ABDULKADIR SALADIN 14

14. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
....
Jumma’a duk za a yi holin mayaka. A kan jeru a yi sahu uku, ko wanne da shugabansu. Bayan an shirya, Mahadi ya kan zo ya tsaya a tsakiya. Sai a ba da odar gaisuwa, mutanen nan dubbai kan dubbai, duk su bude baki gaba daya su gai da Mahadi. Gumjin sai wanda ya ji! Bayan sun yi shiru, sai shi kuma ya shiga kewaya su yana sa musu albarka. A irin wannan farati babu karairayin da soja ba su fada. Wani ka ji ya ce ya ga Annabi a bisa taguwa kusa da Mahadi suna tadi, wani ya ce ya ji murya daga sama tana sa wa sojan Mahadi albarka, tana kuma tabbatar musu da nasara. Wani kuwa sai ya ce ya ga mala’iku suna yi wa Mahadi laima da fikafikansu don kada ya ji zafin rana. Kai, ga su nan dai, maganganu barkatai.
AN JEFA NI A SARKA
Ran nan labari ya zo, cewa Gordon ya fada wa Abu Girga da yaki, watau barden Mahadi wanda ya je ya zauna a kofar Kahartum, ya kuwa yi masa kaca-kaca. Mahadi bai ko kula ba. Shi ya tabbata karya Gordon ke yi, in dai Sudan ce, a hannunsa ta ke. Kafin kuwa gwamnatin Masar, ko ta wata kasa, ta kwace, sai an yi kare jini, biri jini. Amma duk da haka ran nan sai Mahadi ya tashi wani mutumin Greek wai shi George Calamatino da takarda, ya kai wa Gordon. Ma’anar takardar, watau ya gaya wa Gordon cewa babu amfani ya ce zai kame a Kahartum, gwanda ya zo ya nemi lalama, a yi sulhu. Ta haka ni ma na samu na aika da tawa ’yar guntuwar wasikar zuwa ga Gordon a boye. Ana cikin haka, sai watan azumi ya kama, aka tashi da azumi, kome kuma ya yi sanyi. Watan yana mutuwa, aka sha ruwa, sai Mahadi ya tattara iyakar Karfinsa duk, ya gaya wa jama’a, cewa Annabi ya umurce shi da ya je Kahartum ya kwato ta daga hannun Gordon.
Nan da nan cikin ’yan kwanaki kadan kusan a ce Sudan duk ta taru a Rahad. Da shiri ya gamu, muka tashi ran 22 ga Agusta. Aka kasa runduna uku, ko wacce aka fada mata hanyar da za ta bi. Haka aka dunguma aka doshi Kahartum. Bayan tafiyar kwana uku muka isa bakin garin. Ran nan da maraice. bayan duk mun kare kafa tanti, sai ga manzo, ya zo ya ce wai Mahadi yana kirana. Nan fa zuciyata ta shiga sake-sake, don ban san irin abin da wannan kiran zai jawo mini ba. Manzo ya wuce gaba na bi shi. Na same shi a zaune, halifunsa sun kewaye shi. Bayan mun gaisa. ya ce, “Ya Abdulkadir, dalilin da ya sa na kira ka, ina so ne ka rubuta wa Gordon takarda, ka ce masa gwamma ya nemi sulhu. Im ba haka ba fa, da shi da mutanensa duka za su halaka. Ka fada masa ni ne Mahadil Muntazir, im bai bi ni ba, kome ya same shi ya kuka da kansa. Gaya masa na tabbata zan yi nasara a kansa."
