TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 12


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//12📿*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Ibn Taimiya yake magana game da yadda Annabi SAW ya yi ma'amalla da munafuqai ya ce "Annabi SAW ya riqa yi musu salla da nema musu gafara sai da aka hana shi, aka nuna cewa yin hakan kafurci ne, da wannan za a fahimci cewa duk wanda ba a san boye kafurcinsa ba za a iya yi masa salla da nema masa gafara, koda kuwa bidi'arsa ta fito fili kuma yana fada wa wasu zunuban" har dai ya ce "Manufa dai don mutum ya abka wani zunubi, ko wata bidi'a ko ma ya kira mutane gareta wannan bai isa a yi masa hukuncin boye kafurci ba, sai dai in munafuqi ne, amma kamar mutumin da akwai imani da manzon Allah da abinda manzon ya zo da shi a zuciyarsa, sai ya yi subul da baka wajen yin wani tawili na bidi'a wannan sam ba kafiri ba ne".

Ya ce "Khawarijawa (Boko haram) sun fi kowa bidi'antarwa da yaqar al'umma, da kafurtata, amma ba a sami wani daga cikin sahabbai wanda ya kafurta su ba, har Aliy RA, kawai dai sun yi musu hukuncin azzaliman musulmai ne masu wuce gona da iri, kamar yadda aka sami maganganun magabata a kan haka ba ma wuri guda ba (Ak-Fatawal Kubra 2/113) idan ya kasance hukuncin da za a yi wa wanda ya boye kafurci kenan ba a sani ba, ko ya kafurta musulmai ya halasta jininsu, to wanda ya boye kuskure ko sabo shi ya fi dacewa a rangwanta masa matuqar a kwai ilimin da aiki da shi.

To matsalarmu gaggawa, wace a qarshe in ba a yi dace ba riya ko tsanani ya shigo har a kasa kaiwa ga ainihin abinda ake kwadayin isa gare shi, dan abu kadan a ce tunda wane ya ce kaza ko yake abota da wane, ko ya yi kaza dan Shi'a ne ko dan Ikhwan ne, misali a rayuwata aqidar da ban taba sha'awarta ba ita ce Shi'a, na fahimci qaryarsu ga mabiyansu da yaudarar sauran al'umma tun ban san meye aqidar shi'ar ba ma, amma abin mamaki kan wasu hudubobi da na yi, wanda zahiri na yi su ne ba tare da karantar yanayin matattarar da na dawo ba, wannan kuwa kuskure ne ba ko shakka.

Ina zaune sai ga wasu daliban ilimi daga Tudun Wadan Kaduna sun zo wurina, na shiga masallaci muka zauna da su suka gabatar min da kansu sannan suka ce sun zo muqabala ne da ni a matsayina na dan Shi'a, na ce musu ni ba dan Shi'a ba ne ban karbi abinda suke suka ta da shi ba kuma ba wata muqabalar da zan yi da su, amma in suna da wani abinda za su janyo hankalina da shi na gode, amma ba zan karbi cewa ni dan Shi'a ne ba, sai ga shi dalibaina a cikin aji sun fara qalubalantata da maganar Shi'an, har wani ya kalle ni ya ce shi ba zai yi karatu a wurin dan Shi'a ba, wani ya ce duk zulle-zullen da zan yi ban isa na kauce masa ba don ya san Shi'a ba sanin yara ba, na qaryata maganar na yi musu nasiha, duk da haka wani ya tashi a masallaci yana gaya wa mutanen da muke zaune da su hatsarin Shi'a da kuma ba da shawara a kaikaice kan cewa a kore ni a ma'aikatar.

