*Tambaya:*
Assalamu aleekum anwuni lafiya malam inada tambaya gameda azumi inada olsa lokacin azumin banida lafiya danasha magani nafara dayan danakai bansakeyiba nakasa kwanaki nafara inayin daya olsan yadameni natambaya akace nacire to zaniya cire shinkafa da masara ko abudaya zanbada allah yasaka da gidan aljanna
.
*Amsa:*
Waalaiku mussalam.
Rashin lafiyar da za tasa ka aje azumi don ciyarwa ita ce wadda aka cire tunanin waraka, ya zama tilas kwararru a fannin lafiya sun tabbatar lalular ta kai matakin ba yadda za a iya yin azumi duk da iko yana hannun Allah SWT, idan har lalular ta kai haka to in anzo ciyarwan za a ciyar ne gwargwadon abin da mutum yake mallaka, ba dole bane in an fara da wani jinsin abinci ace se an kare da shi, za a iya canzawa batare da yin dubara ba wajan gujema tsarin Allah.
والله اعلم.
*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*
*🕌Islamic Post WhatsApp.*