ƘALUBALAN KU IYAYE MATA

*🇸🇦ZAMAN AMANA WIRTER'S*🤜🤛



KE GABATAR MUKU

                DA

*K'ALUBALEN KU IYAYE MATA*




_Abinda yawancin iyayen mu suke yi a yanxu shine basa kaunar suga an tab'a yaran su._




_Yaro ya shigo miki cikin gida da kuka, abu d'aya kawai zaki tambaya shine "wa ya dake ka?" yana baki amsa sai ki zari mayafi ki fice._



_yaron yana ganin haka sai ya biyoki, ko be biyo bayanki ba to daga ganin irin fitar da kikai yasan fad'a zakije yi a kan shi._



_daga lokacin ran yaranki zai yi fari ya zamana ko yaushe in an dokesu sai sun fada miki, ke kuma babu ruwanki da binciken meya faru waye me gaskiya da mara gaskiya, kawai zaki fita ti-ti kiyta yage murya kin zama 'yar daba a unguwa, kina mace amma kece fad'a da maza, kece yi da mata, har tsofaffi ma baki k'yale ba in dai kan yaranki ne._




*to saurara kiji illar da kike jawowa yaranki a kan yin hakan*



1- _rana d'aya idan kika fita yin fad'a domin an taba yaranki to yin hakan kamar kin bawa yaronki dama ne akan ya kara kangarewa kuma karya ragawa Kiowa, duk da ke baki fadi hakanba, amma goyawa yaron bayà da kkai zaisa yaçe bari in cigàba inada mai taremn a gida._



2- _zai jawo miki tsanar 'yan unguwa, dake dà shi kuma zai jawo yaro ya zama fitinanne mara son zaman lafiya._




3- _zai zàma munafuki me yawan had'a husuma._



_ba'a ce laifi bane dan kin nemawa yaranki hakki, babban laifin shine goya musu baya kan abinda yake laifin su ne yin hakañ lalàta rayuwar yaranki kike yi baki sañi ba._



_idan yaro ya shigo gida da kuka watakila ma harda rauñi to tsaya kiy biñçike tukun, in yaronki keda gaskiya to zaki iya bi mishi hakkin shi, domin Allah baya zalunci kuma ya haràmta yinsà, amma idañ zakiy hukunciñ kar kije da yaron kuma karki bari ma yasani, idan ya sani wannàn karon shi aka zalunta, na gaba shi zaiyi zaluñciñ tunda yaga an yi magana a wancan na baya, kuma ba akan komai uwa take zak'ewa ba kan magànàr yaro gaskiyà sai abun yai kamari._



_idan shine mara gaskiya sai ki hukuñta shi._



_yaran nan nà zamàni baki goya musu bayà ba ma ya aka kare, balle kin goyi bayàñ su._



_mu sani cewa goyon bayan yaro kan rashin gaskiya tamkar kin yànkar mishi tikiti ne, kuma kika damk'a a hanun shi, kikace yaje ya nemo rigima._



*ALLAH YA BAMU IKON GYARA TA HANYAR KARAÑTÀRWAR MANZON MU ANNÀBI MUHAMMAD (S.A.W)*







*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*🤜🤛


Post a Comment (0)