SAMUN GAFARAR ZUNUBAI NA KWANA GOMA A RANAR JUMA'A

*SAMUN GAFARAR ZUNUBAI NA KWANA GOMA A RANAR JUMA'A*


Daga Salmanal Farisy رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ,yace;Manzon Allah SAW yace;
*(Babu wani mutum da zaiyi wanka ranar juma'a kuma ya tsarkaka gwargwadon iko na tsarkinsa,kuma ya shafa mai daga mansa,kuma ya sanya turare,sannan ya fita zuwa masallaci,bai qetara tsakanin mutum biyu ba,sannan ya sallaci abinda aka wajabta masa,sannan yayi shiru a lokacin da Liman yake Huduba,face an gafarta masa tsakanin wannan juma'ar zuwa wata juma'ar)*
@صحيح البخاري-رقم:(883).

A wata riwar acikin Saheehu Musulim;
*(.....Da karin kwana ukku....)*
@صحيح مسلم

ابن حجر رَحِمَهُ اللهُ تَعَالَى:-
Yana cewa;
"Kankare zunubai daga juma'a zuwa wata juma'ar baya samuwa sai ya ciki Sharuddan da aka ambata acikin hadisi,sharuddan sune kamar haka;

*Yin wankan Juma'a*

*Yin tsafta da gyaran jiki da tufafi*

*Sanya turare mai dadin kamshi da shafa mai*

*Sanya tufafi mai kyau*

*Tafiya masallaci cikin nutsuwa*

*Kada ka qetara tsakanin mutum biyu*

*Kamewa daga chutar da wani*

*Kuma kayi nafilar gaisuwar masallaci*

*kuma kayi shiru ka saurari huduba*

*Kuma ka baryin Lagwu lokacin huduba*

*Ka fuskanci Liman lokacin da yake Huduba*
@فتح الباري:(372/2)

  Allah ne mafi sani

Post a Comment (0)