Ni dai ban ce kala ba, sai da Halifa Husaini ya ce amsa mana. Na ce, "Ya Mahadi, ga nawa jawabi zam fada in ka yarda. Ni dai na bi, kuma duk irin abin da ka ce shi zan rubuta, ba zan kara ba, ba zan rage ba, Amma in na fada wa Gordon cewa kai ne Mahadin gaskiya, ba zai yarda da ni ba. Da ya ke ba ka son zubad da jini, zan shawarci Gordon ya zo ya nemi sulhu. Zan ce lalle Karfinsa bai kai naka ba ko ko ko kadan, nasara a hannunka ta ke, wanda ko ya ja da kai zai fadi. Ni na yarda in zama wasidi a tsakaninku.” Mahadi ya ce ya yarda da shawarata, in tafi in rubuto takardar. Na komo gida na kunna fitila, na dauki alkalami da takarda na rubuta. Amma maimakon im fada wa Gordon sakon Mahadi, sai na shiga fada masa halin da na ke ciki. Na ce ina rokon Allah ya ba shi nasara, ya sake maishe ni hannunsa. Na ce na sami labari a wurin Greek din nan George Calamatino, cewa ya yi hushi da na yi sulhu da Mahadi. Na ce ya tuna tilas babu abin da ba ta kawowa. Na tuna masa irin jidalin da na sha da su Sultan Haruna, da kuma bi da kabilu iri iri ’yam bore. Amma tun da sojana ba su da karfin fada a zuciyarsu, yaya zan yi ? Hafsoshi Turkawa da Misirawa da ke karkashina sai kulle-kulle su ke mini. Kullum sai watsa labaran karya su ke yi don tsorata sojana. Ni kadai ne fa Bature, ga ni kuma Kirista. Sun kare ma sun ce abin da ya sa yaki ke ta ba mu kashi haka, wai don ni Kirista ne. Ganin haka na ce musu na musulunta, ko da ya ke har cikin zuciyata ban rabu da addinina ba. Na shiga salla da azumi. Ba don kome na yi duk wannan abu ba, sai don in saka musu karfii a zuciya don mu sami nasara. Amma tun da ya ke Allah ya kawo mu kusa, da ni da shi haka, fatana Allah ya sake tara mu, in ci gaba da biyayya gare shi. Na roke shi kuma ya yi kokari ya kubutad da ni daga hannun mutanen nan, don a kullum ba na tabbata cewa raina nawa ne.
Duk takardan nan a cikin harshen jamusanci na yi ta, ama na rika jefa faransanci. Da na gama na dauka sai wurin Mahadi. Gabana ya ta faduwa, don ban san irin hannun da takardar za ta shiga ba. Ya yiwu su sami wani wanda ya ji jamus su ba shi ya karanta. In kuwa haka ya faru, wus, ai ni kuma tawa ta kare a wannan duniyar ke nan! Inda Allah ya kyauta, sai Mahadi da bakinsa ya ce in aiki daya daga cikin yarana ya tafi Kahartum ya ba Gordon. Na tura Morgan Fur, wani saurayi Bature, na ce ya je ya kai. Aka ba shi jaki ya hau. Na ce masa in ya shiga Kahartum, kada ya yi magana da wani mahaluki sai Gordon kurum.
Wajen sha biyun rana, wadansu barade suka zo daga kasar Berber suka kawo labarin wani jirgin wuta na ruwa da Mahadawa suka nutsar a Kogin Nil, suka kashe kulliyar mutanen da ke ciki, har da Kanar Stewart. Suka kwaso takardunsa suka kawo wa Mahadi. Ina zaune sai na ji kira. Da na tafi wurin Halifa, sai ya ce mini in tafi ofishin magatakardansu akwai wadansu takardu suna nan an rubuta da harshen Turawa in karanta. A ciki na sami takardu da dama, amma galibi duk ba na aiki ba ne. Muhimmiya a cikinsu guda ce kurum, wadda ta tabo maganar yaki. Rubutun Gordon ne, ko da ya ke bai sa hannu ba. Ita wannan takarda ban fada wa Mahadi abin da ta ce ba, ashe ita za ta jefa ni cikin sarka. Mahadi ya shawarci Halifansa, ya ce ya kamata a aika wa Gordon da takardun nan. Za su tabbatar masa an nutsad da jirgin Kanar Stewart, kila wannan ya sa ya nemi sulhu.
Kashegari da maraice, sai ga yarona Morgan ya komo, amma Gordon bai ba da amsar takardata ba. Rashin ba da amsa ya tunzura Mahadi, ni kuma ya ruda ni. Na yi ta tunanin me ya ba Gordon haushi da ni har ya juya mini baya haka. Na gaya masa gaskiya ba bisa son raina na bi Mahadi ba, ba bisa son raina na zama Musulmin karya ba. Duk abubuwan nan tilas ne ya kawo su, amma ko sannu bai ce mini ba. Na wuce gaba Morgan na biye sai wurin Mahadi, na fada masa Gordon dai bai ba da amsa ba.
