HALIN MAGABATA A CIKIN WATAN SHA'ABAN 04


HALIN MAGABATA A CIKIN WATAN SHA'ABAN 0⃣4⃣

An ruwaito daga sahabi Uthman bin Affan Allah ya kara yarda agareshi yana cewa alokacin da Ramadan ta kusanto "Wannan itace watan fidda zakkanku, dan haka duk wanda yasan ana binsa bashi to ya gaggauta biya domin ya samu daman fidda zakkarsa, idan ya gama biyan bashinsa to sai ya fidda zakka daga cikin abunda ya rage na dukiyar".

 An ruwaito daga magabata cewa idan watan sha'aban ta kama suna fidda zakkar dukiyoyinsu domin su karfafawa mai rauni da miskinai gwiwa wurin azumtar watan Ramadan (zasu basu zakkan domin su samu damar yin sayayyan kayan abinci saboda samun damar azumtar Ramadan cikin nishadi, batare da fargaban rashin samun suhur ko buda bakiba)".

فتح الباري ١٣/٣١١

# Zaurenfisabilillah

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)