UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA TARA.
Sosai ta shiga duniyar tunani tana kokawa dashi a yarda komai yake cakuÉ—e mata lokaci guda duk wata tufka da take yi ba a zuwa ko ina take wargajewa sosai take tunani wanda ita kanta bayi tsammanin kwakwalwarta zata iya yinsa ba ba tare da ta tarwatse ba hankalin ta sosai ya karkata zuwa ga duniyar tunaninta ta bar duniyar zahiri.
Tafiya take sannu a hankali wanda ita a karan kanta ba ta ina take jefa kafa ba kamar daga sama taji wata irin kara gabadaya ta karaÉ—e mata kunnuwa cikin yanayi na tsananin firgice ta dawo duniyarta ta na faman ambaton Allah gabadaya ta daura hannu akai ta rasa ita a ina take a wannan lokacin domin ta gama yanke tsammani komai zai faru a lokacin ba mai dadin ji bane sam! cikin duniyarta sosai take jin sautin na sauka a hankali gabanta ya fara raguwa daga faduwa da yake yi a hankali ta fara kokarin buÉ—e idanuwanta da suke runtse sosai jikinta gabadaya sai karkarwa yake yi kamar wacce aka jonawa wayar wutar lantarki.
"Ke!".
Kamar daga sama ta ji wata muryar ta amsa amo ga kunnuwanta sosai taji tsawar a ranta sosai da sosai gabanta ya fadi dalilin tsawar a hankali ta daga kanta da idanuwanta da suka rine sukayi jajir sosai.
Tsakiyar titi ta ganta tsaye ga wata bakar mota mai matukar dauka ido gabanta haske rana sai haske yake yi gefe guda kuwa wani matashi ne wanda ba zai hau shekaru ashirin da takwas ba zuwa talatin baki ne dogo mai kaurin jiki fuskarsa doguwa ce mai dauke da dogon hanci da manyan idanu masu kalar barci (sexy eyes) girarsa cike take da suma baka sidik da ita bakinsa dan madaidaici mai dauke da Laɓɓa Pink kala mai duhu kadan haka kansa akwai suma kwantacciya wanda ta samu gyara sosai tayi luf a samankansa sai faman kyalli take yi jikinsa sanye yake da kananun kaya farin wando jeas sai riga mai kalar Ash-colour a gaban rigar an yi rubutu kamar haka *SO MUCH LOVE YOU* da kalar ruwan Gold kafarsa kuwa takalmi mai kalar silifas mai ruwan kasa-kasa sosai da sosai takalmin ya amshi kamarsa mai dauke da dogayen yatsu wanda suka sha gyarar farata sosai.
Lokacin da Mareeya ta gama ƙare masa kallo lokaci guda ta kau da kai gami da jan guntun tsaki kafik ta sake daga idanuwanta ta dube shi shima ita yake kallo wanda kallon ba za ka iya ajje shi a mataki daya ba ne tausayi ne ko na kiyayya
Gefe da gefen titin kuwa tun da abin ya faru jama'a sukayi cirko-cirko suna kallon abin da zai wakana domin har ga Allah kowa ya sadakar mai Motar nan zai yi sama da Mariya sai dai buzunta amma sai Allah yayi ikonsa ko taba bai yi domin kuwa hanzari yayi sosai wajan taka burki.
"ke wacce irin dakikiya ce baki da hankali ne na lura da alamun kan ki akwai ciwo a cikinsa ko".
Sosai ya ke maganar cikin fada yana faman daga hannu kamar zai kwashe ta da mari yana kara fiddo da manyan idanuwansa waje yana sauke su akan ta ita har zuwa lokacin idanuwanta na kansa sai dai sun cika kwalla sosai kadan suke jira su zubo.
Nisawa yayi bayan ya gama kare mata kallo sosai da sosai.
