AMARYA KO UWARGIDA

http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/06/me-zaki-yi-dan-mijinki-ya-kara-sonki.html


⊂___ AMARYA Ko UWARGIDA ___⊃

babu shakka idan kina son soyayyar da mijinki yake yi maki ta Kara hauhawa, ki zama kece madubin dubawarshi a koda yaushe, ki zama kece abun tunaninsa a koda yaushe, yaji yana kara zakuwa da sonki ba dare ba Rana:

to ki kasance kina jin tausayinsa a fili da kuma boye, duk abunda ya kawo gida ya mika maki ki karba kina mai godiya da nuna tausayinsa,
misali :ki karba cikin ladabi da biyayya kina cewa ( baban wance) hada dawainiya haka, in kudi ne kina mai cewa ai da ka Bari ka Kara a cefane, da sauran ire-ire kalamai masu nuna kauna da tausayawa , domin kuwa ko dabba tana zuwa kusa da Wanda ke tausaya Mata ne, ballantana mutum dan Adam, ( uwa uba kuma ace miji) kuma ki rinka nuna masa bajintarsa a fili da nuna masa cewa shine jigon rayuwarki ,masu magana suna cewa tausayi sinadarin soyayyar miji ga matarsa.

◉••••MIJINA____JARINA••••◉
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596


Post a Comment (0)