Eznah 22

*_EZNAH_*🌹
       _wattpad@mamuhgee_

*22*
Wat""""yace cikeda mamaki...

Babban cikin wa'inda aka Aiko Wanda shima tuni hassadar saheeb da baqin cikin cigaban daya fisa samu har zamowarsa babban kanal major yasa yakejin tsananin tsanarsa ya matso cikin wani shu'umin murmushi dabawanda zai gane yace,

Sorry sir but we have the strict order to arrest you.....

Wani kallo ya watsa Masa da big white oily eyes nasa Nan take ya diririce yace,

Sorry sir.

Baikoba cikiba ya fito yabiyosu kusan soldiers talatin Nan take yasan koma menene to babba ne.

Abba da Kamal taredasu mum asee ne suka fito hankulansu amatuqar tashe musamman ma mum asee da tuni ta qanqamesa tareda fashewa da kuka tana cewa,

Nashiga uku ni aseeya mezan gani?
Saheeb fadamin menene?
Meyake faruwa?
Please son talk to me....

Abba ma bayanin yakejiran yayi musu Amma Sam ko magana yakasayi saima idanuwansa dasuka ka'da jajir zuciyarsa na wani irin ra'dadi...

Kamal kuwa yakura ya kashewa Ido daya suka saki murmushi.

Tunda tayi sallar asuba tana zaune Kan sallayar Bata tashiba hakanan takejin tsananin fa'duwar gaba da damuwa..

Hayaniya tafara juyowa sama sama ta miqe tsaye tareda wuce gwaggo dake kwance tana Jan minsharin bacci bayan tayi sallar asuba.

Cak ta tsaya zuciyarta na bugawa da sauri nantake taji kamar jiri zai zubar da ita tayi saurin yin zaman Yan bori a qasa Dan kuwa abinda idanuwanta suka gani yanxu ya tabbatarda aikinsu mum asee yaci...

Hawaye ne suka tsinke Mata lokacinda taqura Masa Ido ko baifadaba ta hango tsananin damuwa da tashin hankali tareda bacin ran dayake ciki....

Sake 6allewa hawayenta sukayi Yana 'dagowa zai wuce idanuwansu suka hadu ta qura Masa Ido cikin hawaye shima bai dauke nasa kanba Saida wayarsa dake aljihu tayi qara ya juya ya nufi motocinsu dake waje Dan kuwa ko nasa anhana yashiga Sai Wadda akazo arresting nasa dasu.

Kasa motsi tayi agurin har aka wuce dashi ta juya cikin wani irin nauyin zuciya takoma 'daki ta zube bakin gado tareda sakin kuka Mai cin zuciya ahankali.....
Abinda takeji azuciyarta yafi qarfin tausayi,
Jitakeyi zuciyarta na Mata zafin dabazata iya jure ganin saheeb ahaka,

Sabon kuka tasaki Dan kuwa zuciyarta batayi Mata adalcin kamuwa da wannan muguwar soyayyarba dabatada qarshe me kyau,,
Meyasa zuciyarta koyaushe Bata iya za6en masoyaba,,,,

Duk yanda taso daina kukan ta Nemo mafita kasawa tayi 
Hawayenta sun kasa tsayawa ta miqe cikin Dan sauri sbd zayyan daya fa'do Mata arai tasan shika'dai zata iya fadawa gaskia...to Amma yakamata na yarda dashi shima kuwa tunda Naga duk nakusada saheeb din ne ke farautar dukiyarsa da rayuwarsa.....

Kallonta gwaggo lokacinda ta tashi taga fuskarta tayi mummunan kumbura tai jajir.....

Jitayi jikinta yayi sanyi Dan ita alamarin Anano yafara Bata tsoro ta miqe tsaye tashiga toilet ta wanko fuskarta da bakinta tadawo ta zauna kusada ananon tareda kallonta cikin tsananin kulawa tace,

Anano indai da gaske kike bakyason Nan din banga amfanin zamanmuba saimu koma gidan tunda can kikeso Amma wannan alamarin yafara bani tsoro gabaki 'daya kin hargitse bakya cikin nutsuwa da walwala duk kwanakinan.......

Sabbin hawaye ne suka gangaro Mata Bata damu data gogeba tace,
Gwaggo zuciyata na zafi,,jinake kamar zuciyata zatabar qirjina ra'dadin datake ciki...

Kallon tausayawa gwaggo tayi Mata sbd 'daukar ciwon zuciya take da gaske tashafo kanta tace,

Allah ya yaye Miki yakawo Miki sauqi Anano.

Amin tace daqyar tana sunkuyar da kanta sbd zuwan wasu sabbin hawayen Sai kawai ta miqe tabar dakin Dan kukan nata ba tsayawa zaiyiba gwara taje tayisa ko ra'dadin zuciyarta ya ragu.