"a fuska kamar mai natsuwa amma sam ba haka bane na lura ba ke burik rayuwar duniya cikin duniyar ki sam! bakya lale marhabin da duk wani farincikin duniyar nan a rayuwarki".
sosai take jin sautin kalaman sa na sauka a kunnuwant suna samun masauki sosai take jin daci da bauri a kalamansa sosai take jin ranta yana baci da sauri ta kau da kai daga barin kallonsa bayan ta watsa masa wani kallo wanda a karan kanta ba ta san tayi sa ba.
"In ba ki son Rayuwar duniyar ai gwanda kawai ki fadi ki samu wani ya turmushe ki da mota ko ya gille maki makoshi da wuka ba wai ki zo ki daura mani zunubin da ba nawa ba haka kawai ban san hawa ba sai naji sauka ki jaza mani BALA'I ki bar ni da zaman gidan kaso".
Ta fara gajiya da kalamansa sosai komai take ji nata yana jin haushinsa sosai take jin bakin cikin haduwa dashi a wannam lokacin.
"ga ki Mace har mace amma bakin san dadin rayuwar 'ya mace a duniyar nan ba na lura CUTA KAI ki ke dashi kuma bakin DARAJAR dakike da ita ba da kinsan DARAJAR 'YA MACE a duniyar nan wallahi ba zaki so mutuwa ba".
A firgice ta dago idanuwanta wanda a wannan lokaci suka fra zubar hawaye ta sauke akansa mamaki ne ya cika mata kwanya sosai a zuciyarta ba abin da take ayya nawa illa anya mutumin nan na da hankali kuwa anya bashi ya dace alakabawa kalmar hauka ba anya bashi ya cancanci a kira mai CUTAR KAI ba anya bashi kansa ke ciwo ba...
"In da ni ce ke wallahi ko hanya da ganganci da BALA'I yake ba zan bi ba ke Tsautsayi in da ana ganinsa billahillazi ba zan doshi in da zai doso ni ba har ya shigo rayuwa ta ba".
Ta gaji tayi matukar gajiya da jin maganganunsa komai taji nasa ya bata mata rai sosai ba za ta iya tsayawa ta saurare shi ba abin sai yayi yawa da wanne za ta ji da halin da ƘADDARA ta je fata ko kuma da wannan banzayen kalaman nasa da taji masu kokarin haifar da CIWON RAI.
"Malama yasin ki ceci rayuwarki don duniyar nan gidan zamana gidan kuma jindadi...".
Ba jira ya dora a zancen sa ba ta mike ta fara tafiya a hargitse kamar wacce ta samu tabin hankali tafiya kawai take yi domin ji take yi kalaman wannan mutumin na koƙarin hauka ta mata hankalinta sosai da sosai hannu ta saka ta rufe kunnuwanta domin bata bukatar ta sake jin ko kalma daya ne daga cikin kalamansa ba ta so ko ganinsa ta sake yi ko a badininta domin ta sani Mummunar ƙaddara ce ta jeho shi rayuwarta ba komai ba domin kalamansa sun gama tabbatar mata da halinsa ta lura duniya gabadaya ta gama daureshi tamau har da rararr igiya.
Tafiya tayi sosai mai nisa daga bakin titi sosai take tunani tana faman sharce gumin da yake karyo mata dayake lokaci ne na rana ba wai zafin ranar bace ta dame ta a,a wannan mummunar gamon da tayi ne gabadaya ya kara jagula mata lisssafin ta sosai take jin takaicin fitowarta sosai take jin haushin wanna rana sosai zuciyarta da ruhinta suke zafi komai yana kara lalace mata.
"Yaa Rabbi!".
Abin da laɓɓanta suka kokarta fadi kenan cikin wani irin yanayi mai dauke da tashin hankali sosai.
Sannu a hankali ta isa gida kafin ta shiga sai da ta tsaya bakin kofa kamar mai kokarin tunano wani abu kafin ta ja dogon numfashi ta doshi cikin gidan baki ta dauke da Sallama tun daga soro ta fara jin rashim mutane a cikin gidan sosai da sosai take jin shiru ya gauraye gidan ba motsin ko dan tsako a cikin sa a haka har ta isa tsakar gidan ta tsaya yana a yarda suka barshi ko alfarmar shara bai ci ba gyada kai tayi kafinta doshi dakin mahaifiyarta.
