TARIHIN BARIN SALLAR JUMU'A DA SALLOLIN FARILLA A MASALLACI SABODA ANNOBA


TARIHIN BARIN SALLAR JUMU’AH DA SALLOLIN FARILLA CIKIN JAM’I A MASALLACI SABODA ANNOBA KOWASU LARURORI Jumu’ah,2 ga watan Sha’aban 1441(27/03/2020)

01

BismillahirRahmaanirRaheem.Alhamdulillah.Wassalaatu wasSalaam alaaRasuulillah, wa Aaalihiwa As’haabihi waman waalah.

Bayan haka,wannan dan takaitaccen bayanine gameda tarihin dakatar da sallar Jumu’ah dayin sallar jam’i a masallaci saboda tsoron yaduwar Annoba ko saboda wasu larurori dasu kahada da ambaliyar ruwa da yaki. Na tattaro bayananne daga wasu makaloli da littafan da wasu masu bincike suka rubuta bayan na bibiyi asalin littafan da sukayi amfani dasu wajen tsara nasu bayanan.

Ina rokon Allah Yakawo mana karshen wannan Annoba ta Corona virus(COVID-19)data addabi Duniya a halin yanzu.

DAKATAR DA SALLAR JUMU’AH DAYIN JAM’IN SALLOLIN FARILLA A MASALLACI SABODA AUKUWAR ANNOBA KO TSORON YADUWAR TA

,A shekarar 18AH(693CE), annoba mai tsanani ta auku a garin Amawaas kuma tamamaye garuruwan Shaam. Annobar tayi sanadiyyar mutuwar Sahabban Manzon Allah (tsira da amincin Allah sutabbata a gareshi)da suka hadada Abu Ubaidah bn Al-Jarrah, da Mu’az bn Jabal, da Yazeed bn Abi Sufyaan, da Suhail bn ‘Amr, da Utbah bn Suhail (Allah Yayarda dasu), dawasunsu. A lokacin aukuwar annobar, Abu Ubaidah shine shugaba (gwabna) a Shaam. Bayan rasuwarsa, Mu’az bn Jabal yazama gwabna. Bayan rasuwar Mu’az, mutane sun zabi‘ Amr bn Al-‘Aass a matsayin shugaba. Daga cikin hanyoyin da‘ Amr bn Al-‘Aass(Allah Ya yarda dashi) yabi wajen magance matsalar annobar da iznin Allah, akwai nisantarda mutane daga junansu (wanda a yau akekira social distancing da turanci). Imam Ahmad, da Ibn Khuzaimah, da Ibn Hibbaan sun ruwaito hudubar da ‘Amr bn Al-‘Aass yayi bayan yazama gwabna:

“Yaa ku mutane!Idan irin wannan cutar ta auku, tanaruruwane kamar yadda wuta keruruwa; (don haka) kufita (daga gari) zuwa cikin du watsu”.A wata ruwayar:“Ku rarrabu zuwa saman duwatsu da cikin kwazazzabai”.

Dayawa daga malaman tarihi sun bayyana cewa adalilin wannan rarrabuwarsu da nisantar dasukayi wajuna duk da inkarinda Abu Waathilah Al-Huzaliy yayiwa‘ Amr da farko ,sallarJumu’ah bata yiwuba har sai dasuka dawo cikin gari bayan wucewar annobar.

Muhadu a fitowa na gaba
Post a Comment (0)