*Tambaya:*
Assalamu alaekum Malam
Tambayata itace shin mace zata iya daukar alqur'anic mae girma lokacin da take cikin jini?
.
*Amsa:*
Wa'alaikumussalamu Warahmatullah.
Babu wani nassi Qarara daga Alqur'ani da Sunnah da ya haramta wa mace mai haila daukar Alqur'ani ta karanta, duk da cewa akwai malaman da suke a kan haramcin haka, to amma dukkan hujjojinsu ba masu qarfi bane, don haka mu dai kam yanzu a wajenmu ya halatta mace mai jinin haila ta dauki Alqur'ani ta karanta har zuwa lokacin da za mu samu dalili mai qarfi a kan haramcinsa.
Wallahu A'lamu.
.
Daga Zauren
*🕌Islamic Post WhatsApp.*
_Ku turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256* don shiga group dinmu a WhatsApp._