Sosai take jin tausayin kanta sosai komai ke dawo mata sabo sosai take tuna ranar sosai take tuna komai sosai take tuna mahaifiyarta da komai da ya faru da ita can baya sosai da sosai taji zuciyarta na kara rauni ruhinta taji yana kokarin ajje mata komai kamar yanzu ya faru.
Kuka ne yake kokarin kwace mata wanda ita kanta ba ta san ya akayi ya zo ba ko da yake bai dace tayi wa kanta wannan tambayar ba domin ta sani ABOTA suka kulla dashi wacce ba ta tsammani akwai ranar yankewar ABOTAR.
hannunta duk biyu ta saka ta rufe bakinta domin ji tayi kukan na kokarin ba da sauti sosai da sosai.
Da sauri ta mike tashiga neman abin da ta zo dauka cikin lokaci ta kammala komai ta hada ta dauka komai tana yinsa ne cikin rashin hayyaci domin ta tabbata in ta zauna cikin dakin nan zuciyarta za ta iya bugawa ba za iya zaman sa ita kadai ba bata so ba za ta iya ba Allah ya gani gabadaya gidan ne ba ta son zaman sa a wannan lokaci ba za ta so ace ta zauka ba domin DUHU take gani sosau wanda yake kokari rufe mata idanuwa har ma da zuciya da ruhi a hanzarce ta bar dakin cikin sakanni ta bar cikin gidan gabadaya har zuwa lokacin hannayenta na rufe da bakinta domin bata bukatar kukan ya fasu.
gabadaya hankalinta ya tafi fatan ta ace ta ganta a cikin dakin dakin da mahaifiyarta take tare da mahaifinta ba ta so ace tayi nesa da su bata so ace komai ya fau bata nan tana so ace komai in ya tashi faru ya faru akan idon ta ta shirya ta shirya sosai da sosai komai za ta iya dauka komai da zai faru ta shirya masa zata iya jurewa za ta yi dauka ko meye ma ta shirya masa...
"MACE ƘYANƘYAWA".
'Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una'
Mariya ta dankara cikin tashin hankali domin wata katanga ce ta ji ta ruguzoma mata mai dauke da bama-baman tashin hankali sosai taji duniyar na juya mata sosai take ganin wasu taurari masu dauke da kayan yankin kawo mata tashin hankali na shawagi a idanuwanta ba ta san lokacin da ta zubda kayan dake hannunta ba ta daura hannu saman kai tana kokarin kurma ihu amma kafin ta kai ga aikatawa taji wani lallausar hannu yayi wa bakinta ƙawanya habawa ai Mariya ji tayi kamar taji ta ta nutse cikin kasa sosai taji jikinta gabadaya ya tsaya cak! duk sani abu mai rai da motsi na jikinta sai da taji yayi mutuwar wucin gadi zuciyarta kuwa ji tayi kamar ta tarwatse tayi daidai sosai komai ya fara dawo mata jikinta ya dau mazari idanuwanta a rintse sosai.
sautin ajje murmushin sa taji ya dakar mata dodan kunni kafin taji sautin muryarsa.
"Anya kuwa na dauka zan ganki a jaruma lamba guda amma sai na ga akasin haka".
sosai ta sake runtse idanu gami da sanya hannayenta ta toshe kunnuwanta ba abin da take ambato sai Allah a ranta da ruhi.
"Don Allah".
Ta fadi cikin tashin hankali da rashin abin yi
Sosai yake kallonta da yanayin da ta firgice lokaci guda gabadaya idanuwansa ya juye akanta yayi mata kur! da idanu fuskarta yake kallo bakinta dake rawa yake kallo sosai da yarda ta motsa laɓɓanta ha ta furta 'Don Allah'.
