YADDA ZAKA SACE ZUCIYAR BUDURWA KO MATAR KA

*✤ YADDA ZAKA SACE ZUCIYAR BUDURWA / MATARKA ✤*

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji

FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348141712330

Kasantuwar mu na ‘yan adam a doran Ζ™asa, Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu.

Saboda haka samarin da suke Ζ™oΖ™arin ganin mallakan zuciyar ‘ya mace ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyin guda takwas da ake bi don sace zuciyar budurwa. Hmmmm 

TSARI:✎.... Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba.

KYAU DA KWALLIYA:✎...

 Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar Ι—awisu.

KALAMAI:✎.... Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata ‘ya mace, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar Ι—an bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa.

KIRKI DA KULAWA:✎....

 Namiji yakan tafiyar da zuciyar ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci ko sa’ar da ba ta fi rana Ι—aya ba, ko kwana biyu a ce kana zuwa ganin ta ko kuma kana kiran ta, idan ya yi yawa ne a ce kun haΙ—u sau uku.

Musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare. Wani lokacin idan haΙ—uwa ta yi Ζ™aranci sai ka kirata a waya.

 Amma fa ka sani yawan zuwa gun mace ko masoyiyarka ce wani zubin nasa gundura.

 Ma’ana za ta ji duk ta gaji da ganin ka, musamman idan ya zama soyayyar taku ba ta yi Ζ™arfi ba.

KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA GABAN ƘAWAYE:✎..

.. Ka guji yawan kula yarinya cikin sahun Ζ™awayenta ko kuma cikin jama’a. Hakan zai karama kima, sannan da nesan ta kanka ga barin wulakanci. Wata kila lokacin da ka je mata cikin jama’a ko Ζ™awayen ta, ta ji tana son ka. To amma watakila a lokacin shigar da ka yi bata mataba da dai sauransu.


Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji

FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348141712330


Post a Comment (0)