YI KOKARI KA RIBACI WANNAN LOKACIN, KAFIN YA RIBACEKA.
Alhafiz Ibnu Hajar Allah ya masa rahama yake cewa "yana daga cikin fa'idar Annoba; karancin buruka, da kyautata ayyuka, da kuma farkawa daga gafala, da yin guzuri dan tafiya".
بذل الماعون في فضل الطاعون ٣٧٨
NOTE
Ya kai musulmi na kwarai, hakika wannan lokaci na wannan gamammiyar annobar damace agareka na samun riskar abunda ka rasa da cikace gibin da ka samu alokutanka na baya tsakaninka da ubangijinka, lokacine da zaka ribace da komawa zuwaga ubangijinka da tuba zuwa gareshi da yawaita karatun alqurani da kuma nafilfili domin samun rahama da kariya daga Allah. Ka zama mai lizimtar wasiyar manzon Allah a irin wannan lokacin; ka kame harshenka, gidanka ya yalwaceka sannan kayi kuka akan zunubanka, idan ka aikata haka hakika ka rabauta. Amma idan kayi sakaci da watsi da wannan wasiya ta manzon Allah to kasani tabbas wannan lokaci shi zaiyi riba akanka.
# zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah