba mai karfi​ ba, na bar wa mai karatu sani.
Yadda abin ya faru, tajirai korarru ne da dama suka yi ta zuwa wurina, suna roko in shiga tsakanin wani saurayi da wata mace, da ke kiran kanta matarsa. Yaron duk shekarunsa goma sha tara ne kadai, shi kuwa dan mutanen Kahartum ne. Suka ce kafin ya bar Kahartum, an yi masa baiwa da wata duburwa kyakkyawa. Iyayen yarinyar sun yarda da auren, amma suka ce sai ya tafi ya nemo kudi tukuna kana a daura. Da ya iso Om Shanga, sai wata tsohuwa ta gan shi. Ta ce kuwa babu abin da zai raba ta da shi. Ta lallashe shi don tajira ce, tana nuna masa gatanci iri iri, har dai ta ciwo kansa, ya aure ta. Labari ya kai kunnen iyayensa da iyayen tashinsa a Kahartum, hankalinsu da na budurwan nan ya tashi gaya. Saba da haka tajiran suka ce suna so in raba yaron nan da makirar tsohuwan nan. Mene ka gani abin yina, malam, mai karatu ?
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D8EBAC33
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada


Post a Comment (0)