TAMBAYA TA 48

*Tambaya:*


Assalamualaikum malam dan Allah inada tambaya 1: Idan aka saki mace saki biyu sai taje tayi aure a wani wuri canma sai aka sakota, sai ta sake komawa gidan tsohon mijinta amma anyi sabon aure da sadaki da komi, wai ya matsayin auren su yake shin wannan saki biyun Yana nan ko ya rushe ya auren fresh yake ko yaya? Nagode
.

*Amsa:*


Waalaiku mussalam 

Idan mace ta rabu da mijinta sanadiyyar saki ta yi wani auren kuma ta dawo aka sake daura aure da tsohon mijin, wannan auren sabone koda da saki uku ne, kamar yadda ya zo cikin. 
صحيح فقه السنة 
Don haka sakin farko ya lalace ba'a kirgashi cikin saki bayan wannan sabon auren.

المغني 
والله اعلم.


*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*

Post a Comment (0)