MANYAN LADUBBA AKAN MUSULMI GUDA GOMA A RANAR JUMA'A

*MANYAN LADUBBA AKAN MUSULMI GUDA GOMA (10) A RANAR JUMA'A*

Hakika Annabi s.a.w ya kebe ranar juma'a da wadansu Ladubba masu yawa,ga kadai daga cikinsu:

*1-Karanta suratul Sadaja da suratul Insan Acikin Sallar Assuba ta ranar Juma'a*.

Domin Annabi s.a.w ya kasance yana karantasu a Sallar assubar ranar Juma'a.
@Bukhari da Muslim.

*2-Yawaita Yin Salati ga Annabi s.a.w*


Annabi s.a.w yana cewa:
"Ranar juma itace mafificiyar rana daga cikin ranakunku acikinta ne aka halicci Annabi Adamu................. Kuma ka yawaita yimin Salati acikinta......"
@Ahmad Kuma Albany yace Hadisine HASAN

@Ana fara yawaitawa Annabi s.a.w Salatine na ranar juma'a tun daga daran juma'ar wato yau alhamis da dare kamar yadda wani Hadisin ya bayyana.

*3-Yin wanka ranar juma'a*

Saboda Fadar Annabi s.a.w:
"Idan ranar juma'a ta riski dayanku to yayi wanka".
@Bukhari da Muslim


*4-Sanya Turare Da Yin Aswaki*.

Annabi s.a.w yana cewa:
"Wankan ranar juma'a wajibine akan duk wanda ya balaga,da yin Aswaki da Sahafa abinda ya saukaka na Turard".
@Muslim


*5-Zuwa Masallacin Juma'a da wuri*.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
"Idan Ranar juma'a tazo Mala'iku suna tsayawa abakin kofar Masallaci suna rubuwa wanda yazo dawuri sannnan wanda ya biyo bayansa................ idan kuma liman ya hau kan minbari yafara khudiba sai su nade takardun su saurari khudibar liman".
@Bukhari da Muslim


*6-Karanta Suratul Kahfi*.

An samu daga aikin wadansu Sahabbai R.A sunayin Hakan.
@Saheehul Jami'i

*7-Yin Shiru da Sauraran Khudiba idan liman Yanayin Khudiba*.

saboda fadar Annabi s.a.w:
"Idan kacewa dan uwanka yayi shiru alokacin da liman yake huduba,to kayi lagawu".
@Bukhari da Muslim


*8-Kada ka riqa ketara mutune dan Kazauna asahun gaba,ka zauna idan sahu ya tsaya*

Daga Jabir Dan abdillahi yana cewa wani mutum yashiga Masallaci ranar juma'a alokacin Annabi s.a.w yana yin khuduba sai ya riqa qetara mutane, sai Annabi s.a.w yace dashi
"Zauna hakika ka cutar ka cutar".
@Ibn Majah ya ruwaitoshi kuma Albany ya Ingantasa.


*9-Yin Nafila raka'a guda biyi,idan kashiga Masallacin koda liman yana Hudubane*

Annabi s.a.w yana cewa:
"Idan dayanku yazo sallar juma'a sai ya tarar da Liman yana huduba,to kada ya zauna har sai yayi sallah raka'a biyu sannan ya zauna".
@Muslim


*10-Yawaita rokon Allah aranar Juma'a*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
"Ku yawaita rokon Allah aranar juma'a domin akwai wani lokaci acikinta wanda babu wani bawa da zai dace da wannan lokaci ya tsaya yana rokon Allah acikinsa face Allah ya bashi abinda yaroka".sai yayi nuni da hannunsa akan lokacin dan kadanne.
@Bukhari da Muslim

Amma malamai sunfi rinjayar da lokuta guda biyu:

-Daga Hawan Liman kan mimbari zuwa kare Sallah.

-Daga Bayn Sallar La'asar zuwa Faduwar rana.

Amma magana mafi inganci kuma mafi rinjaye awajan Malamai shine daga bayan Sallah La'asar zuwa faduwar Rana.
@Zadul-Ma'ad



    Allah ne mafi sani.

Post a Comment (0)