ABUBUWAN DA AKE SO MATAN AURE SU YI KAFIN MAI GIDA YA SHIGO ƊAKI

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Abubuwan Da Ake So Matan Aure Aikata Kafin Mai Gida ya Shigo Daki_*

Ya kamata tayi kyakkyawan shirin da zai farantawa mai gidanta kafin ya shigo dakinta, lokacin da ya shigo bayan sallar isha'i, ga hanyoyin kamar haka;

1. Yana daga sunna mai kyau matan aure tayi wanka ta shafe jikinta da man shafawa mafi dadin kamshi, sannan ta fesa turare kafi sallaman mai gida, domin kuwa kamshi shine yake motsa sha'awar ma'aurata.

2. Yana daga sunna matan aure tasa kwalli a idanunta, sannan kuma tayi kunshi, don shine yake nuna banbanci tsakanin hannayen mata da na maza.

3. Yana daga sunnan matan aure tayi kwalliya da kayan ado iri-iri kamar kwalli, jagira,jambaki, sarka,awarwaro,agogo,zobe da makammantansu da kuma duk irin adon da zai farantawa mai gida rai, don neman yardan Allah.

4. Yana daga sunnan matan aure ta gyara mai gida shimfidar kwanciyarsa kafin ya shigo, kuma ta yarjewa kanta cewa a yau ita nashine kuma taba shi kanta a ko da yaushe don neman yardan Allah.

5. Yana daga ladabin jima'i mata da miji su tsaftace jikinsu kamar yadda ya dace, matan aure ta shafe jikinta da man kamshi, sannan ta tsaftace shimfidar da zasu kwanta tasa turare mai kamshi kuma ta fesawa maigidan nata, yin haka yana kara dankwan soyayya a tsakanin ma'aurata.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)