JAMA'A MU YI HAƘURI AKAN ADDINI

*_JAMA'A MU YI HAKURI AKAN ADDINI:_*

Manzon Allah (s.a.w) yace: "Wani zamani zai zo a bayanku (ku Sahabbai) wanda masu riko da addini a cikinsa sai sun yi hakuri, duk wanda ya rike addini a wannan lokacin yanada ladan shahidai hamsin na cikinku (ku sahabbai)". 

Sahihul Jami'i Hadisi na 2234

A wasu ruwayoyin (kamar yadda yazo a cikin Al-ausad hadisi na 3121)

Annabi (s.a.w) cewa yayi "ladan mutum hamsin na cikinku", sahabbai suka tambayi Annabi (s.a.w): "mutum hamsin cikinmu ko dai cikinsu?" Annabi (s.a.w) yace: "a'a, cikinku dai" 

A lokacin da musulunci fitina ta masa yawa, zunubai suka cika duniya, izgili wa masu addini yayi yawa: ladan masu hakuri a wannan zamanin daidai yake da ladan aikin alkhairi na sahabbai guda 50.

Idan sun fi mu ta wani waje musamman yin zamani da Annabi (s.a.w), to mu ma Allah Ya fifitamu akansu ta wani waje. Aiki ya ragewa mai aikatawa, sabawa Allah Ya ragewa mai saba masa; Allah Ya bawa kowa damar shiga Aljannah. 

Ya Rabbana Ka bamu ikon hakuri akan riko da addininKa domin lallai mutane sun riki masu riko da addininKa abin izgili amma ba su sani ba ne.

Post a Comment (0)