"Me nayi miki?".
a dan tsorace ta bude idanuwanta ta kalle shi ta sauke da sauri domin ba tayi tsammanin idanuwansa na kanta ba.
"Kayi Hakuri...Don Allah".
Miƙar da ita yayi daga durkushen da tayi sosai yake kallonta yana kallon yarda jikinta ke rawa da alamun tsoro sosai take ji akanta murmushi ya saki kafin ya motsa laɓɓansa.
"Ba abin da kikayi mani, ki natsu mana garki ba da mata mana".
Ba ta son jin muryarsa balle kuma kalamansa wanda take yi wa kallo a yan ta'adda da fashi da makami domin ba komai cikin kalaman nasa sai kokarin kashe rayuwar wani rai.
"Ya sunanki?".
Ya fadi a wannan lokacin yayi kasa sosai da muryarsa cikin rarrashi.
ta gefen ido ta kalle shi har yanzu idanuwansa na kanta a dam tsorace ta waje idanun nata sosai tana motsi da baki alamun son magana da kyar ta samu ta furta.
"Mariya".
A nata tunanin in ta fadi zai sake ta domin rikon da yayi wa hannunta ji take yi kamar wuta domin haushi da takaici gabadaya ya rufe ga kuma tsoransa da take ji ya samu waje a zuciyarta ba ta so ƙaddara ta sake watso mata shi a rayuwa ba ta lura ƙaddara sam! ba ta son ta in dai a faggen natsuwar rayuwarta ne.
Sosai taci dacin abin da yayi mata ya taso mata cikin karfin hali ta dago kai ta watsa masa wani kallo mai cike da gargaɗi kafin ta fara motsa laɓɓanta.
"Meye hadi na da kai na dauka tun dazu muka raba gari da kai ko? to don haka ka rabu dani ka fice daga duniyar rayuwata ba abin da ya gama ka dani ina mai rokon ka ka tafi".
Tun da ta fara magana yake kallonta yana sakin wani irin Murmushi wanda ya dan tsorata ta amma ba ta bari hakan yayi tasiri a zahirin fuskar taba kau da kai tayi gami da jan guntun tsaki.
Lokaci guda murmushin dake kan fuskarsa ya dauke sosai ya ji zafin tsakin da yaji tayi masa yarinya karama har ta kalli tsabar idanuwansa tayi masa tsaki sosai yaji abin a ransa amma sai ya kanne ya sake gayyato murmushi ya daura a fuskarsa.
"MARIYA".
ya ambaci sunan cikin amo mai sauti ita kanta sai da taji faduwar gaba duk da taji wani iri da yanayin da ya ambaci sunan nata kamar shi ne ya halicce shi.
Ba tanka ba kamar yarda shima baya bukatar haka.
"HUZAIF".
ya fadi yana mai haɗe laɓɓansa waje daya yana cizawa sosai yake jin daci a ransa sosai da sosai yake jin bakin cikin abin da yarinyar nan tayi masa ba ya tunanin a duniyar rayuwarsa akwai 'ya mace mai amsa suna mace ta taba kallonsa tayi masa haka ko a cikin mafarkinsa gyada kai yayi.
"Bani da wata niyya akan ki ta cutar wa ki yarda dani in da ni mai cutarwa ne da tuni komai ya tabbata akan ki na cutarwa".
Sosai yayi kasa da muryarsa ya na furucin yana kallonta ita kuwa kanta na kasa gabanta na faman bugawa duk sakan sosai take jin tsoro da firgice na mamaye ilahirin jikinta zuciyarta tana amsa amo da sunan da taji ya ambata.
Ba ya zata yarda dashi ba ko kadan, domin dukan farko da yayi mata shi ya tabbatar mata da ko shi waye, don haka dole ta nemi tsari dashi a duniyar rayuwarta da sauri ta durkusa tashiga hada kayanta da suka warwatse bayaj ta fizge hannunta daga gareshi ba ta sake bi ta kanshi ba komai yin sa take cikik hanzari da kokarin barin wajan domin ba zaiya cigaba da tsayu dashi ba ko kadan ba ta muradin hakan.
