TUN KAFIN AURE 31

TUN KAFIN AURE💐31




Senator Rufai ranshi duk a bace da aka sanar dashi result din test din. Ya kalli Hajiya ni yanzu ya zanyi da Hafsatu? Duk irin abinda ya faru kafin a bashi aurenta gashi kuma baaje ko ina ba rayuwarsa ta baya tun kafin yayi aure tana dawo musu. Hajiya tace ni dai idan zaka dauki shawarata Rufai kabari yarinyar nan ta tare. Kullum mu kwana mu tashi da ita bata san makomar aurenta ba ai kaga ba dadi. Irin wannan ne idan iyayenta suka sani lamarin sai ya baci fiye da yanzu. Mommy tace anya Hajiya a bar shi da yar mutane kuwa? Bafa kowacce mace bace zata yarda ta zauna da mutumin da yake da da a waje ba. Wata ko dan kishiya bata so bare dan kafin fatiha. Senator yace to ku bani zuwa wata asabar din sai a kaita. Kisa su Hamida su tambayeta irin kalar motar da take so ma. Mtsw Ya danyi tsaki yaron nan bai min adalci ba wallahi. Gara tun da sauran mutumci na naje har gida muyi magana da babanta.

Zaman dakin duk ya isheta tana ta canja tashoshi babu wani abin kallo ta mike ta daga labule tana kallon waje. Tun jiya da su Nafisa suka zo da nurse bata sake fita daga dakin ba, Nafisa dai ta fada mata zasu dawo ta kai Talatu scanning. Tun dazu take jiran zuwansu ko ta sami abokin hira. Su mommy suna iya kokarinsu wurin debe mata kewa sai dai kuma suna cikin damuwar maganar cikin nan. Tana dan tunaninta ne ta kalli kasa suka hada ido da Junaid. Wani abu ne ya ratsa mata zuciya har kafarta. Murmushi yayi mata tayi saurin sakin labulen. Ta koma ta zauna bakin gado. Meyasa take saurin rikicewa ne akan Junaid..abinda take tambayar zuciyarta kenan.

Meyasa zata masa rowar kyakkyawar fuskarta ne. Su Hajiya suna masa gashin kuma gashi yanzu yana cikin jindadin kallonta ta gudu. Girman laifinsa yasa ya danne zuciyarsa bai dami iyayen nasa akan a bashi matarsa ba. Itama yana jin nauyinta sosai a ransa. Ina amfanin badi ba rai? Karamar yarinya tana masa kwarjini saboda ya zubar da girmansa a waje. Ga su Rosie sunyi kane kane a gidansu. Fasa shiga gidan nasa yayi ya koma main house. Mai aikatan gidan suna ta gaishe shi ya haye sama da sauri. Addua yake kada kowa ya ganshi a hanyarsa ta zuwa dakin Hafsi.

Rub da ciki tayi tana karanta wani littafin tarihin Annabawa da Hajiya ta bata taji an bude kofar. Duk a zatonta Nafisa ce tayi saurin juyuwa babbar yaya ina ta jiranki tun dazu yau bani da....kallon da yake mata bayan ta juyu yasa tayi shiru. Ya zaka shigo min ba sallama? Ni da dakin matata har sai nayi sallama? Ya kara kallonta ita duk kayan jikinta suna mata kyau. Dinkin yau ma riga da skirt ne fitted sunyi mata kyau sosai abinka da yar Mama tela. Ya jawo kujerar dressing mirror banda gulma duk wannan kwalliyar kice babbar yaya kike jira? Fada min gaskiya  dai ni kika yiwa wannan kwalliyar ko. Bargo ta jawo ta rufe jikinta da sauri ni ba kai nayiwa ba. Kan gadon ya dawo ya zauna a gefenta ya rage murya are you sure? Har fa zuwa kika yi bakin window don na ganki kuma na gani. Daga cikin bargon tace ni Allah ba kai nayiwa ba. Ji tayi kamar ya tashi daga kan gadon sai dai kuma har fuskarta ta rufe yace malaiku na jinki kina cewa yar miji kika yiwa kwalliya ba shi ba. Yau littafinki sai cika da rubutu amma fa daga na hagun. Muryar nan ta shagwaba ta fara yi ni ba haka nake nufi ba...kafin ta karasa magana taji ya daga bargon daga wurin kafafunta ya shigo ciki. Hannuwansa yasa ya danne duka sides din don kada ta bude. Tuni idanunta suka raina fata, they were so close suna shakar numfashin juna. Ya kashe mata ido daya ina jinki wa ma kika yiwa wannan kwalliyar? Ki fadi abinda nake son ji sai na fita salin alin. Kanta a kasa tace kai. Malama ni banji ba fa. Ta sake cewa kai a hankali. Bari na sake matsowa kusa kila zanfi ji. Da karfi tace kai nayiwa. Good girl to ki dan bani chance mana na yaba kwalliyar. Bata ankara ba taji ya janyota ya rungume. Yana shafa mata gashi a hankali. Wata ajiyar zuciya yayi Hafsi Hafsi ki tayani addua yau nayi interview har biyu ta neman aiki. Nasan nayi laifi da yawa shiyasa su Mommy basu da time dina amma don Allah zaki zama friend dina kuma special adviser dina. Dago kanta tayi tayi masa murmushi eh. Thank you so much. Ya mike yau zaki min girki? Ban iya ba ta bashi amsa. Au kin manta da malaikun ne? Itama mikewar tayi na iya, me zaka ci? Kallonta ya sake yi gaskiya kayan nan naki fa suna...kodayake ba komai ki dai rufe jikinki kafin kije kitchen din. Indomie da kwai nake so ina sonta sosai. Idan kin gama ki kirani. Wayarta ya dauka yasa mata number dinsa. Duk ta tsufa anma dena yayin irinta. Itama Gwaggo Zainab ce ta siyo mata irin second hand dinnan. Ki taho dashi daki zanzo na karba. To kawai tace ya fita. Tayi tsaki meyasa idan taga Junaid take zama wata wawiya ne. Ko dan jan ajinma sai ya nemi ya gagareta.

Kasa ta sauka babu kowa sai  masu aiki ta dafa masa indomie biyu da daffafen kwai biyu. Tana shiga kitchen Rosie ta hangota ta koma daki da sauri ke Tilly tashi mu jirata a hanya. Akan tray ta dora zata fito wata mai aiki tace madam bari na kai miki Hafsi tayi dariya ai ba nauyi Chinwe nagode. Tana tafiya kamar daga sama Tilly tazo ta bangaje abincin ya zube a kasa plate din ya fashe kawai sai ji tayi Tilly na ihu wayyo Allah cikina.


Batul Mamman💖
Post a Comment (0)