RANAR HARSHEN HAUSA
Sunan Wak'a : Hausa Ba Dabo Ba
Rubutawa/Rerewa: Shamsu Hamza
Kiďa: Mashkur Umar Zaria
Shekara : 2012
Amshi:
Harshen da shi na gada yau ni nake yabawa, tilas na gai da kai harshen Hausa ba dabo ba.
Bisimillah Rabbana Allah Jallah mai iyawa,
Sarkin da Shi Ya yo Ummi har da Abba nawa,
Dubban salatika Allahu Ka yo dad'in dad'awa,
A wurin Nabiy Mad'u Da'i ďan K'uraishawa,
Alihi wa Sahbihi da dukan mabiyanSa ban bari ba.
Ga Shamsu na taho ban dai yi k'asa a gwiwa yau ba,
Bori ba a yin sa da sanyi naj jikin ga66u6a,
Gadon gida alala ga raggo don ba zai iya ba,
Kowa ya bar gida gida zai bar shi bai kula ba,
Sunanta wagga wak'a yau 'Hausa Ba Dabo Ba '.
Na ďauki garkuwa na sa sulke na ďau takobi,
Sannan na kinkimo adaka bindigar maharbi,
To kun ga nai shirin yak'i taimakan ni Rabbi,
Don yau da baki za a yi yak'i ne irin na zabi,
Duk wanda yat ta6a mini Hausata ba zan bari ba.
Harshenmu ba kamarsa kakaf Nahiyar Afurka,
Ba ma Afurka wai ba kawai ba duniya na ďauka,
In ban da Arabik to babu kamar sa kaf a doka,
Tilas na ce haka ko za ku kira ni na yi hauka,
Don ya ďarar wa Turanci ba mujadala ba.
FARFAJIYA
Farfajiyar K'asarmu ta Hausa dai tana Afrikan,
Ta je ta mamaye tsakiyar can k'asa ta Sudan,
Daga can Arewaci a Nijar ta haďe da Azbin,
Har ta wuce hamada nan kudu ta haďa da Benin,
Da garuruwan da tal lashe ba zan k'i in faďi ba.
Da akwai garuruwan Gwarawa har da Kambarawa,
Sannan da ma garin Dakarawa har da Acifawa,
Kana ta yammaci Sanwai da Zabarma tai haďewa,
To sai ta can Gabas ta wawushe Barno ba tsayawa,
Lallai ko ta wuce raini malam idan ka duba.
SIFFA
In anka ce Bahaushe za na faďe shi dai tak'aice,
Fatar jikinsa kun ga bak'a ce ga ni dai kwatance,
In har ko za ya yo magana da Hausa zai yi zance,
Sannan yana rik'on al'adu nasa ko a kwance,
Domin ko rayuwarsa a al'adunsa ta guraba.
MUHALLI
In dai ana batu na muhalli mu gini mukan yi,
Ďaki mu yo Uwaďďaka ko Shigo ko Shirayi,
Mu yo rufi na Soro, Jinka, Boto na yayi,
Zane a Shiggifa Zaure Alkuki mukan yi,
Shadda ko Sakarkari ko Salga ba a Bedroom ba.
SUTURA
To kun ga dai tufa ta Bahaushe dole ne a kalla,
Domin mukan sako riga wando mu ďora hula,
K'ube, Ha6ar-kada Dara har Dankwara madalla,
Sannan mu sanya takalma masu kyau na shela,
Shure da ma Feďe ko Sau-ciki ko ko Taka-teba.
Fannin tufa ta mata ma mun ďara wa gasa,
Don sai su sa Zane da Taguwwa tasa ba makusa,
Su sanya Tsakiya da Awarwaro wanda ba irinsa,
Ga Kallabinsu ko Fatala ko Gwaggwaron a k'yasa,
Su lullu6o Gyale ko Gyauto ba sui tsiraicika ba .
