BA MAZAN BA, BA MATAN BA


BA MAZAN BA, BA MATAN BA:!

Zaku taya ni shaida cewa an wayi gari a yau,akasarin maza idan sun tashi neman wadda zasu aura, babban abin da ya dame su game da macen shi ne "kyau". 

Abin da zai kara baka haushi kuma shine, dà yawan su suna son kyakkyawar ne don su rika yawo da ita a gaban mota suna nunawa jama'a, ana cewa kai wane fa ya hadu,domin ya dauko hadaddiya! Kaga kuwa idan kana neman "sakarci" lamba daya, to shi ne wannan.

Haka zaka ga mace ita kuma, da yawansu
idan an zo maganar aure babban abin da ya dame su "kudi". 

Ba kowa ce ma ta damu da kyakkyawa ba a nan, a'a su dai kudi! To kada in jaku da nisa, wallahi duk namijin da ya auri mace saboda kyau kawai, bata da ilimi da tarbiyya sai kyau kawai, kada ya sa rai zai samu kyakkyawar rayuwar aure. 

Sai fà in Allah Ya taimakeshi ya iya ilimantar da ita da tarbiyyantar da ita, wanda wannan kuma yana da wahala sosai.

Haka duk yarinyar da ta hangi kudi kawai a gun wanda zata aura, bata damu da ilimi ko tarbiyyarsa ba, wallàhi duk abin da ya biyo baya na rashin kwanciyar hankali, kada ta tsaya neman dalili, don gashi na gaya mata.

Allah Ya sanya mu daga cikin masu yin aiki da sani, amin

Rubutawa : Habib Jafar Madobi
Post a Comment (0)