FALALAR ZUWA DUDA MARAR LAFIYA
*1-Zuwa duba marar lafiya koyi da raya sunnar Manzon Allah ﷺ*
Daga Usman dan Affan ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ yana fada a Hudubarsa cewa:
*"Hakika mun munyi rayuwa tare da Manzon Allah ﷺ alokacin zaman gidan da lokacin tafiya bulaguro,Manzon Allah ﷺ ya kasance yana zuwa duba marar lafiya daga cikinmu,kuma yana raka Jana'iza kuma yana yin Yaqi tare da mu......."*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ.
*2-Mai zuwa duba marar lafiya,yana samun adduar Mala'iku*.
Daga Aliyu Bn Abi Dalib ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ yana cewa:Naji Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Babu wani musulmi da zaije duba marar lafiya musulmi da safiya,face Mala'iku guda dubu 70,suna yi masa salati har zuwa yammaci,idan kuma da yammane Mala'iku guda dubu 70 suna yi masa salati har zuwa wayewar gari....)*
@ﺃﺧﺮﺝ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.
*(Wanda yaje duba marar lafiya,wani mai kira yayi kira,yace;kaji dadi ka dace kuma an yi maka masauki a aljanna)*
@ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
*(Babu wani mutum da zai je duba marar lafiya,yana tafiyane acikin rahamar Allah, idan ya zauna,rahama zata lubbubesa)*sai yace ya Manzon Allah wannan duk falalace ta mai duba marar lafiya,to shifa wanda baya da lafiyar ba?? Sai yace:
*(Allah yana kankare masa laifukansa saboda rashin lafiyar)*
@ﻓﻔﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ﻋﻦ ﻫﺎﺭﻭﻥ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ.
*(Wanda yaje duba marar lafiya,bazai gushe ba yana tafiya acikin rahamar Allah har sai ya zauna,idan ya zauna sai Rahamar ta lullubesa)*
@ﻭﻓﻲ ﺭﻭﺍﻳﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ﺃﻳﻀﺎً
*3-Duba marar lafiya Hanyace ta shiga aljanna*
Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
*(Wanda ya tafi zuwa duba marar lafiya,bazai gushe ba acikin inuwar aljanna.....)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ﻋﻦ ﺛﻮﺑﺎﻥ ﻣﻮﻟﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ،
*(Wanene ya wayi gari yana mai azumi??)*sai Sayyadina Abubukar yace:"Gani" sai yace:
*(Wayaje duba marar lafiya yau??)*sai yace "Gani"sai yace*(wa yake rakiyar gawa a yau??)* Abubakar R.A yasake cewa"Gani" sai yace;
*(Wa yaciyar da mai karamin karfi a yau??)*sai Abubukar Ya sake cewa"Gani" sai Manzon Allah ﷺ yace:
*(Babu mutumin da zai hada wadanda a yini guda face ya shiga aljanna....)*
@ﻣﺴﻠﻢ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ.
*(Abubuwa guda biyar duk wanda ya aikata daya daga cikin yana cikin kariyar Allah Madaukakin sarki,na farko shine zuwa duba marar lafiya.......)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻋﻦ ﻣﻌﺎﺫ ﺑﻦ ﺟﺒﻞ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ.
Allah ne mafi sani