TUN KAFIN AURE 32

TUN KAFIN AURE💐32



Wani irin radadi ne ya ziyarci kafafunta duka biyun ta runtse ido ko motsi ta kasa yi saboda duk wurin pieces din glass ne. Tilly kuwa kwanciya tayi wanwar a kasa tana kwarma wayyo cikina, wayyo ta kashe min da na shiga uku. Rosie tace kiyi hakuri Talatu ki mike tsaye. Hafsi ta kallesu tana cewa sannu amma duk kafafunta sun kone saboda zafin abincin harda cikinta don karamin mayafi ta yafa sanin cewa babu ma aikata maza da ake bari su shigo cikin gidan. Ga plate din da ya tarwatse wasu duk sun soke mata saman kafafunta. Duk da haka bata damu ba ta duka tana son taya Rosie ta daga Tilly tsaye. Hannunta taji Tilly ta make tana kara sautin murya. Muguwa azzaluma don kawai ina da cikin mijinki shine kike son zubar min dashi. Wallahi duk abinda ya sami dana kotu ce zata raba mu.  talakar banza.

Wawan mari Talatu taji an dauketa dashi. Mommy ta sake daga hannu Hajiya ta riketa yi hakuri Salma muji abinda ya hadasu. Rosie cikin kukan makirci tace Talatu ce ta fito zata sha iska tace dakin yana tayar mata da zuciya. Tana fitowa wannan yarinyar ta nuna Hafsi, mommy kuwa ta make hannun karki sake nuna min yarinya da yatsa wallahi. Rosie ta share ta cigaba da magana kawai tana ganin Talatu sai tace mata zanga yadda zaki haifi dan shege a gidannan. Tray din da plates din da ke kai duk ta tura mata a ciki. Hajiya ko kadan bata gaskata zancen ba ganin yadda Hafsi ke kuka tace mamana me ya faru. Hafsi ta fadi iya abinda ta sani. Mommy ta kama hannunta su koma falo ayi maganar.
Sai a lokacin suka kula da yadda jini ke bin kafar Hafsi ta dama Mommy tace maza a kira mata Junaid yazo ya kaita asibiti.

Da fara'arsa ya shigo falon. Mommy daga nasa yarki dafa min indomie sai ace in kaita asibiti. Ko ta kitse albarka. Gunjin kukan Tilly yaji daga bayansa ya juya da sauri lafiya? Rosie hade rai ka tambayi matarka da take son zubar wa Talatu da ciki. Yace au ashe sunanta Talatu ai na zata Tilly ne. Muryar Mommy yaji tana kiransa. Ya zan aika a kira ka sai kazo kana wani zancen daban. Ka dauko key mukai yarinyar nan asibiti nace. Ya kalle Hafsi duk fuskarta hawaye yayi saurin karasawa gabanta. Me ya faru Hafsi garin yaya kika ji jiwo? Mommy tace ka tashi mana ka zauna kana mata tambayoyi.

Suna shiga motar Nafisa na isowa Hajiya tace ta debo su Rosie su taho tare. Amma ta taho da security don kada su zama su kadai. A motar Junaid kuwa Mommy tana ta balai ya dauko musu masifa har gida. In Allah Ya yarda sai cikin ya zube. Ga Hafsi nan ki saki jiki kiyi ta zuba masa 'ya'ya tunda su yake so. Hajiyan dangi ta gama waya da senator ta sanar dashi halin da ake ciki sannan ta dubi mommy tana bata hakuri. Junaid kuwa banda sannu babu abinda yake fadawa Hafsi. Hawaye ne wani ke bin wani a idanunta don ita kadai tasan me take ji musamman a cikinta. Ga babban mayafi ta yafa wani karin zafin a cikin.

Suna isa asibiti Junaid daukarta yayi don ganin yadda kafar taki dena jini. Emergency aka shige da ita da Tilly. Kururuwa kawai Tilly take yi ita tasan danta ya mutu. Ai kuwa basu dade ba nurse ta fito tace Tilly tayi bari. Nafisa ta rike baki cike da mamaki wato don sunji yau zaayi scanning suka bullo da wannan abin. Dariya tayi tana gyada kai sai tayi maganin mutanen nan.

Junaid yana tsaye doctor ya zare glass dinda ya shige kafar Hafsi yana ta mata sannu. Bayan an gama cirewa ansa plaster ya lura ta kasa kwanciya da kyau yace Hafsi akwai inda yake miki ciwo bayan kafar ne? A hankali ta daga kanta tace cikina. Fatar ta daye. WHAT??? Shima ya gama tsorata yayi saurin cire mayafin ya nunawa doctor din. Da almakashi ya yanke barin rigar daya kwanta akan cikin yace yi hakuri fatar bata cire ba. Ya dauko magani zai saka mata Junaid ya karba don tuni ya kule da kallon da yake mata. Dr bai ma san me yake ba ya nuna masa yadda zai shafa  ya fita.
Ba karamin tausayi ta bashi ba yana shafawa tana runtse ido duk hawaye. Sai da ya gama ya duka yana hura mata cikin tuni ta hadiye kukan. Ya dago kansa sannu kinji Hafsi rabin raina. Ashe tsautsayi ne yasa nasa ki girki. Amma me ya hadaki da waccan. Fada masa komai tayi yace ba komai. Allah Yayi mana jagora.

Dr Sunusi yana fita Nafisa ta ja shi suka yi magana tace dr ina jin yarinyar nan cikin karya gareta. Yace ya akayi kika sani tace yar uwarmuce ce daga garinmu ina jin karya take ta matsu ne ta haihu sai tayi ta kiran cikin karya gashi kwanaki tayi bari baa wanke cikin ba. So nake don Allah kayi mata wankin ciki zan biya ko nawa ne. Bani da burin da ya wuce Talatu ta sami haihuwa. Ta dan matse hawaye. Dr Sunusi yace ba komai Hajiya ki kwantar da hankalinki. Yana fita Nafisa tace shegiya ai karen bana shike maganin zomon bana.




Batul Mamman💖
Post a Comment (0)