HALIN MAGABATA A CIKIN WATAN SHA'ABAN 0⃣3⃣
Habeeb bin thabit Allah ya masa rahama ya kasance idan watan Sha'aban ta kama yana cewa "Wannan itace watan QURRA'U (masu yawaita karatun Alqur'ani)".
Amru bin qais Al-Mula'i Allah ya masa rahama, ya kasance idan watan Sha'aban ta kama yana kulle shagonsa ya kebance kansa ga karatun Alqur'ani kawai.
Salmata bin kuhail Allah ya masa rahama yana cewa "Ya kasance ana Kiran watan Sha'aban da watan qurra'u.
Alhassan bin Shaheel Allah ya masa rahama ya kasance yana yawaita karatun Alqur'ani acikinsu (watan sha'aban da watan Ramadan) sannan sai yace "Ya Allah ka sanyani atsakanin watanni guda biyu masu girma".
لطائف المعارف ١٣٨
# Zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah