ABDULKADIR SALADIN 03

3. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Sabo da haka tajiran suka ce suna so in raba yaron nan da makirar tsohuwan nan. Mene ka gani abin yina, malam, mai karatu ?
Na dai daure na kira yaro. Ko da ganinsa, na san ba tsohuwa ba, ko yarinyar mace ce ta so shi. Ga shi dai kyakkyawan gasken gaske, sankacece, kakkarfa! Na ja shi waje guda, na daure fuska na yi masa magana. Na nuna masa wautarsa da ya auri kwasgamar tsohuwa, bayan kuwa ga shi can har an yi masa baiwa da budurwa a garinsu, ya bar ta tana ta kuka a kullum. Na ce lalle ya yi maza ya koma gida, ya rabu da wannan tsohuwar banza.
Yaron ya tsaya shiru, ya daga kansa sama, sa’an nan ya saukar. Ya ce ya ji, zai tafi wurin alkali ya sake ta. Nan kuwa ni na rigaya na ga alkali, na gaya masa in yaron ya zo gare shi, ya san yadda ya raba su da tsohuwan nan, ba da ta da hankalinta ba. Dalili, don ni ba na son rabuwar ta zama da tashin hankali a ciki. Na kuma fada wa ’yanuwan yaron, da ce an raba auren, su tura shi Kahartum. Har wa yau na fada wa wakilin gwamnati a Om Shanga, cewa lalle a fada wa yaron ya bar garin cikin kwana biyu. Shi kansa yaron na gaya masa, kome ya ga dama ya fada wa tsohuwar game da ni, na yarda, amma dai ya rarrashe ta ta ba shi kudin tafiya gida. Duk abin nan ban sani ba ashe wuta na ke shirin zuba wa kaina kasaitacciya.
Can wajen karfe hudu na maraice, ina kwance a wani dan gado ina hutawa, sai na ji muryar mace. Da na kara kasa kunne, sai na ji alamar mai maganar tana cikin hushi ne, tana cewa lalle tana so ta gan ni yanzu yanzu. Ba na bukatar tambaya, da ma na san ko wace ce. Sai na tashi zaune, na kintsa, na daure fuskata, don na san ba za a aikata arziki ba. Na ce da odalena ya shigo da ita. Likita Zurbuchen ya firgita kwarai, har ya ce shi dai zai fita dag a dakin. Amma ni kaina ba so na ke a bar ni mu biyu da wannan tunzurarriyar tsohuwa ba, sabo da haka na roke shi, ya yarda ya zauna. Da kunno kanta cikin dakin, suka yi arba da Likita Zurbuchen, ta ko tasam masa haikan kamar kura ta ga nama. Ita a zatonta ni ne. Tana kara, tana fiffige gashin kanta, bakinta na kumfa, tana cewa, “Karyarka ta yi karya, dan la'anannen munafuki. Babu mai raba ni da mijina. Ka yi kadan! Matarsa ce ni, shi kuma mijina ne. Aure mu ke yi a kan sunna, ba wajoko mu ke ba. Ban yarda ya sake ni ba !"
