Matsayin Sallar Jam'i A Musulunci
Daga Imam Murtadha Gusau
Lahadi, 15/03/2020
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkkaken Sarki. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta, Annabin karshe, Muhammad (SAW), da alayensa da sahabbansa da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Ya ku Musulmi, lallai ku sani, shi ilimin fikhu (wato ilimin fahimtar addini) yana daga cikin mafi matsayin ilimomi a cikin addinin musulunci, da haka ne zamu gane cewa fikhu tushe ne da ya kasance musulmi yake auna aikin sa dashi, game da abin da aka halasta ko aka haramta, ingantacce ko batacce, kuma musulmai gaba daya suna kwadayi wurin neman sanin halas da haram, ingantacce da ya shafi alakar su da Allah ko bauta masa, na kusa ko na nesa, makiyi ko aboki, shugaba ko wanda ake shugabanta, musulmi ko wanda ba musulmi ba, kuma babu wata hanya ta sanin haka sai ta ilimin fikhu.
Ya ku 'yan uwa Musulmi, lallai babu shakka, Shari’ah ta umurci maza, masu iko, da yin sallar Jam’i, kuma Shari'ah ta tsawatar a kan barinta, kuma saboda hadarin da ke tattare da barin ta, Manzon Allah (SAW) yayi niyyar ya kona gidajen wadanda basu zuwa sallar jam’i, haka kuma bai yi izini ga barin zuwanta ga makaho ba, bare mai gani. Dalili akan haka shine:
1. Fadin Allah Mai girma da buwaya game da sallar tsoro:
“Idan kana tare da su, ka tsayar masu da sallah, to wasu jama’ah daga cikinsu su tsaya tare da kai.” [Suratun Nisa’i, 102]
A wannan aya, zamu ga cewa Allah Madaukakin Sarki yayi umurni da ayi sallar jam’i ko a halin tsoro ne, don haka a halin zaman lafiya da aminci shi yafi cancanta da sallar jam’i.
2. Hadisin Abu Hurairah – Allah ya yarda da shi – yace:
“Sallar da tafi nauyi akan munafikai ita ce sallar isha'i da sallar asubah. Da sun san abin da yake cikinsu da sun zo masu koda da rarrafe ne (ko jan ciki). Hakika nayi nufin inyi umurni da ayi kiran sallah, a tayar da ita, sai in umarci wani mutum yayi wa mutane sallah, sannan sai in tafi tare da wasu mutane, da tarin kiraren kunna wuta a tare da su, in je wurin mutanen da basu zuwa sallar jam'i, in kona masu gidajensu da wuta.” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]
Ya ku 'yan uwa Musulmi, Manzon Allah (SAW) ba zai kona gidajen wadanda basa zuwa jam’i ba sai don zuwa jam’in wajibi ne, haka nan ba za'a siffanta wadanda basa zuwa jam’i da munafikai ba sai don sallar jam'in wajibi ce.
3. Hadisin makaho, wanda ya nemi izinin Annabi (SAW) a kan yayi sallah a gida, saboda bai da jagora, sai Manzon Allah (SAW) yace masa:
“Shin kana jin kiran sallah? Sai ya ce, “Eh” Sai Manzon Allah (SAW) yace, “To ka amsa.” [Muslim ne ya rawaito shi]
4. Abin da ya tabbata daga Abdullahi Dan Mas’ud – Allah ya yarda da shi – yace:
“Wanda yake son ya gamu da Allah gobe kiyama yana musulmi to ya kiyaye wadannan salloli (guda biyar) duk lokacin da aka yi kiran sallarsu. Hakika Allah ya shar’anta wa Annabinku hanyoyin shiriya, wadannan salloli suna cikin hanyoyin shiriya. Da zaku yi su a gidajen ku da kun bar Sunnar Annabinku, idan kuwa kuka bar Sunnar Annabinku to da kun bata. Babu wani mutum da zai yi tsarki, ya kyautata tsarki, sannan ya tafi masallaci daga cikin masallatai, face sai Allah ya rubuta masa ladar kyakkyawan aiki da duk takun da yayi, ya daga masa daraja da wannan taku, a kankare masa zunubai da shi. A fahimtar mu (mu sahabbai) babu wanda yake kin zuwa sallah sai munafiki sannanne. Saboda ma muhimmancin sallar jam'i, a zamanin mu ana zuwa da mutum yana tafiya tsakanin mutane biyu, saboda bai iya tafiya, har a tsaida shi a cikin sahu, domin ya samu sallar jam'i.” [Muslim ne ya rawaito shi]
Hikimar Sallar Jam’i Da Falalarta
1. Sallar jam'i yana sa sanin juna da 'yan uwa da abokai, da karfafa dankon soyayya tsakaninsu, soyayya da imani basu samuwa sai da ita, saboda babu wata hanya zuwa ga imani ko zuwa ga Aljannah sai soyayya da kaunar juna saboda Allah.
2. Kubutar bawa daga munafunci da wuta ga wanda ya riski kabbarar harama tsawon kwana arba’in a jere, saboda abin da Anas – Allah ya yarda da shi – ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW) yace:
“Wanda yayi sallah saboda Allah kwana arba’in a cikin jam’i, yana riskar kabbarar farko, to za'a rubuta masa kubuta kala biyu: kubuta daga wuta, da kubuta daga munafinci.” [Tirmizi ne ya rawaito shi]
3. Sallah a cikin jam'i yana hada kan musulmi, da hada zukatansu akan alheri da nagarta.
4. Sallah a jam'i yana sa a samu fahimtar matsalolin juna da samun taimakon juna tsakanin musulmi.
5. Sallar jam'i yana kara bayyana ayyukan addini da karfafa shi.
6. Yana hada kan zukatan musulmi, ta yadda zasu hadu a sahu daya, da baki da fari, da balarabe da wanda ba balarabe ba, da babba da karami, da mawadaci da talaka, duk zasu tsaya gefe da juna, a bayan limami daya, a lokaci daya, suna fuskantar alkiblah daya, a wuri daya.
7. Sallah a jam'i yana bakantawa makiya Allah rai, saboda musulmai ba zasu gushe ba da karfi da kariya, matukar suna kiyaye sallah a masallatai, a cikin jam'i.
8. Sallar jam'i yana kankare zunubai, da daga darajar bawa. An karbo daga Abu Hurairah – Allah ya yarda da shi – yace, Manzon Allah (SAW) yace:
“Shin ba zan nuna maku abin da Allah yake kankare zunubai, ya kuma daga daraja da shi ba? Sai suka ce “Eh nuna muna ya Manzon Allah (SAW)” Sai yace, “Kyautata alwala akan gabbai, da yawan taku zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wannan shine Ribadi, wato zama don Allah.” [Muslim ne ya rawaito shi]
9. Sallar jam’i tafi sallar mutum daya da daraja ashirin da bakwai.
An karbo daga Abdullahi Dan Umar – Allah ya yarda da shi – yace, Manzon Allah (SAW) yace:
“Sallar jam’i tafi sallar mutum daya da daraja ashirin da bakwai.” [Bukhari ne ya rawaito shi]
Matsayin yin Sallar Jam’i a Gida
Ya ku Musulmi, wallahi bai halatta ga wani ko wasu jama’ah ba suyi sallar jam’i a gida alhali ga masallaci kusa da su. Amma idan masallacin yana da nisa, basa jin kiran sallah, to babu laifi a kansu suyi sallarsu ta jam’i a gida. Amma matukar zasu ji kiran sallah, to dole ne su amsa.
