DUK WANDA YA ZABI SU PETER OBI A MATSAYIN MATAIMAKIN SHUGABAN KASA NA JAM'IYYAR PDP TO YACI AMANAR KANSA, YACI AMANR MUSULUNCI KUMA YACI AMANAR AREWA

DUK WANDA YA ZABI SU PETER OBI A MATSAYIN MATAIMAKIN SHUGABAN KASA NA JAM'IYYAR PDP TO YACI AMANAR KANSA, YACI AMANR MUSULUNCI KUMA YACI AMANAR AREWA

A daure ka karanta a tsanake.
Lokacin da Peter Obi yake matsayin gwamnan jihar Anambra farkon abinda ya farayi shine ya gabatar da kudurin kora a rubuce ga 'yan arewa mazaun jihar, ya bada iznin kora ga hausawa dilolin awaki na jihar, ya bada iznin korar hausawa a tashar mota na Arewa Park, Osogbo Park, Akure Park, Ilorin Park, dilolin albasa wato Arewa Onion dealers da kuma hausawa da yarbawa dilolin goro ya koresu daga wata babban cibiyar kasuwancinsu wanda sune suke sana'a a wajen tun daga shekarar 1977, kuma wannan gurin mallakin gwamnatin tarayya ne amma ya basu takardan kora daga wajen don ya nakasa musu kasuwancinsu, a dalilin haka aka hallaka wasu aka kone musu dukiya

A lokacin da ya gabatar musu da takardan koran, Maimartaba Sarkin Musulmin Nigeria Muhammad Sa'ad Abubakar ya tashi ya tafi Anambra da babban basaraken Sarkin Etsu Nupe, da babban kwamandan sojoji shiyya na 83 General Officer Commanding (GOC) 83 Army Division, suka hadu shi Peter Obi din suka ziyarci gurin da abin ya faru, Mai alfarma Sarkin musulmi ya roki shi gwamna Peter Obi akan ya janye kudurin koran 'yan arewa daga cibiyarsu na kasuwanci da yayi amma wallahi mutumin nan yaki amincewa, daga karshe ya koresu ya rushe musu matsuguninsu da cibiyarsu na kasuwanci, har da manyan masallatai guda bakwai duk ya rushe, yace suk wanda zai zauna a jihar sai yayi rijista yace duk wanda baiyi rijista ba 'dan ta'adda za'a kamashi ko a kasheshi

A lokacin wani malamin addinin musulunci bayarbe ne shine yake jan sallah a babban Masallacin Uga street Fegge gurin da aka haifi tsohon gwamnan jihar Kogi Alhaji Ibrahim Idris, a lokacin malamin addinin sai ya tafi ibadar Umara a Kasar Saudiyya, ya kuma hadu da Alhaji Usman Shamsuddeen tsohon minister a gwamnatin Jonathan shima yaje Umara, ya gabatar mishi da korafi akan abinda Peter Obi yake yiwa 'yan arewa a jiharsa, Ministan ya tabbatar mishi da cewa babu damuwa zai kira Peter Obi a waya ya masa magana akan abinda yake yiwa 'yan arewa domin abokinsa ne sunyi aiki tare a Banking Industry lokacin da shi Minista Alhaji Usman Shamsudden yana aiki da babban bankin Nigeria (CBN)

Lokacin da Ministan ya kira Peter Obi a matsayjnsa na wanda suka taba yin aiki tare kuma suke cin gwamnati tare ya kirashi daga Saudiyya ya masa magana akan abinda yake yiwa hausawa a jiharsa, maimakon ya duba mutuncin dake tsakaninsu kawai sai Peter Obi yaje ya samu maigidansa shugaban Kasa Jonathan yake bashi shawaran cewa ya kori Alhaji Shamsuddeen daga mukaminsa na minista, saboda kawai yana gadara yafi kusa da Jonathan kuma 'dan uwansa ne sunfi kusa

Jama'a; a lokacin Peter Obi yaci gaba da kakabawa hausawa ukuba da wahala aka dinga kashesu kamar dabbobi, wasu aka kamasu da ransu a daura musu buhun siminti a jefa a cikin kogi, ina zantawa da wani ma'aikacin tsaron sirri da yayi aiki a can muna tare dashi anan dandali na facebook yanzu haka, yace min bayan gawarwakin 'yan arewa da aka karkashe aka jefa a kogin Ezu shima ya jagoranci kwaso gawarwakin 'yan arewa da aka kashe a Anambra aka watsar dasu a bakin gadar Onaka, yace haka suka kwaso gawarwakin suka kawo Asaba suka bunne

Yanzu an sake dauko wannan mugun mutumi makiyin arewa da musulunci anaso ya zama mataimakin shugaban Kasa wanda karshen lamari su sake kakaba manashi ya zama shugaban kasa, shin 'yan arewa zaku amince? Ku tuna da wani rubutu da nayi kwanaki kadan mai taken WALLAHI WALLAHI 'YAN AREWA KAR MU YADDA, zaku sake fahimtar manufarsu da suke boye, misali idan Atiku Abubakar ya zama shugaban Kasa zai jasu a jikinsa sosai, kuma wallahi karshe amanarsa zasuci cikin sauki don su tabbatar da wannan rikakken 'dan rajin kafa Kasar Biafra ya zama shugaban Nigeria 

Don haka maganin ayi kar a fara, ko da wasa kada mu kuskura mu zabi jam'iyyar PDP a matakin shugaban kasa, aikata hakan cin amana ne, kuma tamkar cikin mu muke da6awa wuka, wannan rubutun bashi da alaka da siyasa, gaba muke hangowa da makomarmu

Yaa Allah muna rokonKa Ka tsare al'ummar Annabi Muhammad (SAW) daga sharrin wadannan mutane
Post a Comment (0)