ABDULKADIR SALADIN 15

15. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Abu Anga ya dube ni ya ce, “Abdulkadir, ka ci amana. Ka yi alkawarin za ka yi biyayya ga Mahadi, to, wajibi ne gare ka ka cika alkawarin nan. Wajibi ne gare ka ka bi umurni, ka aikata abin da aka ce maka ko ba dadi. Haka ne, ko ba haka ba ?"
Na ce, “Haka ne! Kai kanka Abu Anga ka sha ba ni umurni daga Halifa ko Mahadi, ka kuwa ga na cika.” Abu Anga ya ce, “To, am ba ni umurni in saka ka a sarka, amma ban san dalili ba.” Yana rufe baki sai Haji Zubairu ya fizge takobina ya jefar, ya kuma figi hannuwana ya ce in tashi tsaye. Na ce, “Kai Haji Zubairu, shiga taitayinka! Ni ba fada ya kawo ni nan ba. Don me za ka yi mini wannan irin kamu na wulakanci ? Abu Anga, kai sai ka cika umurnin magabatanka, amma ba wani kawai ya zo ya tursasa ni haka ba.”
Abu Anga ya ce mini, “Tafi tantin can. Kai Haji Zubairu da saura duk ku bi shi.” Ko da jin haka na san ashe da gaske Abu Anga ke yi. Na wuce, mutum shida suna biye da ni sai cikin tanti. Haji Zubairu ya ce in zauna a kasa, na zauna. Sai na ga ya jawo wata katuwar sarka mai mundaye biyu, an soka kafafuna a ciki, an sa hamma an buge bakinsu, an kuma bama mini wata munduwar, mai sarka, a wuya. Don nauyin wannan munduwar, da kyar na ke iya motsa wuyana. Ina dai kallo ban ce uffan ba. Haji Zubairu, ya fice abinsa ya bar ni daga ni sai masu gadina. Aka jefa mini wani keson tabarma, aka ce abin kwanciyata ke nan. Na zama fursuna !
Na yi ajiyar zuciya, na shiga kogin tunanin zarafin dunjya, raina ya baci. Da farko na ji haushin kaina. Na rasa sakarcin da ya hana ni tserewa in shiga cikin Kahartum. Kuma duk bayan wannan, ba abin da ya kara bata mini rai kamar ban san irin abin da miyagun nan suka tanadar mini ba. Na ga azabu iri iri da aka yi wa makiyan Mahadi, galibinsu kuwa ma gwamma mutuwa da su. Tun ran da na fada hannun Mahadi na ke taka-tsan-tsan, ba na yarda im bata hankalin kowa don kada a bata nawa. Na daure wuya, na daure wulakanci, wai dai don in tsira da raina da mutuncina.
Yau ga shi babu gaira babu dalili, an karya mini mutunci. Ni da ke gwamnan kasar Durfur duka, ni da ke da soja da bindigogi, ni da ke ce a yi, a yi, in ce a bari, a bari, ga ni cuku cuku cikin sarka har wuya !
Can bayan kamar sa’a guda, sai na hango mutane da fitila sun nufo tantina. Suna shigowa, sai na ga Halifa Abdullahi ne. Na yi kokari na mike da kyar, nauyin sarka kamar zai karya mini wuya. Halifa ya dube ni ya ce, “Abdulkadir, ka saduda da hukuncin Allah, ko kana da wani tasiri ?" Na ce, “Ai ni ba ni da wani tasiri ya Halifa, duk yadda Ubangiji ya yi da bawansa tilas ya hakura.” Halifa ya ce, “Takardarka da ka yi wa Gordon ita ta ja maka. Mu da mun zaci ka bi mu har cikin zuciyarka, amma wannan takarda ta nuna da gindin gyare cikin sha’aninka.” Na ce, “Lalle gaskiya ne, na yi wa Gordon takarda, amma Mahadi ya sa ni.” Halifa ya ce, “Amma Mahadi bai ce ka rubuta abin da ka rubuta ba”. Na ce, “Daidai yadda ya ce, haka na rubuta. Amma duk wannan gardama sai a bar ta. Ni dai rokona da kai daya ne, ka dauki hanyar adalci, ka rabu da ashararancin magabta.” Kafin in karasa ya fita, ya yi tafiyarsa.
Aka bar ni daga ni sai tunanina kuma. Lokacin da mu ke tadi da Halifa har na manta da azabar matsin sarka, sai da ya fita zafin ya komo. Wannan daren dai ko runtsawa ban yi ba. Gari na wayewa, rana ta fara kunnowa, sai ga Abu Anga ya shigo, yara na biye da shi dauke da abinci. Ya zauna a kan tabarmata, aka ajiye abincin a tsakiyarmu. Abinci ne mai kyau, da su naman tunkiya da shinkafa da madara da zuma da gamsasshen naman kaza. Ya ce, “Bismilla.” Na ce masa ai ba na jin cin kome. Ya ce, “Ya Abdulkadir, tsoron me ka ke haka, har da za ka kasa cin abinci ?“ Na ce, “Ba tsoro ba ne, yunwa ne ba na ji, amma in zato ka ke kin ci na yi, bari in yi loma biyu." Na gutsuri loma biyu, na murtsuke hannuna. Abu Anga ya ce, “Halifa ya yi fushi kwarai da gaske jiya da ya ga ba ka saduda ba, duk da wannan abin da aka yi maka. Ya ce a tsaye ka yi magana da shi, ko sunkuyawa ba ka yi ba, balle ka tuba.” Na ce, “Haba Abu Anga, ta yaya zan rusuna in tuba don laifin da ban yi ba ?"
AN KASHE GORDON
Abu Anga ya gaya mini gobe za a tashi a kara turawa gaba, har zuwa bakin kofar Kahartum. Da sassafe kuwa sai aka kada gangar tashi. Ni dai kowa ya sani ba na iya ko cira kafa don nauyin sarka. Sabo da haka sai aka nannade sarkar a jikina aka sa kattai suka dauke ni suka dibiya bisa jaki, suka rirrike ni. Da haka muka tafi har kofar Kahartum. Lokacin da mu ke tafe, abokaina da idon sani, in sun dube ni, sai su sunkuyad da kai kurum su wuce. Babu mai ikon tsinkawa da ni, suna gudun dauri ko bulala, ko ma kisa dungum.
Da muka isa kofar gari aka sauka, Mahadi ya sa aka kewaye Kahartum duk, ba shiga ba fita. Abu Anga da Fatarel Maula aka ce su fada wa barikin Omdurman. Nan da nan suka yi wa barikin kaca-kaca, har suka nutsad da jirgin gwamnati daya da ke kan Kogin Nil. Ni a lokacin nan babu wanda ya kula da ni. Da ma mai ’yar hananata Abu Anga ne, to, yanzu shirye shiryen yaki sun sha masa kai. Yunwa kawai ta kusa i mini, balle kuma azabar sarka.
Wata rana dai, da na ga na yini, na kwana ban ci kome ba, kuma zan sake kwana hakanan, sai na aiki wani wurin matar Abu Anga don ya roko mini abin karin kumallo. Na yi haka don ganin amincin da ke tsakanina da mijinta ne. Da yaron ya fada mata, sai ta ce, “Shi Abdulkadir din ne ya aiko ka ?" Yaro ya ce, “I.” Ta ce, “Watau shi nan ya saki baki ne mu yi ta ba shi abinci, bayan ga kawunsa Gordon yana ta sako wa Mahadi wuta ? Ai da ya shawarci kawunsa ya bi, da yanzu ba ya cikin sarka da wahalar yunwa haka. Tafi ka ce masa an hana.” Ko da yaro ya zo ya mayar mini, ban zargi matan nan ba, domin ita ma da gaskiyarta. Sabo da haka sai na sa hakuri.
Wata rana ina zaune, kawai haka kuma sai ga wani yaron Halifa ya zo da mari ya sake buga mini a kafa. Wannan abu ya ba ni mamaki kwarai, ga sarka a kafa, ga ta a gindi, ga ta a wuya. Amma duk ba su isa ba, sai an kara mini mari a kafa, ban kuwa yi laifi ba. Ni dai ban ce kome ba, na mika masa kafa ya kare buge bugensa ya fita, na ci gaba da jan tasbahata, wai ni Musulmi! Ba na magana da kowa, wani ba ya yi da ni, duk an hana. Iyakan abokan tadina sai masu gadina, ko su kuwa sai in ’yantattun bayi ne. Amma in Larabawa ne, ba ni da ikon in ce musu ko sannu.
Wani dare ina zaune, sai ga wani yaron Halifa ya zo, ya ce ubangidansa ne ya aiko shi ya gaya mini yana zuwa. Na yi mamakin abin da zai kawo Halifa gare ni a wannan lokaci. Na san dai ba alheri ba ne, don babu niyyar alheri a zuciyar Halifa Abdullahi zuwa gare ni. Can, sai na hango mutane tafe da fitilarsu. Suna shigowa na mike. Kafin in gai da Halifa sai ya ce mini, “Abdulkadir, zauna. ” Na zauna, shi kuma aka shimfida masa buzu kusa da ni ya zauna. Ya ce, “Na zo gare ka ne. Ga wata takarda na samu, ina so ka fada mini abin da ke cikinta bisa gaskiya. Ka yarda ?" Na ce na yarda. Ko da na duba takardar sai na ga rubutun Gordon ne, ko da ya ke babu sa hannunsa. Na haska gaban fitila, sai na ga Gordon ne ya rubuta wa wani, cewa yana da soja 10,000, kuma zai iya tsare Kahartum har karshen Janairu.
Da na gama karantawa, Halifa ya ce, “Me aka ce ?" Ni kuwa sai na ce, “Wannan takarda Gordon ne ya rubuta ta da hannunsa, amma da faransanci ya rubuta, ni kuwa ba na jin faransanci.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Post a Comment (0)