HALIN MAGABATA A CIKIN WATAN SHA'ABAN 0⃣2⃣
Abubakar Albulkhy Allah ya masa rahama yana cewa; "Watan Rajab watane na shuka, watan sha'aban kuma watane na ban ruwa (bayi), watan Ramadan kuma watane na girbi".
Sannan ya kara cewa "Watan Rajab kamar iskane (guguwa), ita kuma watan sha'aban kamar hadari ne, ita kuma watan Ramadan shine kamar ruwan saman".
Wani daga cikin magabata yake cewa "Shekara tana nan kamar bishiyane, watan Rajab shine lokacin fidda furenta, watan sha'aban kuma shine lokacin fidda ya'yanta, watan Ramadan kuma shine lokacin tsinkan ya'yan, muminai sune suka cancanci tsinkan ya'yan, ga wanda ya bakanta littafinsa da zunubai sai ya farantashi da tuba zuwa ga Allah acikin wannan watan, wanda kuma bata shekarunsa abanza sai ya ribaci abunda ya rage na shekarunsa".
لطائف المعارف ١٢١
# Zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah