TAMBAYA TA 021

*Tambaya:*


Assalamu Alaikum malam dafatar kana cikin koshin lpa malam nice ina aykata zina kuma aduk lkcinda nagama aykata ta sainaji raina yabachi kuma inason indaina mezan rinka yi don indaina ngd
.

*Amsa:*


Waalaiku mussalam.

Alhamdu lil Allahi Rabbil alameen.

Muna rokon Allah Ya yaye maki wannan fitina don tsarkin sunayensa.

Idan mutum na sa6o yana so ya tuba, to abin da ake so ya dage ya cika sharuddan tuban duka kamar su:

1-Tuba don Allah. (ikhlasy)

2- barin sa6on da rabuwa da abokanan yi da barin wurin/garin yin sabon. 

3- Yawaita tuna Allah ta hanyar istigfari da sauran azkar.

4- duk abin da zai sa a tuna wannan alfashan kamar su hotuna ko video to a guje su gaba daya.

5- Yi ma Allah magiya wajan neman shiriya.

6- Daukar matakin kange faruwar hakan kamar yin aure ko kari in rashin shi ne ya kai ga hakan.

Wannan su ne matakan da malamai suka yi magana a kan su.


والله اعلم.

*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*

Post a Comment (0)