NASIHOHI GA 'DALIBAN ILMI

NASIHOHI GA 'DALIBAN ILMI


Asalin wannan rubutun muhadara ce dana saurara daga bakin *Sheikh Abubakar Muhammad Sani Birnin-Kudu {Hafizahullah}* wacce ya gabatar da ita a garin Adamawa. A gaskiya nayi matukar karu sosai da wadannan nasihohi masu mahimmanci kuma sauraransu yasa zuciyata ta raurawa sai naji kaman Malam akaina yake Muhadarar. 

Ina baiwa yen uwa daliban ilmi da suyi kokari su nemi wannan muhadarar su saurara domin karuwa da wadannan fa'idodi.

Malam ya gabatar da Muhadararsa akan wasu abubuwa masu mahimmanci daga cikinsu:

1) *Ikhlasi:* Malam ya fara nasiha ga daliban da su ji tsoran Allah a duk al'amuran domin babu aiki da ake yin sa babu Iklasi. Kuma malam ya ja hankalinmu da cewa ya kasan kamar yadda dalibi yake a fili to ya kasance zuciyarsa haka take, domin mutum yafi kowa sanin kansa. Haka kuma Malam ya jawo hankalin da irin yadda dalibai ke yadawa abubuwa musamman a social media misali mutum yaje Umrah ya rika yadawa.

2) *Sabon Allah:* Malam ya yi bayani sosai akan wannan gabar domin sabon Allah yakansa a rufe zuciyar mutum ta yadda zuciyarsa zata dod'e ta daina amsa gaskiya daga karshe ta halaka. Shin sabon Allan nan a fili ne ko a bayyene yana da kyau a rika kiyayewa.

3) *Ruduwa Da Jiji Da Kai Da Ganin Girman Matsayin Da Ka Kai A Ilmi:* Malam ya jawo hankali ga daliban ilmi musamman in dalibi ya ga ya fara taka wani mataki a ilmi sai ya fara jiji da kai yana ganin cewa yafi kowa ko kuma yanzu ya isa ya fada ko ya bada fatawa, kuma ya musu cewa kar mutum ya rika ganin wadanda ba suyi ilmi maqasqantane.

4) *Tuna Mutuwa:* Malam ya yi bayani akan cewa yana da kyau dalibin ilmi ya rika tunani a kullum cewa zai mutu.

5) *Karanta Tarihin Magabata Na Kwarai:* Malam yayi bayanin cewa yana da kyau dalibin ilmi ya rika karanta tarihin magabata domin ya ga yaya suka nemi ilmi kuma Yaya suke mu'amala a tsakanin junansu. Kuma ya nusantar da cewa dalibi ya dauki *Siyaru A'alamin Nubala* domin ya ga yadda magabata su ke.

6) *Kiyaye Duniya Da 'Kyamatarta:* Ana wannan gabar shima Malam ya yi bayani mai mahimmanci ta hanya nuna dalibi bai kamata ya sanya soyayyarsa ga duniya ba musamman zamanin da muke ciki, sai ka ga jama'a su na jira malami yayi wani dan qiris su yaya ta saboda sai abi a hankali.

7) *Himmantuwa Da Ibada:* Malam ya ja hankali sosai da yawa wasu dalibai sukan zaci cewa don sunyi ilmi shikenan sai su rika sakaci da ibadarsu. Wanda hakan kuskure ne babba, domin magabata ba haka suke ba; domin hakan ma ita ce kariya daga gare su. Saboda haka a kiyaye ibada sosai kada ilmi ya hana yin ibada.

8) *Rashin Gaggawa Wajen Yin Fatawa:* Malam ya jawo hankalin dalibai da su sa ni cewa duk sanda mutum aka yi ma sa tambaya ya bayar da amsa to ya sa ni kamar ya wakilci Allah da Manzonsa ne. Amma abin takaici sai ka samu dalibi ko malami yana da an tambayesa sai kaji ya bayar da fatawa. Malam ya bada misali ga Imamu Malik.

9) *Rashin Alfahari Da Nuna Kafi Kowa:* Malam ana gabar shima ya ja hankalin dalibai akan su guji alfahari da Ilmi ta hanyar nuna cewa yafi kowa ko kuma kaji mutum yana fadin cewa duk garinsu bashi da malami, wanda magabata na kwarai ba haka suke ba. Malam ya bada misali da Imamu Malik cewa kafin ya fara karantarwa sai da Malam 70 su kayi sheda akan cewa ya kamata ya fara karantarwa. 

10) *Mayar Da Harkan Jarhu Wa Atta'adil Ga Malam:* Malam ya baiwa dalibai shawarar cewa aikin tantance malamai ace wancen yayi dai dai ko yayi kuskure ba aikinsu ba ne aikin malamai ne saboda haka dalibai su dena shiga fagen da ba nasu ba.

11) *Rashin Son Asan Wane Ya Fishi Ilimi:* Malam ya yi nasiha sosai ta yadda dalibi yana jin yafi karfin ace wane malaminsa ne.

12) *Nisantar Jayayya:* Malam ya yayi nasiha cikim hikma da bayar da shawarwari ga dalibi, ganin yadda dalibai su ke bata lokacinsu wurin jayayya akan wata mas'ala wacce zata shagaltar da su akan neman ilmins. Abin takaici har a group na kafofin sadarwa.

13) *Rarrabewa Tsakanin Malamai:* Malam a wannan gabar ita ma yayi bayani sosai ganin yadda wasu dalibai suke zaben malamai ace wane ai yayi takhassusi ne a bangare guda ko kuma ai wane bai fita jami'ar musulunci ba. Duk kuskurene da dayawa daliban ilmi suke fadawa.

Wannan kadan daga cikin abinda na iya tsakurowa kenan a cikin Muhadarar. Saboda ina kara bawa yen uwana dalibai da su nemi wannan muhadara su saurara da kunne na basira.

Allah ka shiryar da mu ka kara mana ikhlasi cikin neman ilmin mu.

*_Dan uwanku a Musulunci: ✍_*
*_Abu Ja'afar_*
*_Yusuf Lawal Yusuf_*
7th Rabi'ul Auwal, 1440Ah
{15/11/2018}.
Post a Comment (0)