AZUMIN TSOHO DA TSOHUWA

AZUMIN TSOHO/TSOHUWA

Tsoho ko Tsohuwa za su yi azumi idan za su iya, idan ba za su iya ba; saboda raunin jiki da kasantuwar shekaru sun ja, sharia ta yi mu su sassauci za su ajiye azumi sai su rinka ciyarwa, an samo hakane karkashin aya ta 184 dake suratul Baqara da kuma fassarar magabata na kwarai kan ayar.

 YA AKE CIYARWAR:
1. A kowace rana za a ba miskini rabin sã'i na abincin da aka fi amfani dashi a yankin da mutum yake. Sannan a babin kyautatawa ana so a haɗa masa harda kayan da zai dafa abincin, in ma an haɗa masa da irin nama ko kifi an kyauta kwarai.
Ko kuma duk sanda aka sha ruwa a zuba abinci a mazubi wanda zai ƙosar da mutum daya sai aba mabuƙaci.
2. Za a bari sai an gama azumi gabadaya sai a tara miskinai 29 ko 30 (abisa adadin azumin da aka yi a shekarar) sai a ciyar dasu abinci, za a ba kowa abinda zai Æ™osar dashi a take. An samu Sahabi Anas bn Malik r.a yana aikata haka a sanda ya manyanta baya iya azumi. 

TAMBIHI: Mutum zai iya ciyarwa da kan shi, ko kuma wani ya ciyar a madadin sa amma da izinin sa. Kamar yadda Shaiykh Salih bn Abdulazeez Sindiy ya bayyana a risalar sa gameda mas'alolin azumi.

Allaah Ya datar da mu.

Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
12/Ramadan/1441.
05/May/2020.

Kasance damu a tashar mu na manhajar Telegram@

Maza: https://telegram.me/almadeeniymodernschool

Mata: https://telegram.me/almadeeniymodernschoolfemale

Post a Comment (0)