Ukubobi Guda Biyar Ga Masu Barin Sallar Jam’i Da Falalar Sallar Jam’i
Mala’ikah Jibrilu (AS) yace:
"Ya Rasulillah (SAW): Wanda ya bar jam’i shine mafi sharri daga masu cin riba, wanda ya bar jam’i shine mafi sharri daga masu yin annamimanci da suka, wanda ya bar jam’i shine mafi sharri daga yin rowa na mutum dubu da cutar da makwabta. Ya Muhammad (SAW) kada kaje gaishe da su idan basu da lafiya, kada kaje jana’izarsu idan sun mutu, wanda yake barin jam’i baya shiga Aljannah, baya da wani rabo a wurin Allah, baya da rahama, domin baya da gaskiya."
Manzon Allah (SAW) yace:
"Ya ku taron Musulmi, Allah maɗaukaki ya saukar da ukubobi guda biyar, wadanda ba kowane mahaluki ne zai gan su ba, sai suka ce, ya Rasulillahi (SAW) su waye? Sai Manzon Allah (SAW) yace: 1. Mutuwa da magagin mutuwar. 2. Kabari da duhun sa. 3. Tambaya da tsanantawa. 4. Siraɗi da siririn sa. 5. Ma’auni da rashin nauyin sa. Sai Abubakar (RA) yace, Ya Rasulillah (SAW) ga su wanene aka yi hani ga waɗannan ukubobi guda biyar? Sai Manzon Allah (SAW) yace, Ya Abubakar, wanda yake yin sallar asubah a cikin jam’i Allah zai hana masa mutuwa da magagin ta. Wanda yake yin sallar zuhur a cikin jam’i Allah zai haskaka kabarinsa. Wanda yake yin sallar magariba a cikin jam’i Allah zai hana masa shan wahalar siraɗi da siririnsa. Wanda yake yin sallar Isha’i a cikin jam’i Allah zai hana masa mai tambaya da tsanantawa." [Kitabul Mawa’iz]
Kuma abinda ake nufi da barin jam’i shine mutum ya bar sallah a cikin jama’ah, yayi ta shi kadai, ko shida wasu mutane a gida ba a masallaci ba, kuma ba tare da wata lalura da musulunci zai karba ba. In da lalura ana iya dubawa.
Wadanda aka yi rangwame gare su:
1. Anyi ragwame ga mata, domin sallah a jam'i bai zamo dole a gare su ba.
2. Anyi ragwame ga maras lafiya.
3. Anyi rangwame ga matafiyi, jam'i bai zamo dole a gare shi ba, sai dai yayi kasaru.
A takaice dai, ya kamata mu fahimci cewa, sallar jam’i wajibi ce akan maza da suke ‘ya’ya (ba bayi ba), masu iko, mazauna gida, domin umurnin Allah akan hakan.
Kuma shi umarni yana nuna wajibci ne, sai fa idan an samu wani dalilin da yake nuna rashin wajabci a wannan umurnin.
Sannan idan ance jam'i to ana la’akari da liman ne da kuma mamu, koda kuwa mutane biyu ne, ko da ko mamun macece, saboda hadisin Abu Musa wanda ya danganta shi ga Manzon Allah (SAW) cewa:
“Mutane biyu zuwa sama to su jama’ah ne.” [Ibnu Majah ne ya ruwaito]
Sannan kuma an sunnanta yin jam'i a masallaci ne, tare da jama’ah, amma kuma yana halasta ayi jam'i a wani wurin da ba masallaci ba, idan akwai bukatar yin hakan, wato lalura karbabbiya a Shari'ah.
Su kuma mata sun sami damar yin jam'i idan sun kebanta ga maza, domin aikin Nana Aisha da Ummu Salamah, wanda Imam Darul-kutuni ya ambata:
"Kuma Manzon Allah (SAW) ya umarci Ummu Waraka da ta jagoranci mutanen gidanta." [Abu-Dawuda ne ya ruwaito shi]
Ina rokon Allah ya bamu ikon kiyaye yin sallah a cikin jam'i, kamar yadda Allah da Manzon sa su ka yi umurni, amin.
Ya Allah, muna tawassali da sunayen ka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka a koda yaushe.
Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).
Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za'a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.