Likita Zurbuchen ya kadu gayar kaduwa, ya fada mata cikin dan guntun larabcin da ya ke ji, ya ce shi ba ruwansa, ni ke da ruwa da maganar, ya nuna ni. Wayyowo! Nan da nan kura ta komo kaina. Matar ga ta katuwar gaske, ko da ta tsaya a gabana, sai na ji hantata ta kada. Lokacin da ta shigo ban ga fuskarta sosai ba, don tana da lullubi. Amma da hushi ya yi hushi, ba ta san lokacin da lullubin ya kware, har kallabinta ya fadi ba. Ko da na dube ta, sai na ga fuskan nan babu kome cikinsa sai tamoji. Tana da tsagen kwale uku a taya-ni-muninta, karkashin ko wane ido. A hujin hancinta da jan dutse, a kunnenta ga 'yan kunnen gwal suna lilo. Gashin kanta duk ya yi bidi-bidi, hurhura ta tasam masa haikan. Ni dai ban taba ganin mace da munin wannan ba. Wai duk abin nan ban yi mata kallon tsabta ba ke nan, don ta ruda ni da bambami. Ni dai ban ce mata kala ba, sai da na ga ta lafa, sa'an nan na ce, “Na ji duk abin da kika ce, amma a wannan magana ai babu ta cewa a ciknta. Mijinki dai bako ne, lalle kuwa ya bar garin nan cikin kwana biyu ke kuwa da ya ke nan garinku ne, ban yarda ki fita ko kofa ba. Na ga alamar ba ki son a kashe aurenku, amma ki tuna a shari’ar Musulunci, igiyar aure tana hannun miji ne, ba hannun mace ba, in ya saki shi ke nan. Watau namiji ke da ikon sakin matarsa, ba mace ta saki mijinta ba."
Ta ce, “Da ba domin kai ka bata zamammu ba, har abada ba zai bar ni ba. Allah dai ya tsine ranar da ka zo garin nan!”
Na ce, “Na roke ki kada ki sake fadan haka. Ke tajira ce, sabo da haka ban ga dalilin da za ki rasa wani namiji wanda ma ya yi daidai da shekarunki ba."
Ta ce, “Kada ka gaya mini zancen wani miji. Ko ji ka yi na ce ina son wani, ga mijina? Zancen banza ke nan !”
Ganin za ta zarce, sai na kirshe, na daka mata tsawa, na ce, “Ke, yi wa mutane shiru hakanan! 'Yanuwan mijinki su ke so ya rabu da ke. Sun ce da kudi kurum ki ke rudinsa har ya yarda yana zaune da ke. To, yanzu dai an raba ku, kome za ki yi, je ki yi. Ke ko kunya ba ki ji, tsohuwa kamarki ki auri wannan yaro, sa'an jikanki? Tafi ki ba ni wuri !"
Wai, wai, wai! Ai sai ka ce na kwara mata wuta, wai na kira ta tsohuwa. Ta haukace sosai, ta fige kallabinta ta yar, tana bugun kirjinta. Ba don dai odalena ya ji hargowar ta yi tsanani ya zo ya fita da ita ba, ban san abin da zai faru bayan jefad da kallabin nan ba. Odalen ya ce mata abin nan da ta ke yi abin kunya ne ainun, har mutane suna yi mata dariya.
Washegari dai mijinta ya bar garin, na kuwa tabbata ta dade tana bakin cikin rabuwa da shi. Da haka dai muka rabu da wannan tsohuwa, na bar Om Shanga bayan kwana biyu. Bayan yan shekaru, sai muka sadu da yaron. Ya je ya auri yarinyan nan, har sun haihu. Ya yi mini godiya gaya sabo da fid da shi da na yi daga kumbar matan nan.
Ran nan kwaram ina zaune, sai ga waya daga wurin gwamnati, aka ce, “Zauna kan shiri. Wani mutum, malami, wai shi Muhammed Ahmed, ya auka wa Rashid Bey, babu gaira babu dalili. Ya yi kaca kaca da shi da sojansa. Wannan tashin hankali yana da ban tsoro. Yi kokari ka hana mutane a kasarka bin wannan dam bore.” Sai na mai da amsa na ce, “Waya ta same ni. Zan yi iyakar kokarina in hana mutane bin dam bore.”
Na dan jima da jin labarin wannan dam bore. An ce yana fada wa mutane kada su bi mulkin kowa, su bi shi kurum. Ashe ni ma kaina zan shiga cikin azabarsa, har daure ni zai yi cikin sarka !
Kafin im fadi irin jidalin da gwamnatin Masar ta sha, kafin ta i wa wannan Mahadi, bari mu taba dan tarihinsa mu ga yadda ya tsiro.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D8EBAC33
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada


Post a Comment (0)