JAN HANKALI GA MATA


NORTHERN RANGERS GROUPS

Assalamu alaikum. Ina mai yima mata barka da warhaka suna na doctor Aisha. 

Ayau an ne mi in ware dan kadan daga cikin lokuta na don mu wayar wa da 'yan uwa mata kai game da wasu product da ake ta tallata masu da sunan wai vaginal wash, da wani wai shi vaginal tightening gel to abisa la'akari da abubuwan da mu masu magunguna muke ta fama dasu na game da wahalhalun warkar da mata wanda suke kamuwa da sababbin cututtuka game da irin wadannan product yasa dole mu fito ta social media inda ake saida maku irin wadancan product din mu wayar maku da kai game da wannan bala'i daya same mu. 

Idan muna son mu tabbatar da cewa wannan products din suna illah to sai mu ziyarci asibitoci manya inda ake shanya al'aurar 'yan uwa mata wanda an rasa ma ta ina za'a iya taimaka masu mu gani da idanun mu.

Idan kina da dan'uwa ko 'yar uwa dake aiki a LAP ki tambaye ta yàya farjojin mata wanda irin wannan product din ya bata yake? Hakika baki iya kallon wajen balle ki shaki iskar wajen don warin da wurin yake tare da zubar da wani ruwa me wari🙊

Yaku 'yan uwa mata hakika muna jefa kan mu ga halaka kan sabulan tsarki da muke saye wanda babu komi a cikin su sai chemical masu matukar hadari ga lafiyar mu.

Maza da dama na complain kan cewar matan su suna da matsalolin da suka kasa gane masu. To amma ba sabulun tsarki ne mafita ba dole mu gaya maku mafita yanzu.

Shi sabulun tsarki da kuke saye an goshi ne daga kayan da ake yin sabulun wanke wanke da ake kira liquid soap! Chemical din nan ko jiki kike wankewa dashi dole wata rana ki fuskanci matsala, karin da ake samu a cikin kayan ingredients din sune garin farin miski
Man kanumfari
Coconut oil
Sai kala da ake canzawa zuwa fara da muke kira whitener 
Sai mai na ayu ko gasaya 
Wannan sune abunda ake kira vaginal wash soap.

Babbar matsala anan itace shi kanshi liquid soap yana da sinadarai da suke kawo cancer wanda turawa da suka wàye suke kin suye product din sabulan wanka ma da suka kunshi irin wancan chemical da mu muke tsarki dashi da sunan magani infection ko kara ni'ima.

Vaginal tightening 
Shi kuma ya kunshi chemical na sama da muka ambata sai sinadarai dangin alum wanda anyi ittifakin yana kawo cancer al'aurar mata to, mata me muke son jawo wa kan mu? Kan namiji mu kashe kan mu idan cancer ko wata cuta ta same ki an gaya maki zai tsaya sai kin warki ne zai yi sex? Kin kuwa yi babban kuskure, da sannu wancan product din zai watsa martabar farjin ki da duk wata baiwa da Allah yayi maku, mu kuma asibiti da masu magunguna muna jiranku inda zaku kashe dubbai baku warke ba a karshe ku mutu abanza kuje lahira ba ladar jinya sai azaba dan ku kuka saya da kudin ku. 

*Natural vaginal wash with henna leaves*
Idan kina gani ruwa na fita ta farjin ki fari me za kaikai yadda zaki yi sai ki sawo kwalba daya na kaltufa
Ganyen lalle wanda ba'a daka ba gwangwanu daya1 ki debo bishiyar tura ganyen gwangwani 1

Sai ki dora tukunya ta silver bisa wuta ki sa wutar kadan sai ki Juye kaltufa duka cikin tukunya ki rufe idan ta dau zafi sai ki Juye wannan ganyen lalle dana turare da kika samo ki juya ki sake rufe su wutar kadan ake so ba so ake ki dafa maganin ba irin tafasa ciki ake so suyi na minti biyar, sai ki sauke ki dan janye marfi ya huce, sai ki tace ki maida a kwalba ki rufe ki boye wuri me duhu, zaki rika zuba 2 teaspoons a ruwan da bashi da sanyi kuma baida zafi ki sha, sai kuma ki rika zuba marfi daya a ruwan dumi kina tsarki dashi.

Dole ki dena shan sugar na wata daya da cin bread

Dole ki bar yawan zama da pant, in ya zama dole dan yawan discharge sai ki sayi cotton pant don Sam ba'a son al'aurar ta zama cikin lema shike kawo kwayoyin cuta su ha66aka. Kada ki wuce sati 2 kina amfani da wannan magani. In baki warke ba to ciwon ya shiga hanta ko koda dole ki je ayi maki test a asibiti don gano matsala domin kuwa ko wace cuta da irin nata magani.

Don Allah ku yada wannan sako don ceton 'yan uwa mata daga sharrin kamfanoni masu son arziki dare daya.

Wannan sako ne daga likitoci mata musulmi masu Kishin mata, don Allah kuyi sharing ta WhatsApp, Facebook fisabilillah!
Post a Comment (0)