Tambaya
:
Shin ko ya halatta Mace ta ɗauki wani abu a dukiyar Mijinta tayi sadaka dashi ba tare da izinin Mijinba??
:
Amsa
:
Dangane da hukuncin cewa Mace ta ɗauki wani abu daga cikin dukiyar Mijinta tayi tasarrufinta cikin wani aikin alkhairi kamar sadaƙa, kyauta, taimakon mabuƙaci, da dai sauransu, Malamai sukace hukuncin yin tasarrufi da dukiyar Mai-Gida ya kasu cikin halaye ne kamar guda uku:
:
(1)--Hali na ɗaya shi ne, idan ya kasance dama Miji ya yiwa Matarsa izini a bayyane cewa ta yi tasarrufi a cikin dukiyarsa gwargwadon yadda ya dace, to a nan babu wani Ishkāli (Rikitarwa) a cikinsa, danhaka kai tsaye ya halatta ta iya yin sadaka daga cikin dukiyarsa, domin Mαnzon Aʟʟαн(ﷺ) Yace:
:
"لا يجوز لإمرأة عطية إلا بإذن زوجها"
MA'ANA:
Baya halatta ga Mace tayi kyauta (da dukiyar mijinta) sai in da izinin Mijin nata:
:
(2)--Hali na biyu shi ne, ya kasance a bayyane dama Miji ya hana Matarsa tayi tasarrufi a cikin dukiyarsa, to shima wannan babu wani Ishkāli (Rikitarwa) a cikinsa game da cewa kai tsaye haramun ne Mace ta ɗauki wani abu acikin dukiyar Mijinta tayi sadaƙa ko kyauta dashi tunda ya hanata, saboda Annαвι(ﷺ) Yace:
:
"لا يحل مال إمرئ إلا بطيب نفسه"
MA'ANA:
Baya halatta (ayi tasarrufi da) dukiyar Mutum sai in da daɗin ransa (yardarsa):
:
(3)--Hali na uku kuma shi ne, ya kasance a bayyane Miji bai bawa Matarsa izinin tayi tasarrufi cikin dukiyarsa ba, haka kuma a zāhiri bai fito fili ya hanata ba, wato shi dai bai hana ba sannan kuma bai ce ayi ba, to dangane da wannan hali na uku sai Malamai sukayi saɓani a kansa,
:
Wani sashe daga cikin Malamai suka tafi a kan cewa ya halatta Mace tayi tasarrufi a cikin dukiyar Mijinta, zata iya bada sadaƙa ko kyauta daga ciki gwargwadon abin da ba zai zama ɓarna da dukiyar ba ko ya tozartar da ita, danhaka za ta yi ne dai dai gwargwadon urfi (al'ādarsu) bisaga yanayin yadda ko da Mijinta yaji labari ba zai damu ba, Misali kamar idan ya kasance a bisa ga al'adar yanayin yadda aka saba gani a garinsu idan wani almajiri ko mabuƙaci yazo yana neman taimako galibi akan ba shi daga ₦1,000 zuwa ƙasa da haka a Misali, to babu laifi tabayar da hakan. Amma idan taɗauki ₦10,000 ko ₦100,000 ta bayar ko shakka babu ta wuce gona da iri, amma idan ta yi ne dai dai yadda ya dace to shikenan babu laifi, sai dai in dama tasan halayyar Mijinta Mutum ne da baya son a taba masa dukiya danhaka ko da ta bayar idan yaji labari zai nuna damuwarsa, to a nan haramun ne Mace taɗauki wani abu nasa komai kankantarsa tayi sadaka dashi, daga cikin dalilan Malaman da sukace ya halatta Mace tayi tasarrufi ba tare da izinin Mijinta ba sun kafa hujja da wannan Hadisi na Mαnzon Aʟʟαн(ﷺ) da ya ke cewa:
:
"إذا أطعمت المرأة من بيت زوجها غير مفسدة، كان لها أجرها وله مثله،"
:
"وفي رواية"
:
"كان لها مثل أجره، لها ما نوت حسنا، وللخازن مثل ذالك"
:
MA'ANA:
Idan Mace ta ciyar daga ɗakin (dukiyar) Mijinta ba tare da tayi ɓarna ba to tana da lada shima kuma yana da lada,
:
Awata ruwayar a ka ce:
:
"Ta kasance tana da lada saboda kyakkyawar niyyar ta, haka nan mai dukiyar shima yana lada misalin haka"
:
Sai dai wasu daga cikin Malamai sun tafi ne akan cewa idan ya kasance Miji bai fito fili yace tayi ba haka kuma bai fito fili ya hanata ba, sukace to bai halatta ba ta ɗauka ta bayar dole sai in ta nemi izininsa, idan kuma ta ɗauka to ta aikata haramun kuma sai ta biyashi a ranar kiyama, daga cikin dalilan Malaman da sukace haka shi ne, sun kafa hujja da wannan Hadisi na Annαвι(ﷺ) da yake cewa:
:
"لا تنفق إمرأة شيئا من بيت زوجها إلا بإذن زوجها، قيل يا رسول الله(ﷺ) ولا الطعام؟ قال ذاگ أفضل أموالنا"
MA'ANA:
Kada Mace ta ciyar da wani abu daga ɗakin (dukiya) Mijinta sai da izinin Mijinta, sai a ka ce Ya Ma'aikin Aʟʟαн(ﷺ) ko da abinci ne ta bayar? Sai Ya ce to ai wannan (abincin) shi ne mafi falala a cikin dukiyoyinmu,
:
Amma magana mafi rinjaye acikin zantukan da Malamai sukayi itace, idan yakasance Miji bai hanaba kuma bai ce ayiba, to ya halatta Mace tayi sadaka da dai dai gwargwadon abinda zuciya ba za ta yi ƙyashin a bayar da shi ba,
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/