SABULUN WANKA GA MATA


SABULUN WANKA GA MATA
****************************
Kasancewar da yawa an bukaci sake yin post akan wannan sabulun In shaa Allahu ga shi na sake post akai.

yin tsarki da sabulun wanka yana kawo wa mata matsala sosai, saboda irin sinadaran Chemicals din da ake hada sabulun yana da hatsari ne ga dan Adam, musamman ma mata (domin yakan kawo musu cancer of vagina).

Amma ga wata FA'IDA da zaku hada sabulu da kan ku domin yin wanka ko tsarki, kuma ba tare da ya kawo wata matsala ba kuma za'a iya amfani da shi cikin kwanciyar hankali, ba tare da wata damuwa ba, kuma bayan haka yana maganin yawancin cutukka na mata musamman na kaikaiyin gaba, da sauransu. Zaa iya samun hadden sabulun a wajen ...

Abubuwan da zaku nema.
• SABULUN ZAITUN
• MISKI
• BAGARUWA.
• MAN HULBA.

Da farko, za'a nemi sabulun Zaitun, amma fa wanda aka rubuta Zaplan a jikin kwalin (DOMIN YAFI KYAU), kada a ba ku marar kyau. idan kuma ba'a sameta ba ayi da ta kamfanin Hemani.

Sai a nemi Bagaruwa, a daka ta ta
daku, a zuba a roba sai a yanyanka sabulun zaitun din kanana-kanana a kan garin bagaruwan, a zuba Miskin a ciki a Kwaba shi da ruwan Hulba, a kwaba su sosai har sai ya yi kauri.

Sai a zuba a roba mai kyau a rufe, Sai a rika wanka da shi, kuma ana yin tsarki da shi.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa irin wannan Sabulun ba shi da wani hadari ko ‘Side effect’ ga mace, kuma zai kara tsuke mace, sannan ta rika kamshi da kuma karuwar ni’ima.

Sannan mazama zasu iya hada wannan sabulun su rika wanka da shi.

please ku turawa 'yan uwanku domin mu amfana
Post a Comment (0)