Tambaya
:
Shin waɗanne irin abubuwa ne suke iya halattawa Mace ta nemi saki a wajen Mijinta??
:
Amsa:
:
Asali dai a shari'ance a na yin aure ne da nufin sai dai mutuwa ta raba auren ba wai da nufin a rabu ba, shiyasa idan ya kasance Ma'aurata suna irin zamanda a shari'ance babu wata cutuwa a tsakaninsu, to baya halatta ga Mace tanemi saki a wajen Mijinta kamar yadda Mαnzon Allαh(ﷺ) ya faɗa cewa:
:
"أيما إمرأة سألت زوجها طلاقا في غير ما بأس، فحرام عليها رائحة الجنة"
(رواه الترمذي/1187)
MA'ANA:
Dukkan wata Mace da ta nemi saki a wajen Mijinta ba tare da wani tsanani (sababi) ba, to an haramta mata taji koda ƙanshin Aljanna,
:
Danhaka asali a shari'ance Mace ba ta da ikon ta nemi saki a wajen Mijinta, to amma idan ya kasance akwai wani sababi ko wata larura da shari'a ta yarda da su to babu laifi idan Mace tanemi saki a wajen Mijinta ba tare da ta biya shi wata fansaba, akwai yanayin ma da yake iya zama wajibi akan Mace ta nemi a sake ta din. Danhaka Malamai sukace ya halatta Mace ta iya neman saki a wajen Mijinta idan ya zamana rayuwarta tana cikin wani garari a zamantakewar auratayya tsakaninta da Mijinta, kamar Misali idan ya kasace Mijin yana munana mata, ko yana ƙauracemata ya dena saduwa da ita ba tare dawani dalili da shari'a ta aminta dashi ba. Malamai sun ambaci waɗansu abubuwa waɗanda a dalilinsu Mace za ta iya neman saki a wajen Mijinta, kamar Misalin.
:
(1)-Idan ba ya iya ciyar da ita yadda ya kamata.
:
(2)-Idan ya kasance Miji yana dukan Matarsa.
:
(3)-Idan ya kasance Miji yana zagin Matarsa ko kuma zagin Iyayenta.
:
(4)-Idan ya kasance Miji baya iya biyawa Matarsa buƙatar aure kuma tana cutuwa a dalilin hakan.
:
(5)-Idan ya kasance Matar ta ga wani aibu a tare da shi ko wata cuta.
:
(6)-Idan yakasance yana wasa da Sallah sai yaga dama yakeyi ko kuma ba ya Azumi.
:
(7)-Idan ya kasance mai aikata kaba'ira ne kamar shan giya ko sata ko neman Matan banza ko luwaɗi.
:
(8)-Idan ya kasance yana ɗauke da wata cuta da za ta iya shafar ita Matar.
:
(9)-Idan ya kasance yana tilastawa Matar akan dole sai tayi wani abu na Saɓon Allαн(ﷻ).
:
(10)-Idan yakasance yana ɗauke da wata cuta da za ta iya hanawa Matar haihuwa.
:
(11)-Idan ya kasance ba ya barin Matar taje ta sada zumunci da iyayenta da kuma 'Yan'uwanta.
:
(12)-Idan ya kasance Matar ta ƙyamaci ɗabi'ar Mijin saboda mummunan halinsa.
:
(13)-Idan ya kasance ba ya a dalci a tsakanin Matansa wajen rabon kwana ko zaman takewarsu.
:
(14)-Idan ya kasance sana'ar da yake yi ta haramunce kamar saida giya ko gumaka ko kuma caca.
:
(15)-Hakanan wasu daga cikin Malamai sukace idan ya kasance Miji sunyi sharaɗi da Matarsa akan ba zai yimata kishiya ba kuma sai yayi, ko sukayi sharaɗi akan ba zai ɗauke ta daga garinsu ya kaita wani garinba kuma sai yakaita din, to Malamai sukace idan har Miji yasaɓa ire-iren waɗannan sharuɗɗa to ya halatta Mace ta nemi a saketa,
:
Danhaka kenan a yayin da Mace ta samu kanta a wasu daga cikin sabuba makamantan waɗanda aka ambata, to idan za ta iya yin haƙuri da juriya a hakan tare da shi, to babu laifi suci gaba da zamansu tare, amma idan taga ba zata iya jurewaba to alal-haƙiƙa ya halatta tanemi Mijin ya saketa, amma idan ya kasance Mijin ba ya yin sallah ne ko azumi ko kuma wasu abubuwan da Allαн(ﷻ) ya wajabta masa, to da farko ya kamata tayi masa wa'azi ko tasa ayi masa, idan kuma yaƙi denawa to bai halatta taci gaba da zama da shi ba, danhaka wajibi ne ta nemi ya saketa dan tatsira da addininta awajen Allαн(ﷻ)
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/