Zuwa can dare, Mahadi ya sake kirana, ya ce in rubuta wata takardar im fadi labarin nutsewar jirgin Kanar Stewart. Ya ce ya tabbata in Gordon ya ji haka, ya san karyarsa ta kare ke nan, sabo da haka zai ba da amsa. Na koma tantina, na kunna fitila, na rubuta wasika. A ciki na fadi galibin abubuwan da na fada a takardar farko, watau ta shekaranjiya. Na ce ya taima ke ni in kubuta, babbar hanyar taimakon kuwa, ita ce ya fada wa Mahadi in zama jakada a tsakaninsu bisa shirya maganar sulhu. Na like da ambulon na ba Morgan. Gari na wayewa, sai ga shi ya komo da amsa. Ko da na duba, sai na ga ba rubutun Gordon ne kansa ba, Hansal ne ya rubuta, watau wakilin kasarmu ta Austria wanda ke zaune a Kahartum. Ya rubuta da jamusanci, da kuma larabci, ya ce :
“Masoyina Slatin Bey,
“Na sadu da takardunka, kuma ina so ka zo Tabia Ragheb, watau barikin sojan Omdurman. Ina so in yi ’yar magana da kai bisa yadda za mu tsira. Im mun kare kana iya komowa wurin abokinka, Mahadi, babu mai taba ka.
Amintaccenka,
Hansal .”
Lafazin wannan takarda ya ruda ni kwarai, tumbana kalman nan ‘abokinka.’ Na yi ta juyayi a zuciyata ko da gaske su ke yi da suka kira ni abokin Mahadi, ko kuwa dabara ce suka yi yadda Mahadi zai saki jiki da ni, har in sami tserewa ?
Na dauki takardar sai wurin Mahadi, na bayyana masa abin da ke ciki. Da na kare karantawa, sai ya tambaye ni ko ina so in tafi Omdurman wurin Hansal. Na ce masa ni ba ni da wani zabi, sai abin da ya zabam mini. Ya ce, “Amma ina tsoro in ka tafi Omdurman Gordon zai kama ka, kila ma ya kashe ka. Me ya sa bai rubuto maka ba shi da kansa, in dai ba kinka ya ke ba ?”
Na ce, “Ban san dalilin haka ba ni kaina. Kila ko gwamnatin Masar ce ta hana ya yi mana wasika. Amma in na ga wakilinsa Hansal ina iya shirya kome na maganar sulhu in suna so. Maganar cewa Gordon ya kama ni, to, ai ko ya kama ni kana da ikon kwato ni." Mahadi ya ce, “To, sai ka shirya, zan aiko maka ka tafi .”
Na koma tantina ina ta murna, hanyar kubuta ta zo. Shiru, shiru, shiru, ban ga manzon Mahadi ba. Har na fara karaya a zuciyata, can sai na ji dudduge an nufo inda na ke. Jim kadan yarona ya shigo, ya ce ga yaron Halifa yana son ganina. Na ce ya shigo. Da shigowarsa sai ya ce in mike im bi shi zuwa gidan Yakubu kanen Halifa. Na nada rawanina muka tafi. Muna isa tantin Yakubu, sai aka ce ai Halifa yana tantin Abu Anga. Da jin haka na san ana can ana mini kulle-kulle ke nan, wannan kira ba na alheri ba ne. Ko da muka isa sai na ga Yakubu, da Abu Anga, da Fadlel Maula, da Zeki Tummal, da Haji Zubairu suna zaune, sun sa fitila a tsakiyarsu. Kewaye da su ga askarawa rike da bindigoginsu. Amma duk wurin babu Halifa wanda aka ce shi ke kirana. Manzon da ya yi kirana ya tafi ya fada wa Yakubu, aka ce in shiga.
Abu Anga ya dube ni ya ce, “Abdulkadir, ka ci amana. Ka yi alkawarin za ka yi biyayya ga Mahadi, to, wajibi ne gare ka ka cika alkawarin nan. Wajibi ne gare ka ka bi umurni, ka aikata abin da aka ce maka ko ba dadi. Haka ne, ko ba haka ba ?"
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Post a Comment (0)