Tana fitowa nufi hanyar gefen part'din saheeb inda gym dinsa yake cikin wani mugun yanayi taji fixgota tareda 'daga hannu zai sharara Mata Mari 
Ta rintse ido batareda ta motsaba Dan kuwa tasan zai zargi hakan kodan ganin daya Mata jiyan a palon saheeb din.

Sauke hannunsa yayi tareda yarfewa cikin tsananin fushi da 6acin Rai idanuwansa har wani ruwa suke tarowa sbd 6acin Rai ya kalleta da jajayen idanuwansa yace,

Koki fadamin ubanda kikewa aiki Kona daureki nakaiki headquarter inda zakifi Jin da'din magana..

Cikin tsinkewar zuciya ta kallesa hawaye nabin fuskarta ta bu'de baki cikin sanyin murya tace,

Bani nayiba.....'dauketa da lafiyayyan Mari yayi sbd yakasa tankwarar zuciyarsa Kuma tabbas Babu abin zargi akan wannan abin Sai ita Dan kuwa saheeb nacan tuni aka rufesa a 'dakin qanqara duk bayan 30min Sai anmasa shock sbd kawai yayi admitting laifinsa shi munafikin sojane Yana tareda 6arayi....

'dagowa tayi ta kallesa da idanuwanta dasuka ka'da sukai jajir ga gefen bakinta daya fashe sbd Marin tace,

Ka dakeni,kasa a 'daureni,kayimin azaba Zan cigaba da maimaita maka bani nayiba sbd banyiba...
Kuka tasaki tana cigaba da cewa,

Kana tunanin Dana iya computer dazan bar hakan tafarune?

Wani kallo ya watso Mata sbd dai maganarta tasake tabbar Masa da koba ita tayiba tasan ya akayi hakan ta faru.
Baisan meyasa zuciyarsa keson tayarda da itaba duk da kuwa ita din ba abin yardabace.

Cikin qunar Rai da fushi yace,

Ok then idan bake kikayiba then prove yourself..

Rintse idanuwanta tayi hawayenta nacigaba da zubowa tace,

Wallahi bani bace....

Cikin wata gigitacciyar tsawa yace,

Then who is it bitch.... talk coz am loosing my patience hia..

Girgixa Masa Kai tayi ahankali tana sake zubo da hawaye..

Cikin zafin Rai da takaici yakallleta ganin taurin kanta yace,

Ok then zanmiki yanda zakifi ganewa....

Palon saheeb ya nufa tareda zuwa har bedroom ya dauko laptop dinsa tareda wayarsa daya yafito ya fizgi hijabinta yafara janta tana tana kuka yakaita motarsa ya jefa but yarufe yajata Bai tsaya ko'ina ba Sai barrack.

Budeta yayi yakuma jawota Nan take akayi ciki da ita zuwa lokacin tuni hawayenta suka qafe jikinta ba inda baya rawa hankalinta yayi mummunan tashi...

Office din general major ya nufa cikin girmamawa ya Sara Masa.

Cikin kulawa general major Muhammad tukur Garba ya zare medical glass dinsa yakalli zayyan yace,

Zayyan hope kasamo evidence din dakace coz we're running out of time within 24 hours idan Babu wani prove nabashine yayiba he will be sentence to dead...

Sir I have the prove sbd yarinyar gidansuce ta 'dauki laptop din taje tana wani Abu da ita so she mistakenly send it...

Wat...? do you expect me to go the headquarter nabasu wannan bayanin...

Where is the girl?

She's here with me sir..

Let's go and see her...yafada tareda miqewa..

Zaune take a wani dakin horo an 'daureta Kan kujera tareda kunna wani mugun kwai daya masifar kashe Mata idanuwa jitake kamar idanuwanta zasu zazzage Banda ko hawaye basa iya fitowa sbd dasun nufato fitowa saisu bushe sbd azabar Kwan da haskensa.

Qare Mata kallo general major muh'd yayi cikin mamaki yace,

Zayyan are you sure of wat you're saying..?

Yes sir yace,.

Kashe qwan akayi ta rintse idanuwa da qarfi Dan kuwa ta daina ganin komai tasaki wani razanannen ihu tana Dan kuwa ta tabbatarda tadaina gani Koda zata gani kuwa ba Yan kwanakin nanba.

Cikin wata irin muryar ban tsoro general major ya daka Mata tsawa tareda sake maimata Mata abinda zayyan yafada..

Tsit tayi cikin wani sabon tashin hankalin Dan kuwa Sai yanxu tagane dalilin kawota Nan kenan ita zasu maqalawa laifin..

Ganin yanayinta yasa zayyan matsowa da niyar walwaleta qasa qasa gurin kunnenta yace,

Is better kice keki daukar Masa laptop by mistake Kika tura internet coz kina qaryatawa saheeb zai iya rasa rayuwarsa nidake Kuma zamu iya qare shekarunmu a prison sbd already munriga munshiga cikin zancen so better be careful.

# vote
# comment
# share

Post a Comment (0)