HALIN MAGABATA A CIKIN WATAN SHA'ABAN 01


HALIN MAGABATA A CIKIN WATAN SHA'ABAN. 0⃣1⃣

Yana daga cikin manyan ayyuka na kwarai da bawa ke kusantan Ubangijinsa dashi acikin watan sha'aban akwai; Azumi, tsayuwar dare, yawan karanta Alqurani, gaggauto da zakka da kuma yawaita sadaqa. wannan sune abubuwan da aka ruwaito daga magabata da za'a ribaci watan sha'aban dasu. 
 Alhafiz Ibnu Rajab Allah ya masa rahama yana cewa "Kasantuwar watan sha'aban tamkar muqaddimace ga watan Ramadan, hakan yasa aka shar'anta acikinsa duk abunda aka shar'anta acikin Ramadan na daga azumi da karatun Alqurani saboda shirin fuskantar watan Ramadan, da kuma tarbiyantar da zuciya akan yiwa mai Rahama biyayya".

لطائف المعارف ١٣٨ 

# Zaurenfisabilillah 

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)