Huzaif mamaki ne ya cika msa zuciya sosai yarda da ya ga Mariya na komai nata cikin nuna halin ko in kula gareshi ya lura sosai cikin idanuwanta akwai tsanarsa hakan ba karamin mamaki ya bashi ba saboda bai san dalili ba shi dai ya san bai yi mata wani abu na cutarwa ba amma yana mamakin yar da tsanarsa ta sami gurbin zama a kwayar idanuwanta wanda ya tabbatar hakan ne har a zuciyarta.
Murmushi ya saki gami da dunkule hannayensa waje guda ya zuba mata idanu yana kallon yarda take tafiya cikin sauri saurin da daka kalle shi ba jarumta a cikinsa domin tafiya take tana hada hanya kamar wacce tayi tatir da kayan maye.
Sosai Mariya take ji a jikin ta ana kallonta tun da tabar wajan domin tasan dole hakan ta faru dama sosai zuciyarta ta shiga saƙar fargaba domin sosai take jin tsoron Huzaif ko da dai bai nuna mata a kalamansa ba amma ta ji a jikinta haushin ta yake ji haushi na sosai da sosai.
Sai da tayi nisa sosai sannan ta ja burki ta tsaya tana mai da numfashi har zuwa lokacin kuma jikinta bai bar sanar da ita ana kallonta ba. A hankali ta juya sosai gabanta ya yanke ya fadi domin hango shi tayi zaune saman Motarsa mai kirar BMW M6 baka wuluk da ita idanuwansa na kanta da sauri ta dauke kai tana mai ambatar.
"Yaa Rabbi! Kayi min tsari da wannan mutumin da yake kokarin bibiyar rayuwata".
Kara azama tayi a tafiyar ta sosai take sauri kamar wacce zata kifa kallo daya zaƙayi mata ka tabbatar da ba natsuwa game da ita duk in da ta gilma sai an bi ta da kallo domin kuwa gabadaya a hargitse take daurin zanin da yake jikinta abin a kalla ace ba natsuwa ne haɓa daya ta zanin sai faman reto yake yi yana jan kasa kafar nan ta ta bututu tayi da jar kasar dake hanyar da take bi zuwa komawa Asibitin.
Tunda ta bacewa ganinsa ya koma cikin Motar sa ya yi mata Key ya bi bayan ta a hankali har ya isa Asibitin shi ma can gefe guda ya samu yayi Parking ya fito yana karewa Asibitin kallo tunda daga zubin yanayin Asibitin da tsarinsa ya tabbatar sai marasa hali ne masu zuwa cikinsa don shi dai ya tabbata ko mura yake yi ba zai zo wannan asibitin da sunan neman magani ba sosai ya shiga tunanin abin da ya kawo Mariya wannan Asibitin ya tabbatarwa zuciyarta kila wani nata ne bashi da lafiya lura da yayi da yanayin datake ciki ya tabbata nata ne makusancin na sosai da sosai ba lafiya ji yayi kamar ya shiga asibitin amma sai wat zuciyar ta hanashi tana mai tambayarsa in ya shiga yayi me? A matsayin sa na wa zai je gareta? Tambayoyin da suka taru akansa kenan ya fasa shiga asibitin da sauri ya juya ya fada motarsa ya ja ta ya bar bakin Asibitin.
Da shigar Mariya Asibitin ba in da ta dosa sai dakin da Mahaifiyar ta take a kofa ta tadda Mahaifin nata zaune ya zabga tagumi sosai ya shiga damuwa sosai za ka fahimci yana cikin yanayi matsananci.
"Baaba!".
Mariya ta fadi cikin sauti da rauni a muryarta kamar zata rushe da kuka.
A hankali ya dago idanuwansa da sukayi matukar canza launi sosai tashin hankali ke zagaye da su.