Fannin Tufar Saraki ba kamarmu je ka duba,
A shigarsu Rawwani, Alkyabba har da Riga-babba,
Kufta da Tokare, Shakwara, Jamfa ba rasa ba,
Aiki na hannu Dagi ko Aska-tara ku duba,
Asalinmu tun a da ba mu yo yawo tsirara kau ba.
ABINCI
Shi galibin abinci namu hatsi muke haďewa,
Irin su Alkama, Masara, Gero da ma su Maiwa,
Kayan haďi akwai Gishiri, Mangul da ma Ku6ewa,
Kuka da Kalkashi, Lalo, Tafasa da Tungunuwa,
Kanwa da Daddawa ga Mai da Albasa ku duba.
Kaya na marmari a K'asarmu ba za a ko rasa ba,
Don ga su Zogale da Rama, Yakuwa da Kwalba,
Tafasa da Yaďiya, Dinkin har Goruba da Gwaiba,
Doya da Dankali, Rogo mui Mandak'onmu babba,
Kaya na marmari wasu sunayensu ba sani ba.
SANA'A
Sannan wajen Sana'a mu gado muke biyewa,
Farko akwai Gini, Magina su suke yiwo wa,
Noma da Sassak'a, K'ira, Jima, Sak'ar abawa,
Ďinki da Kasuwanci, Fatauci, Jaura, Su haba wa!
Kiwo da masu Fawa Mahauta wassu ko Maharba.
ADDINI
Kana ta 6angaren Addini ko fa ban faďi ba,
Kusan gaba ďaya sai wanda ba za a ďan rasa ba,
Mun shaida La'ila Ha'ilallah ba da alfahar ba,
Sannan muna yawan k'aunar Rasulu ba ba'a ba,
Kana muna gaba a wajen bautar Ilahu Rabba.
ILIMI
Har yanzu dai k'asar Hausa idan akai kulawa,
Muna da nau'uka na rututu biyyu ba musawa,
Boko da Ajjami biyu kenan ga su nai faďowa,
Muna da illimai tari da sun fi zayyanowa,
In ma na ce ko za na faďa ba za na ma iya ba.
ADABI
Harshenmu ba kamar sa a don ya ďaram ma saura,
Adabinsa kwai su Tarihi har da Almara,
K'issa, Tarihihi da Hikaya ga su babu kyara,
Har ma da Zambo ko ko Habaici Waskiya da Sara,
Wasa kwaikwayo mu yi wak'a Hausa ba hulul ba.
Sannan mu yo Kacici-kacici har mu tsara tashe,
Sannan akwai Kirari Take ga Salo na zanshe,
Kana muna Karin Magana Kiďanmu babu kushe
Tatsuniya da wasanni akwai su kodayaushe,
Sannan akwai Raha da Nishadi Hausa ba mu gaba.
KALMOMI
Harshenmu kwai wadatar kalma walla in ka duba,
Komai muna da sunayensa a Hausa ba ba'a ba,
Bargo da Bibiya, Bera, Bebeji har da Baba,
Bak'o, Bagobiri, 'Bera, Balami, Bak'i da Babba,
Baiko, Baro, Bari, Bororo duk Hausa ce ku duba.
Tsando da Tsattsafa, Tsami, Tsame da ma su Ratse,
Tsoho, Tsaka-tsaki, Tsakiya, Tsutsa da Rantse-rantse,
Tsaki, Tsaro, Tsaka, Tsattsama, Tsada har da Datse,
Hatsaniya, Hatsi, Tsari, Hantsi, Datsi da Latse,
Dutse da Tsakiya, Fatsa duk a Hausa ba dabo ba.
Kura, Kare, Kara, Karara har Kokara da Kora,
Karo, Karoo, Kira da Kurame, K'orama da Kara,
Gulbi da Goruba, Gwiwa, Gwano, Gamo da gora,
Gari da Gargari, Garari, Gora, Garii, da Gyara,
Abin akwai yawa zan shekara ba Gamo faďi ba