TAMBAYA TA 75

Salamu alaikum Malam dangane da ciyarwa da aka ce mai ciki tayi idan baxata Iya axumi ba, shin dole sai a ranar da ta sha xata ciyar ko kuwa xata Iya ciyarwa daga baya, sannan dole Wanda xata bawa yayi buda baki da abincin ko ko daga baya xaka Iya bashi bayan isha haka? Sannan kuma dole shi kadai xai ci ko xasu Iya ci da wasu? Shin xata Iya bada kudi a maimakon abincin ko dole sai abinci

Amsa

Wa'alaikumussalam
A dunkule abinda ake buqata kowanna azumi Daya aciyar da mutum daya ya Qoshi kawaiba'a buqatan wani abu sama da haka

Ciyarwa ake nema "Kunada zabin chiyar da mutane 30 arana daya ko kubawa mutum daya na tsawon kwana 30 na abinda ze wadatar dashi, da abinda ze dafa kayan miya da sauran su..."

Ba se lalle a ranan ba "yazama dai bashi akanki, idan kinsamu dama seki sauqe nauyi"
Wallahu a,alam

Post a Comment (0)