Duk wannan fa a kan zargi ne bisa abinda aka ji na ce, ina cikin unguwa ba a tuntubi maqwabtana an ji ba, ina da mata ba a ga wata sifa ta Shi'a tare da ita ba, tana da qawaye ba su ji tana maganar Shi'anci ba, abokaina daliban ilimi ba su taba tsinkayar wata aqida ta Shi'a tare da ni ba, dalibaina qanana a makaranta da nake koyar da su addini ba su san komai game da wannan ba, ta ya mutum zai iya boye wannan kuwa a kasa ganewa sai a maganarsa ta lokaci guda? In kuma subul da baka ne ko wata karkata ce da za a iya gyarawa kafin ta yi nisa fa? Ko mutum ya boye dai zai je tarukansu, za a yi hira da shi a ga irin mutanen da yake hurda da su, ko littafan da yake sha'awar karantawa, ko batutuwan da yake son tattaunawa, ko tarbiyar matansa da 'ya'yansa ko suturu da sauransu, wani abin mamaki kuma sai ga shi ni din dai tare da wasu muke sahun farko wajen hankatso sharrin shi'ar a matattara ga wadanda ba su santa, yanzu qoqarin muzanta mutum ya fi sauqi sama da neman shiriyarsa.

Nawa da sauqi tunda ba malami ba ne, in an soke ni zai tsaya a kaina ne kawai, qila ko iyalina tunda da abin ya yi nisa za a iya tsanarsu, ko diyoyina a rayuwarsu ta aure qila, amma abinda ya fi muni shi ne sukar manyan malamai da ake yi da Ikhwananci, malamannan dubban jama'a ne suke karatu a qarqashinsu, suna da littafai, da majalisai a jahohi daban-daban, da dalibai a ko'ina, a zahiri su kansu suna yaqi ne da muggan aqidu sai kuma su din ne za a soka da aqidun ko a tura musu bidi'anci? Wa ke irin wannan ta'asar? Daliban ilimi ne, abin haushi wadanda ba su kai ma su durqusa a gabansu kai tsaye su yi karatu ba, sai dai mu roqi SW afuwa, amma mun yi nisa, tunda har mun kai ga hukunta kammu koda kuwa ba mu da wata hujja qwara daya da muka dogara da ita a wajen hukuncin

*GINSHIQI NA SHA BIYU*

DOLE NE MU YI ADALCI

Ya zama dole a yi wa wanda ake da sabani da shi adalci, adalcin kuwa da za a yi masa ya shafi wasu al'amura masu dama:-

1) A amince da cewa tabbas yana da karatu in an san yana da shi din, ba wai a ce jahili ne bai san komai ba, bayan an san ya yi karatu din, qila a zamanance ba wai digirin farko ne da shi ba har na uku, ko kuma a zaurance an san malaman da ya yi karatu a wurinsu ko daliban da yake karantarwa, ko littafan da ake karatun a wurinsa.

2) In ya yi dai a wasu mas'aloli a amince a karba, da ma daidai din ake buqata kuma ya kawo, in ya yi kuskure a bar shi.

3) Kar a ce maganarsa tana nufin kaza kenan tunda ya ce kaza, sai in a zahiri abin nufin kenan ko shi ya furta hakan.

Wannan shi ne adalci na asali kuma shi ne yake bude qofar da mutum zai ga gaskiya kuma ya karbe ta, mu a yanzu da wahala ka ga an yi wa wanda ya bar hanya wannan hanzarin, ni a ganina in mutum ya qi gaskiya kamata ya yi a yi ta binsa a boye, a yi haquri har ya karbe ta, in mun yi gajin haquri sai mu dawo mu bi shi a hankali din dai amma a bayyane, a nan kam ko shi bai karba ba Allah SW zai haska zuciyar wasu daga cikin mabiyansa su karba, shi ma nasara ne, nuna kai ya yi yawa, za ka ja hankalin mutum ka saki faifai wa duniya wai kana yi wa mutum guda gyara a kan kuskuren da ya yi, ko ka yi rubutu a kafofin sadarwa na zama "Budaddiyar wasiqa zuwa ga wane" mutum dubu dari miliyan sun karanta, wai kuma mutum guda kake yi wa gyara.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa:Abulfawzhaan*
Post a Comment (0)