KHUDUBAR MASJID UMMINA HAUWA'U UNGUWAR DOMA GOMBE STATE

KHUDUBAR MASJID UMMINA HAUWA'U UNGUWAR DOMA GOMBE STATE:


 
⚫16/RABI'U TSANI/1439-HJRY
⚫05/JANUARY/2018-MLDY
🎤MAI GABATARWA= Abubakar BN Mustafa Biu
TOPIC= [[DARUSSA GUDA 9⃣ DAGA ABI-HANEEFA]]
1⃣➖GIRMAMAWARSA GA QUR'ANI MAI GIRMA❗
🔵IMAM ABU-HANEEFA yanada yaronsa takwaran Malaminsa (HAMAMAD)
Lokacinda HAMMAD yasauke SURATUL FATIHA sai ABU-HANEEFA yashirya gagarumin walima kuma yabawa MALAMIN yaronnasa dirhami 500 ko 1000- wato a naira daidai yakeda kusan N3000,000 ko N6000,000— sai MALAMIN yace- fatihane kadai na karantar dashifa kudin yayi yawa❗
Sai ABU-HANEEFA yace➖da munada abinda yafi hakama da mun baka‼
{250- MIN HAYATIL A'IMMATIL AR BA'A}
2⃣➖HIMMARSA GA TATTAUNAWAR ILIMI❗
🔵ABU-HANEEFA ya fita daga masallaci🕌 bayan an idarda sallar isha'i yana rike da takalmansa👞👞 a hannu kafin yasaka, Sai IMAM ZUFAR yazo da wata mas'ala ta ilimi suna tsaye suna tattaunawa akanta har aka kira sallar ASUBA,
Sai suka koma cikin masallacin sukayi salla kuma suka cigaba da tattaunawar karshe dai suka tsaya akan maganar ABU-HANEEFA❗
{ABU-HANEEFA ABDUL HALIM AL-JUNDY}
3⃣➖KARFIN BASIRARSA WURIN SAURIN GANO MAFITA‼
🔵LAITH IBN SA'AD yace➖naji wani Mutum yacewa IMAM ABU-HANEEFA— yaronane sai in kashe makudan kudi in masa aure bazai dade da matarba sai yasaketa haka nake ta asarar kudina, menene mafita❓
Batareda bata lokaciba sai IMAM ABU-HANEEFA yace➖kashiga dashi kasuwan bayi yazabi baiwarda yafiso sai kasayeta ka aura mishi ita, kaga in yasaketa tana nan a baiwarka dukiyarka bai salwantaba kuma bai isa ya 'yantataba tunda ba baiwarsa bace❗
➖LAITH yace- WALLAHI abinda yabani mamaki shine saurin amsarda yabayar batareda bata lokaciba❗
{MIN AKHLAQIL ULAMA'I-LISH SHEIKH MUHD SULAIMAN}
4⃣➖BIYAYYARSA GA IYAYENSA DA KUMA MALAMINSA‼
🔵IMAM ABU-HANEEFA akoda yaushe yana yawan adu'a da ISTIGFARI ga iyayensa 2 da kuma ga malaminsa, kuma akowace wata yakanyi sadaka da dinari 20 wato N 1,183,000 da niyyar ladan yasami iyayensa 2❗
5⃣➖DABARARSA A ILMANCE‼
Wani Mutum yazo WAJENSA da dare sai yace masa— kaceto mini aurena kafin ASUBA, matatace taki mini magana a darennan sai nace mata in bata mini maganaba har ASUBA yayi na saketa saki 3, nabi dukkan hanya don tayi magana amma taki kuma lokaci yana wucewa,
🔵sai IMAM ABU-HANEEFA yace masa➖kaje wajen ladani kace masa yayi kiran salla kafin asuba kai kuma kafinnan kaje kacigaba da rarrashinta,
Mutumin ya aikata haka- taki magana- tana jin kiran salla- sai tace ALHMDLH na kubuta daga aurenka- sai yace ALHMDLH aurena yana nan don ASUBA bata yiba❗
{ABU-HANEEFA ABDUL-HALEEM ALJUNDY}
6⃣➖TSANTSININSA A ABINCINSA‼
🔵An sace tinkiya agarin KUFA, sai ABU-HANEEFA yatambayi makiyaya— nawane mafi yawan shekarunda tumaki sukeyi❓
Sai akace masa shekaru 7,
Sai yakauracewa cin naman awaki da tumaki har na tsawo shekaru 7 don kada yaciyarda karo dashi❗wannanfa baiyi laifiba Koda yaciyarda domin a rashin sanine❗
{AL-KHAIRATUL HISAN}
7⃣➖TSANTSININSA A KASUWANCINSA‼
🔵AL-HASAN IBN ZIYAD yace➖IMAM ABU-HANEEFA ya aikawa abokin harkarsa dilolin kayan sayarwa sai yasanar dashi cewa acikinsu akwai riga guda daya mai aibi don haka awareshi gefe idan mai saye yazo anuna mishi aibin kuma arage mishi kudin,
Atakaice dai an sayarda kayan an manta ba'a wareshin kuma an jahilci wanda aka sayarwa,
Sai ABU-HANEEFA yayi sadaka da dukkan kudin dilolin❗kudin sun kai dirhami 30,000/ wato samada N 100,000,000‼
8⃣➖TSANTSININSA A RANTSUWA‼
🔵MUTSANNA IBN RAJA'I yace➖ ABU-HANEEFA ya azawa kansa duk lokacinda yayi rantsuwa da ALLAH akan gaskiya- sai yayi sadaka da dinari guda- wato a naira kwatankwacin N60,000‼
Kuma duk lokacinda yasaya kayan abinci na ciyarda iyalansa ko tufafi said yayi sadaka da makamancinsa‼
9⃣➖SUFYAN AL-THAURY YA ILMANTU DAGA ABU-HANEEFA‼
Wani Mutum yazo wurin ABU-HANEEFA yace masa- matata taki mini magana— sai nace mata WALLAHI in nasake miki magana kafin kimini magana to kin saku❗
Ita kuma tace— WALLAHI in na sake maka magana kafin kamini magana to sai na 'yanta baiwa❗
Yanzu haka mun daina yiwa junanmu magana domin ni banason aurenmu yamutu❗ ita kuma batason 'yanta baiwa❗meye abin yi⁉
🔵ABU-HANEEFA yace➖je kafara yi mata magana kuma itama tayima magana babu kaffara kuma babu 'yanta baiwa kuma aurenku na nan❗
Daman kafinnan mutumin yaje wajen SUFYAN AL-THAURY sai yace masa- aurenku ya mutu❗😭
Da SUFYAN yasami labarin hukuncin ABU-HANEEFA take yagarzayo wurinsa sai yace masa➖shin zaka halattawa mutum farji haramtacce ko⁉
Sai ABU-HANEEFA yace➖ai da yafara magana yagama- sai itama tayi nata maganar, maganar nata yariga ya warware rantsuwarsa, don haka shima yanzu in yayi mata magana ya warware mata 'yantawa❕
Sai SUFYAN yace➖MASHA'ALLAH kai kam kana binciko abinda muka gafala daga barinsa❗
{ABU-HANEEFA- ABDULHALIM ALJUNDY}
👏🏽👏🏽👏🏽RABBANA YAYI MUSU RAHAMA - MUMA YATABBATAR DAMU AKAN IMANI👏🏽👏🏽👏🏽
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN.
via= Abubakar BN Mustafa Biu✍
Post a Comment (0)