KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE: A RUBUCE

KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE: A RUBUCE


 
🔴10/RABI'U-TSANI/1439-HJRY
🔴29/DECEMBER/2017-MLDY
🎤 MAI GABATARWA= Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu.
TOPIC= [[MIYAGUN KWAYOYI SUNA HALLAKARWA]]
🗝🗝MABUDI🗝🗝
SARKIN KANO- SUNUSI NA II tareda MANYAN AREWA DA MASANA SUN NUNA TAKAICINSU AKAN KARA YAWAITAR SHAYE SHAYE GA MAZA DA MATA ANAN AREWACIN 9JRY musammanma KANO da JIGAWA inda a kullum ake shanye kwali 3000,000❗
🗝KAGUJI SHA KO SAIDA KAYAN MAYE DON KAUCEWA TSINUWAR ALLAH SW DA TSINUWAR ANNABI SAW❗
-MALAM YA KASA WANNAN KUDUBAR ZUWA GIDA➖ 🔟
1⃣➖MUQADDIMA✔
Yaku bayin ALLAH! Muji tsoron ALLAH murigayi ajalinmu da kyawawan ayyuka, musayarda gida mai karewa musayi gida mai wanzuwa dashi domin samun dawwamammen ni'ima, WALLAHI duniya ba gidar dawwama bace❗
2⃣➖MUHIMMANCIN HANKALI✔
HANKALI yana daga mafi girman kyautarda ALLAH SW yayiwa mutum,
💡ALLAH SW yace <<lalle hakika mun karrama 'yan adam>>
⭕IBN-ABBAS yace- karkashin wannan ayar= mun karramasune da hankali,
ALLAH yabawa Dan ADAM hankaline don banbance mai anfani da mai cutarwa da kuma fahimtar shari'ar ALLAH da hakkokin ALLAH da NANZONSA,
HANKALI zinarine da ba'a kimantashi da dukiya, duniya batada amfani ga wanda yarasa hankali koda yana cikinta, domin da HANKALIN Dan ADAM ALLAH yake magana, ALJANNA da kanta batada anfani ga mai HANKALI, atakaice HANKALI shine mafi girman kyautar ALLAH ga bayinsa,
3⃣➖MAQASUDIN BAYANI AKAN MUHIMMANCIN HANKALI✔
Ana samun wasu kaso na matasanda idonsu ya makance suka mayarda kansu tamkar dabbobi koma fiyeda haka- sukayi anfani da hannunsu wajen rugurguza HANKALI da kimarda ALLAH yabasu da jawowa kansu kaskanci wajen shaye shayen kayan maye da giya da muggan kwayoyi don gusarda HANKULANSU,
4⃣➖HUKUNCIN KAYAN MAYE A QUR'ANI✔
💡ALLAH SW yace <<ya wadanda sukayi imani lalle kayan maye da caca..................... kazantane daga aikin shedan ku nisanceshi domin ku rabauta * lalle shedan yanason jefa gabane atsakaninku cikin giya da caca kuma yakangeku daga ambaton ALLAH da kuma salla, shin zaku hanu❓>>
5⃣➖HUKUNCIN KAYAN MAYE A HADISI✔
💡Ya ku matasa! Masoyinku ANNABI SAW yace "duk abin maye giyane kuma dukkan giya haramunne" {AHMD & ABU-DWD}
💡ANNABI SAW yace "ALLAH ya tsinewa kayan maye❗da mai shanta❗da mai shayarda ita❗da mai sayarda ita❗da mai saya❗da mai sana'antata❗da abinda aka sana'anta da ita❗da mai dakonta <a mota ko mashin ko aka>❗da wanda aka kaiwa❗{ABU DWD}
6⃣➖DAGA ILLOLIN KAYAN MAYE DA KUMA MUGGAN KWAYOYI✔
🔺MALAMAI DA LIKITOCI SUN IRGA ILLOLIN KAYAN MAYE KAMAR HAKA➖
➖lala ta addini➖lalata HANKALI➖lalata halayya➖lalata gangar jiki wajen tafiyarda karfinta da gaggauta zagwanyewarta da tsufarta➖lalata zurriyya➖kazantar shedance➖najasace➖gadarda kaskanci da wulakanci➖cutarda al'umma➖cutarda tattalin arziki➖kawo tsaikon gudanar jini cikin huhu➖sabautarda mutuwar bazata➖lalata fararen kwayoyin halitta da ALLAH yasasu cikin jini don tsarin lafiyar jikin mutum➖rasa gani kwatsam➖yanke sha'awa da dakileta da yanke haihuwa➖yawaita hatsarurruka da tada boma bomai‼
7⃣➖MUGGAN KWAYOYI DA KAYAN MAYE TSINANNUNE✔
Mun gabatar a gaba na 5⃣ tsinuwar ALLAH ga kayan maye da masu alaka da ita guda 8,
🔺IBN-TAIMIYYAH cikin fatawarsa yace= wiwi tsinanniyace ita kanta da kuma masu amfani da ita da masu halattata kuma fushin ALLAH ya wajaba a kansu da na bayinsa mumini................ . Ya maida mutane dayawa mahaukata‼
8⃣➖UQUBAR MAI ABUTA DA MASHAYA✔
🔺an zowa UMAR IBN ABDUL-AZIZ da wasu mutane sun sha giya, sai yace a bulalesu❗acikinsu akwai wanda baya shan giya hasalima yanada azumi, sai UMAR yace a fara dashi, sai yakaranto fadin ALLAH SW cewa <<idan kunji ana karan tsaye da izgili wa ayoyin ALLAH kada kuzauna a wurin......... in kun zauna awurin to kun zama irinsu>>
9⃣➖DAGA UQUBAR MASHAYI A LAHIRA✔
💡ANNABI SAW yace "wanda yasha kayan maye ALLAH yayi alkawarin shayar dashi kwatar masifa❗wato gumi da mugunyar 'yan wuta❗{MSLM}
💡ANNABI SAW yace" wanda yamutu yana shan kayan maye ALLAH zai shayar da daga tekun GUTDA, wato wani ruwane mai doyi mai tsananin wari da yake fitowa daga farjin Karuwai da mazinata" {AHMD}
🔟➖YADDA SAHABBAI KE KYAMAR KAYAN MAYE✔
⭕ALIYU IBN ABI-TDALIB R/A yace➖ da digon kayan maye zai diva acikin rijiya sai aka gina hasumiya akanta bazan Kira salla akantaba❗da digon kayan maye zai diga akogi yabushe ciyawa yatsira awurin bazan kiwaci dabbata awurinba❗
⭕IBN UMAR R/A yace➖da yatsata zai taba kayan maye bazanso tabiniba‼
{MAWARIDUZ ZAM'AN LIDURIS ZAMAN}
♦Kana sabawa ALLAH afili yana ganinka♦
♦ka manta tabbas gobe zaka hadu dashi♦
Ina Kira ga matasanda sukayi nasara kammala samun horon aikin soji suka da abubuwa kamar haka➖
➖suguji shaye shaye
➖suguji neman mata
➖suyi rikoda musulunci
➖sukiyaye mutuncin 9jr
➖surika tuna iyaye a albashinsu🔴
👏🏽👏🏽👏🏽ALLAH YASA MUWANYE LAFIYA👏🏽👏🏽👏🏽
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN.
*>>>Majlisin Sunnah.*
www.facebook.com/majlisinsunnah
Post a Comment (0)