ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 5


*05→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

11. Cikin zina akwai kamancecceniya da dabbobi, saboda mazinaci ba ya daukar nauyin abin da zai biyo bayan lalatarsa, kamar yadda dabba ba ruwanta da abin da ke biyo bayan saduwarta da ’yar uwarta, na kula da mai ciki da tufatar da ita da rainon abin da aka haifa da yi masa tarbiyya. Ka ga ke nan mazinata rayuwar dabbobi suke yi. Allah Ya kiyaye mu.

12. Zina tana kawo kisan kai a cikin al’umma. Sau da dama fada kan faru tsakanin masu neman mata a wajen yawon banzarsu; wani ya kashe wani, kamar yadda yawancin yaran da ake yarwa, ko ake kashewa ’ya’yan zina ne. Haka yawancin cikin da ake zubarwa cikin zina ne, wanda duk wannan kisan kai ne da Allah ba Zai kyale wanda ya yi shi ba.

13. Zina tana lalata al’umma, ta ruguza rayuwa gaba daya, ta hanyar samar da ’ya’yan da ba su da tarbiyya, ba sa ganin girman kowa. Kai, suna jin haushin al’umma, lura da hanyar da suka zo, abin da da dama yakan sa su zamo ’yan daba da fashi da sauran miyagun ayyuka, su bata rayuwarsu, su bata rayuwar al’umma.

14. Yawaitar zina alama ce ta tashin Alkiyama, kamar yadda ya zo a Hadisi, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yayin da ya ce: “Ya al’ummar Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), wallahi babu wani da ya fi Allah kishin a ce yau bawanSa ya yi zina, ko kuma baiwarSa ta yi zina. Ya al’ummar Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kun san abin da na sani da kun yi dariya kadan da kun yi kuka da yawa.” Sannan sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya daga hannunsa sama ya ce, “Ya Ubangiji, na isar,” Buhari ne ya rawaito.

15. Zina tana jawo fushin Allah da azabarsa ga al’umma. Abdullahi dan Mas’ud (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce: “Zina ba za ta bayyana a wata alkarya ba, face wannan alama ce da Allah Ya yi izinin halakar da ita.”

’Yan uwa wadannan kadan ke nan daga cikin abin da zina take haifar wa masu yin ta da sauran al’umma. Allah Madaukakin Sarki Ya kare mu.


Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

Zaku iya bibiyar mu a telegram sai a danna koren dake Qasa👇
https://t.me/joinchat/M_XPUBckMpCl_dPC-2MrVA

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)