*Tambaya:*
Assalamualaikum
Allah ya qarawa malam imani
Malam Dan Allah waye mahauci? Kuma meyasa ba'ason auren su?
Nagode.
.
*Amsa:*
Waalaiku mussalam.
Ban san wata mas'ala ta musulunci ba da ta haramta auren MAHAUTA ba, amma akwai canfi tsakanin su da Fulani wanda wannan gargajiya ce ba addini bane. Kawai abin da ake nema mutumin kirki wanda aka yarda da addininsa da tarbiyyarsa kamar yadda manzon Allah saw yace:
*"إذا جاءكم من ترضون دينه وخلقه فزوجوه الا تفعلوا تكن فتنة فى الأرض وفساد كبير.“*
سنن الترمذى وغيره.
*"Idan wanda ya zo neman ku (da aure) kun yadda da addininsa da ďabi'unsa to ku aura masa in ba haka ba fitina za ta auku a ban 'kasa da b'arna me yawa.”*
Tirmizi.
Saboda haka Ba wata al'ada makamanciyar wannan da musulunci ya tabbatar .
والله أعلم.
*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*
(Abu Ammar).
*🕌Islamic Post WhatsApp.*