"Har kin dawo Mariya?".
ya fadi cikin sanyin murya. Gyada kai tayi gami da samun waje kusa dashi ta zauna tana ajje numfashi da kyar.
Ba wanda ya sake kokarin tankawa a tsakaninsu tsayin lokaci suna cikin halin shiru kafin Mariya ta nisa cikin sanyin jiki.
"Uhmm amma Baba ya na ganka a nan zaune wa aka bari da Umma?".
Ta tambaya tana mai kafeshi da idanuwanta da suke a hargitse.
Shiru yayi ba tare da ya bata amsa ba har ta fara tsire tsammani da amsawar tana kokarin sake magana taga ya motsa laɓɓansa.
"Barci take yi".
"Har yanzu bata tashi ba?".
Ta sake tambayarta domin lokacin da ta bar asibitin a cikin halin barci ta bar ta.
"Ta farka ta sake komawa".
Mariya ta fara motsa laɓɓanta ta na son yin magana sai ga Dr.Aqeel yayi Sallama garesu amsawa sukayi Mariya tayi masa Sannu da zuwa. Murmushi yayi kafin ya ce,
"Mariya har kin dawo kenan. na zo dazun Abban ki ke cewa dani kin je gida".
Gyada kai tayi gami da kalato Yaƙe ta ajje a fuskarta.
Shiru ne ya tsake ziyartar wajan ba wanda ya sake magana sai ajiyar zuciyoyi dake fiddo da sauti sosai lokaci yaja a tsakanin su har zuwa lokacin ba wanda yake kokarin tsinkawa.
Dr.Aqeel da ke tsaya hannunsa rike da wani File yana dubawa bayan ya gama ya dube su.
"Hala ciki da zafi kuka zauna a nan?".
"Ko daya Likita kawai gani nayi tana barci na fito nan na zauna".
GyaÉ—a kai kawai yayi bai sake magana ba ya juya bayan yayi musu sallama ya tafi.
Mariya ta bishi da kallo sosai halin Dr.Aqeel ke burgeta natsuwarsa gami da karamcin sa yana kara mata mutuncinsa a idanunta sosai take ganin girmansa tabbas ta yarda ba duk mutane bane suke iri daya a duniyar nan ta yarda halintar Dan-adam daya ne amma halin kowanne ya bambanta ba ta taba tsammanin za su samu mutum mai karamci da taimako irin Dr.Aqeel a da can ta dauka kowa ba mai kirki bane ashe da bambanci.
"Amma Mariya naga kin jima kafin ki dawo ina kika tsaya?".
Bello ne ya katse mata tunanin zuccin da take yi da sauri ta dube shi tana faman gyada kai sosai ya kafe ta da idanu ganin halin da ta nuna hakan ya kara daburta mata tunani ta rasa amsar da zata baiwa mahaifin nata shin ta fada masa haduwarta da mutumin da ya kusan kashe ta tun lokacin ta bai yi ko kuwa...
"Kika yi shiru?".
Ya katse mata tunanin da ta afka.
"Uhmm dama ba abin da ya tsaida ni kawai dai wani ne...".
Sai kuma tayi shiru ta kasa krasaw domin yanayin da ta ga Mahaifin nata ya nuna sai tayi da nasanin sakin bakin da ta so yi domin ta san tabbas sai ya ji ba dadi in har ta fada masa.
"Wani mutum yayi me?".
Ya fada ya na kafe ta da idanu sosai hakan ya sanya ta shan jinin jikinta a dan daburce ta daga laɓɓatanta.
"Bakomai".
Shiru yayi yana nazarin maganar tata ya tabbata akwai wani abu amma da alamun ta na tsoron sanar dashi.
"Allah ya kyauta".
Abin da ya fadi kenan ya koma ya zabga tagumi.
'Ameen'
Mariya ta amsa ita ma a ranta gami da mikewa domin kai kayan da ta zo da su cikin dakin.